Chapter 88
Chapter 88
gurin ba dan na suma ba sai dan kafafuwana da suka min sanyi, ga hawayen da suka soma nin zuba babu kakkautawa. “Haba Mom miyasa kike min haka ne? Wallahi da ki yi ma Nawwara fada kara ki yi min” Tasowa ta yi ta karaso inda na ke. “Ban san kaddara ba Nawwara, duk na rasa dana saboda ke ki fara kirga irin asarar da zata sameki kema” “Tir da mace dattijowa irin ki ta tsaya tana fadin bata yarda da kaddaraba, ke an fada miki Nawwara son Mustapha take ne?” Cewar Bilal yana kokarin defending dina, wata muguwar harara Hajiyar Mustapha ta watsa masa. Sai mahaifin Bilal ya katsa masa tsawa. “Bilal wuce muje” Sai da ya kalleni kamar ba zai iya bari a gurin ba, sai kuma ya juya ya fice tare da mahaifinsa, ni kuma na unkura na tashi ina nuna na fito daga gurin na nufi sashen da Noor yake. Ko da na tura kofar na shiga Noor yana bachi hankalinsa kwance, kusa da shi na zauna hawaye na zuba a idanuwana, na kai hannu na shafa shi. Ina haka sai Jibril ya turo kofar dakin ya shigo yana sanye da labcoat, bayan ya maida kofar ya rufe ya zuba hannayensa cikin aljihu ya doso inda nake. “Na sallami yan sandan” Ban dago na kalleshi ba balle kuma har na amsa masa. “I'm sorry Nawwara” “Na tsane ka Jibril” “Na sani” Ya amsa min a takaice. “Ka sake dawowa saboda ka ruguza sauran farincikin da ya rage min ko?” “Wallahi ba dan haka na dawo rayuwarki ba, Nawwara ba ki cancanci auren kowa ba sai ni ko dan Noor, yanzu kin fi son ki barwa wata uwar ta yi miki rainon da? Dan kin san ba zan taba bari kije min da shi gidan duk wanda kika aura ba ko?” “Kowa kallon mahaukaciya yake min, ka kunyata ni a gaban mahaifin Bilal” “Bani da wani zabin ne Nawwara, Wallahi ina son ki sosai, saboda ke nake ta canja rayuwata Nawwara, dis week wani Malami zai fara zuwa yana karantar da ni saboda kawai na samu xama cikakkane namiji da kike so, amman hankalin ya koma kan Bilal, kin kasa fahimtata Nawwara” Na daga kai na kalleshi. “Bana son ka Jibril miyasa ka kasa fahimta? Hakika Noor be yi dacen uba” “Babu wanda zuciyarki take so sai ni Nawwara, Nawwara idan kika aure wani ba ni ba, rayuwata da ta Noor tana cikin hadari” “Bari idan na auri Bilal din, ku fadi ku mutu” Ina fadar hakan na mike tsaye na share hawayena na fice daga dakin zuciyata na mugun kuna. Ko da na iso gida numfashina har sama yake kamar zan hadiye zuciya na mutu saboda bacin rai, tun daga yanayin sallama ta ya kwantarda Inna irin damuwar da na taho da ita ga wani uban ja da idanuwa suka yi sun kumbura sosai saboda kukan da nayi. Muryata a dakishe na zauna saman tabarmar da Inna take zaune na fara rusa kuka, sai hankalin Inna ya tashi. “Lafiya miya same ki?” “Jibril ne” “Yi hakuri tsagaita kukan sai ki min bayani, amman kamin nan kina da bakuwa” “Wacece?” Na tambaya cikin kuka. “Muma ba mu santa ba, amman tun dazu take jiranki” Na share hawayena na mike tsaye na nufi dakin Inna domin ganin wacece, abun mamaki sai na samu Aisha zaune tana kallon kofa da alama ta ji shigowata kuma ta ji lokacin da na doso dakin. _____________________________ Assalamu alaikum fans i will be offline for awhile saboda fever na damuna sosai, jiya ma daker na yi typing yau ma karfin hali kawai na yi Wallahi dan kar na barku kuna ta jira, zan je ganin doctor gobe so yanzu kan sai na samu sauki sosai sannan zan sake yin typing. Thanks All Best regards ♥️🖤 [11/8, 9:37 PM] +234 703 352 5246: *RAI BIYU...♥🖤* Wattpad @KhadeejaCandy 4⃣9⃣ JIBRIL POV. Bayan fitar Nawwara ya zauna kusa da gudan jininsa yana ta kallonsa, shi kansa yana jin rashin kyauta a abunda ya yi ma Nawwara sai dai ya yi hakan dan ya bata ta a gurin iyayen Bilal, kuma ya banbance wanda ta fi so tsakamin Bilal da Mustapha. Hannunsa yasa aljihu ya dauko wayarsa ya kira wata nurse ta kawo masa wani file tare da sai ya cire wata kadarda ya rubuta ma Noor takardar sallama, sannan ya dauki dansa ya saba a kafada hakan yasa Noor farkawa sai ya soma jijjigashi kamar jariri. “Shiiiiii cigaba da bachinka Daddynka ne” Hakan yasa Noor tafewa a kafadar Jibril ya fito tare da shi harabar asibitin ya sakashi gaban mota sannan na zagayo ya shiga driver seat ya tashi motar sai kuma ya daga wayarsa ya kira wata number “Ki shiga dakin da aka sallami Noor ki kwashe komai zan aiko da dareba ya dauka” Yana fadar haka ya kashe wayar, ya tashi motar ya hau titi dake cikin asibitin kamin ya sadu da babban titi marafa dan baba da ke cikin birnin sokoto. Duk bayan seconds ya kan kalli gefen da dansa yake sai idanuwansa su cika da kwalla, hamdalla yake yi ma Allah akan yau yana da gudan jinin wannan dalilin kadai ya isa yasa ya cigaba da tirsasa kansa gurin Nawwara, domin ita ce kadai macen da ta kawo masa wannan farinciki a rayuwa, bayan ya yanke tsammanin zuwansa. ‘I promise you Noor i will to my very own best na ga na zama uba na gari a gareka, i will make you and Nawwara proud of me’ A kasan zuciyaraa yake wannan tunanin yana sauke ajiyar zuciya. “Ba zan iya hakura da kw ba Nawwara, kema kina bukatar farinciki a rayuwarki, ni na bata komai dan haka ni ya kamata ace na gyara komai” Wannan karon a fili ya yi furucin yana danna horn a bakin gate din gidansa, a hankali ya yi parking sannan ya dauko wayarsa ya yi ma Nawwara text akan cewar an sallami Noor saboda kar taje asibitin bata tarar da kowa ba, sannan ya fita motar ya zagaya ya bude ya dauko Noor da ke kokarin bude idanuwansa. “Zan iya tafiya” Ya fada saboda ya samu a sauke shi ya samu kallon gidan da kyau, kamar Jibril ya sani sai ya sauke shi ya rika hannunsa suna tafiya a hankali, rabon ido kawai Noor yake kamar zasu fado sabo kallon yadda kukasan wani tsohon bakauye, yana saka kafarsa cikin falon sai sayin tile din ya ratsashi ga sanyin ac da ya mamaye ko ina a cikin falon, suna shigowa Jibril ya sake shi ya nufi bedroom yana amsa waya, sai Noor ya daga kansa sama yana kallon pop falon da fankar kamin da dawo gurin kujerun falon da suka katsance farare sol kamar fentin falon da kuma center carpet din da ke falon, karasawa ya yi gurin kujeru sai ya zauna kasa ya kai hannu yana shafa manyan cushion din idanuwansa kuma suna kan katuwar plasma TV mai daukar ido gashi an kawata gurin da wallpaper fari mai daukar hankali, ga wasu manyan flowers da aka aje a gurin suma farar kamar labulayen falon. “Noor Son tashi tashi zauna saman kujera ya zaka dauka kasa” Jibril ya fada ganin dansa a kasa kamar wani almajiri. “Momy ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119