Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 16

Chapter 16

Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel 1,207 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kuma ta yi min aike ni da Noor. Ba su kwana ba ranar da suka zo ranar suka koma bayan mun yi ma Noor tsaraɓar kayan maƙulashe da kuma tufafi, Inna kuma suka kawo mata atamfa da buhun kishinka ƙarami. Ranar da suka kwana biyu da tafiya ina zaune tsakar gida misalin ƙarfe goma sha ɗaya na safe wayata ta yi ƙara alamar saƙo, ban kulata ba dan na daina ɗaukin aikin a yanzu tunani ba zan samu ba, tun da kullum ina sa ran ganin saƙon kamfanin amman sai na samu saƙon mtn. Sai da na gaji da kwancin da nake na tashi zaune ya miƙa hannu na ɗauki wayar da ke kusa da ni ina dubawa. Ina ganin sunan Kamfanin One-On-One jikina ya fara rawa, cikin zumuɗi na buɗe saƙon Congratulations na ga an rubuta a sama.ban iya tsayawa karanta sauran ba na buga tsalle ina ihun daɗi. WHO IS READY FOR THE NEXT CHAPTER? I can't wait to see Nawwara in One-On-One limitless company. 😍 *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 1⃣3⃣ Ihun da na yi ne yasa Inna fitowa daga ɗaki da sauri tana kallona. “Na samu aikin Inna sun ɗauke ni” Murmushin haukan da na ke ta yi, tana girgiza kai for first time bayan rasuwar mahaifinmu yau na ga murmushin Inna. Zuwa na yi da gudu na rumgumeta ina ta murna kamar babu abunda ke damuna. Haka na wuni cikin farinciki da jindaɗi kamar wacce aka yi ma kyautar kujerar makka. Ban san farincikina kaɗan ne har sai da Habiba ta dawo na sanar mata da labarin sai ta yi kamar zata haɗe kanta dan murna kai kace ma ita ta samu aikin ba ni ba, a ranar Habiba bata iya cin abincin rana ba dan tsananin murna, da maraici ta siye alawa da kuɗin Inna ta yi sadaka. Haka ta ke nunawa kulawarta da damuwa a duk lokacin da wani abun ya sameni, ta kan zauna ta labarta min abunda Inna bata sani ba, zata iya ɓoyewa Inna abu amman ni bata ɓoye min ba, mutune har mamakin yadda muke son junanmu suke, ganin ita take bina amman bama taɓa samun saɓani, ko ma mun samu tun anjima kaɗan zanje na rarrasheta ko kuma ita ta zo ta bani haƙuri ko da kuwa ni ce bana da gaskiya, irin tsabanin da ake samu tsakanin mabiyi da mabiyi ni ban cika samunsa da Habiba ba, muna son junanmu sosai, ko ciwo ɗayan mu yake sai ɗayan ya ji kamar ya cirewa ɗan'uwansa ya sakawa kansa. Lokacin da Baba na da rai idan ya tashi zolayarmu har cewa yake yadda muke son junanmu bama sonsa haka, wani gurin ma idan mukaje ba dan kamanni ba da mutane za su ce Habiba ƙawata ce ba ƙanwata ba. Ba zan iya misalta irin son da take yi ma Noor ba, tun da na haifeshi ita ce da ɗawainiyarsa har ya kawo yanzu, babu kuma wanda ya isa ya nuna masa ɗan yatsa a unguwarmu ko ma a cikin gidanmu ni kaina ban isa na hukunta Noor ba indai a kan idon Habiba ne. Ni kaina shaƙuwar ta kan ba ni mamaki, wata ƙila dan akwai tazarar shekara bakwai a tsakaninmu. Duk farinciki da ɗaukin aikin da nake idan na tuna Baba ba ya raye sai na ji babu daɗi, na so ace na samu aikin yana da rai na san zai yi farinciki sosai, sai dai kuma ƙaddara ta riga fata abunda Allah ya rubuta dole shi zai samu bawa. A daren ranar da na samu aiki sai ga Bilal ya kirana ni a waya na yi zaton zai ce na fito ne sai ya ce na aiko masa Noor yana bakin ƙofar gida, ba musu na miƙawa Noor wayar, ban san mi suke tattaunawa ba kawai dai na ga Noor yana dariya yana ɗaga kai sai kuma ya wulgumin wayar ya tashi ya fita da gudu har yana ƙoƙarin faɗuwa. “Falfala da gudu ɗan gidan Bilal sai in be kiraka ba” Cewar Habiba tana dariya. Nishaɗin dake fuskarta shine a fuskar Inna da Jamila har ma Sakina da kuma ni kaina. “Bilal ɗin nan yana son Noor kuma na tabbatar son da yake miki ne ya shafe shi” Na ɗago na kalli Inna da furucin da ta yi. “Ba fa so na yake ba, mutunci ne kawai a tsakaninmu, be taɓa cewa yana so na ba” Habiba ta watsa min harara. “Ji matar nan muna-muna munafuka, Wallahi son junansu suke amman shi ba zai iya faɗa ba ita ba zata ba shi dama ba, ai da yanzu an wuce gurin, duk alamun da yake nunawa ai na son ki ne, ke kuma kina kauce masa” Na yi dariya ina girgiza kai. “To ya kike son na yi?” “Ya dai kamata ki bashi dama, zama haka ba zai yiyu ba, Allah kaɗai yasan iya gulmar da ake muku a unguwarnan, kin kore kowa kin zauna a gida gashi har mahaifinki ya rasu be ga wani auren na ki ba” Wannan karon Inna ce ta yi maganar, kuma maganar da ta yi ta ɗan taɓani, tabbas mutuncin ƴa mace da kuma darajarta a gidan aurenta ne, sai dai ba kowa ne zai maka son tsakani da Allah ba, wasu kan zo so na saboda sha'awata da sun gwasa sun gano ni ba ƴar iskar barawarar nan ba ce sai su gudu, wasu kuma su nuna maka ba zasu yarda da je da yaron ka ba, wasu kuma basa da wani sana'ar kirkin da za su iya riƙe sauran iyalansu ma balle kuma a haɗa da ni, kowa da irin matsalarsa. Bilal ɗin ma laƙe min ya yi da sunan abota, sai dai ko da wasa ban bashi alamun da zai iya nuna min so ba, saboda na san iyayensa ba zasu yarda ya auri mace da taɓa aure har biyu ba kuma har da ɗa ma. Uffan ban ce ba, Inna da Habiba kawai ke ta nanata maganar. Muna nan zaune Noor ya shigo da ƙatuwar leda a hannunsa har biyu a hannunsa baki har kunne. “Momy kalli abubuwan da siyo min, kuma ya ce Mama Habiba kawai zan bawa kar na sammi ki, kuma ya ce yana kiranki yana ƙofar gida” Shi da Habiba suka riƙa kokuwar buɗe ledar, ni kuma na zari Hijabina na nufi ƙofar gida. Tsaye na sameshi yana kallon ƙofar gidanmu da alama dai yana jiran fitowata ne. “Ina ta zuba ido na ganki yau a kamfaninmu ban ganki ba” Ban bashi amsa ba sai da na yi masa sallama ina murmushi. “Assalamu alaikum” Sai ya amsa min da murmushi. “Wa'alaikissalam Nawancy, na zo na taya ki murnar samun aiki, ai na faɗa miki zasu ɗauke ki” “Ɗazu na samu saƙon, na jidaɗi sosai” “Mutane na ta zuwa karɓar uniform amman ke ban ganki ba” “Uniform kuma?” “Yes ai Uniform zaku saka, tun safe ake zuwa ƙarɓa kin ga ɗaga yau zuwa gobe ne kawai ake bada uniform ɗin, on monday zaku fara zuwa aiki, kuma idan kunje karɓar uniform ɗin za a nuna muku irin aikin da zaku yi” “Gobe zanje Inshallah, ai ban san ana zuwa yau ba” “Sai dai matsala ɗaya, Nawancy bana son ki saka wando, ina ganin kamar ba be

Table of Contents

Chapters

119 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});