Chapter 9
Chapter 9
yaja baya, Baba Dahiru ya shiga duba Baba, Baba Sulaiman kuma ya fasa kuka yana faɗin “Sun kashe min ɗan'uwa ba bisa haƙƙi ba, Wallahi ɗan'uwana be yi sata ba, ya rantse min da Allah be ɗauka ba, sun ɗauki alhakin ɗan'uwana Allah ya isa Allah ya isa” Yasa taɓar rigarsa ya share hawayensa sai kuma ya faɗin a gurin yana kuka. Har sai dai sauran ƴan'uwansa suka riƙashi, sai ya fisge kansa ya nufi ƙofa yana faɗin. “Bayan sun karɓi dubu ashirin na beli sai kuma su kawo mana gawa, ba zata saɓuba” Baba Dahiru yayi saurin riƙeshi. “Sulaiman ina zaka je cikin dare nan?” Komawa yayi ya zauna yana rawar ƙafa alamun masifa na tare da shi. Inna A'i ce ta zo ta riƙa Inna ta tasheta daga gaban Gawar Baba ta maidata can gurin ƙofar ɗaki ta zaunar da ita. A nan suka shiga tambayar Sakina yaushe suka kawo shi, kasancewar itace mai wayo saman da Jamila, cikin in'innar kuka ta zayyana musu abunda ta sani. Ni kan ina zaune gurin kamar kayan wanki komai ina ganinsa kamar mafarki, har kuma lokacin babu hawaye a idona balle alamun kukan. Habiba na gefena tana rusar kuka. Can ƙasa-ƙasa na riƙa jiyo muryar Baba Sulaiman yana faɗin. “Sai da ya faɗa min suna ta dukansa akan sai ya karɓa laifinsa cewar yayi satar, shi kuma ya rantse min da Allah ba zai amsa ba sai dai su kashe shi, amman da naje na samu ƴan sanda nan na ce mu mun yarda yayi satar kuma za mu biya, daker suka yarda zasu ba da belinsa dubu ashiri, da yamman mu ka cika musu kuɗinsu sai kuma su kawo mana gawa? Shiyasa suka ƙi bamu shi, suka ce sai dai su kawo shi da kansu ashe sun san sun kashe shi, kuma suka karɓe kuɗin, Wallahi ba zamu bar wannan maganar ba, ba zamu barta ba” Faɗa yake cikin kuka kamar ba mace ba, sai yana buga ƙafarsa yake da ƙasa. Magana da shi ta ƙarshe a police station ne ya dawo min a rai. _“Mahaifinku be yi sata ba Nawwara, kuma be taɓa yi ba, ki gamsar da ƴan'uwanki da wannan”- A take na ji idona ya cika da ƙwalla, kan kace kwabo sai ga hawaye suna saukowa daga idona kamar ba gobe, ban san lokacin da na kwara wani uban ihu ina kiran sunansa ba. “Baba! Baba!! Baba!!!” Mama ladi ta zo da gudu ta rufe min baki, sai na faɗa hannunta ina kallon fuskarta da ke min gizo kamar ta mahaifina... *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 8⃣ Riƙani ta yi ta tayar ta maida can kusa da Inna ta zaunar tana bani haƙuri da kalaman da za su sanyayamin zuciya. Kuka muke ta yi ni da Habiba, yayinda Inna ta rafka uban tagumi tana kallon gawar Baba. Baba Dahiru ne yaja janena dake kan igiya ya rufa masa. Haka muka zauna har garin Allah ya waye babu wanda ya runtsa. Su Baba Dahiru ne suka yi alwala suka tafi masallaci yayinda mu muka yi namu sallah a gida, bayan na gama na ɗauko alƙur'ane ina karantawa, izuwa yanzu bana da buƙatar wani kuka bayan wanda na yi jiya ya haddasa min ciwon kai da kumburewar idanu, ina jin yadda maƙota na nesa da na kusa ke ta shigowa suna jajantama Inna, wasu na san gulma ce ta kawo su tun da gari ma be gama wayewa ba amman har labarin ya zaga unguwarmu da ma unguwanin da ke kusa da mu. Bayan fitowa Masallci sauran ƴan'uwan Babana suka shigo maza da mata cikin har da Yakumbo. masu kuka na yi masu faɗa na yi, Baba Ayuba ne ya bada shawarar a ɗauki gawar Baba aje da ita police station a mayar musu, Baba Sulaiman kuma ya hana wai ba za a tagayar masa da gawar ɗan'uwa ba, idan aka yi haka ɗan'uwansa aka wulaƙanta. Daga ƙarshe suka yanke shawarar zuwa station ɗin ba tare da gawar Baba ba, a ɗakin mu aka saka shi sai aka rufe ɗakin duk muka kwaso muka dawo ɗakin Inna. Noor ya zo kusa da ni ya zauna, Jamila da Sakina kuma suka zauna gurin ƙofa suna ta aikin kuka kamar yadda Habiba ke yi. Ni kuma ɓa noce kaina ƙasa bana kuka kuma bana tunani kaina kamar fanko na ke jinsa, shigowar Jidda da Mahaifiyarta ce ta ɗaga hankalin kowa, saboda kuka da take kamar ita akayi ma mutuwar, sai gida ya ɗauki kuka muryarta muryar Habiba da Inna sai kuma Jamila da Sakina. Yakumbo ce ta katsa musu tsawa tana faɗa kan kuka da suke, musamman Inna da take ganin ita ya kamata ace ta rarrashe mu amman ita take kukan ma. “Mamaci addu'a yake so ba kuka ba, bawan Allah nan fa yana cikin gidan nan amman kuna ta masa kuka, kuka ai ba zai dawo da shi ba, ba zai muku maganin komai ba, amman addu'a zata iya sanyaya muku zuciya kuma ta canja lamarinku, sannan shi kuma Allah ya karɓa yayi masa rahama. Yanzu ke Hajara ke da ya kamata ace kin bawa yaran nan haƙuri, sai ki zauna kina kukan tare da su, Allah be yi wani dan wani ba, be yi Musa dan ku ba kuma be yi ku dan Musa ba, shi ya hallita abunda yasa masa rai yanzu kuma ya karɓi abunsa, gode masa ma ya kamata ku yi kuma ku yi haƙuri sai kuga Allah ya yi muku wata mafitar” Ba laifi kalamanta sun yi tasiri gurin Inna da har tasa hannu ta share hawayenta tana ta kokuwar tsayar da kukanta, Habiba kan kunne uwar shegu ta yi sai abunda ya cigaba, kusa da ni Jidda ta dawo ta zauna ta kama hannuna ta riƙe sai hawaye take, ni kan kallonta kawai na ke ina jin kaina kamar babu komai a ciki. Tun da suka ta fi basu dawo ba sai ƙarfe goma na safe har da ƴan mintuna, mutane da suka je tun hasken alfijir ba gama yayewa ba. Tare da tawagar ƴan sanda suka zo wanda hakan ya haddasa mana dandazo jama'a a ƙofar gida. Dpo ne ya shiga da kansa ya duba gawar baba tare da wani ƙaramin ɗan sanda mai ɗaukar hoton jikin Baba, bayan ya gama dubawa ne ya dawo gurinmu, a bakin ƙofa ya tsaya yana ba mu haƙuri tare da faɗar za a ɗauki mataki da ya dace. “Wacan ƴarsa ce?” Ya tambaya ganin ni kaɗaice na kasa ɗago kai na kalleshi tun da ya soma maganar har ya gama. Inna A'i ta nuna Habiba da Jamila da kuma Sakina “Eh da wannan da wacan da wacan, su kaɗai Allah ya bashi” “Allah sarki ku yi haƙuri zamu ɗauki mataki, yanzu haka mun sa an kama ƴan sandan da suka yi wannan aika-aikar kuma za a gabatar da su a gaban kotu In'sha Allahu” Ya ƙarasa yana ciro duba goma da uku ya miƙawa Jamila da ke kusa da shi, kana ya miƙe tsaye yana mana sallama. “Mu za mu tafi Allah ya sanyaya zuciyarku” Na yi zaton ya tafi hakan yasa na ɗago idona da ke cike da hawaye na kalli ƙofa, karaf idona sai cikin nasa, sauke na sa idon yayi ya wuce ƴan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119