Chapter 21
Chapter 21
ni dai abunda na sani ba shi kaɗai na ya yi lalata da ita ba, nasan kuma duk na faɗa mata cewar shi ne zata iya zuwa ta samu iyayensa wanda hakan na san ba zai mana daɗi ba, domin zasu iya ɗauka ko wane irin mataki a kan ɗan su ƙwalli ɗaya da suke ji da shi. Can ƙasa-ƙasa na hango muryar Inna tana cewa. “Habiba ta ci amanata kuma ta ci amanar kanta, ta zubarda ƙima da duk wani mutuncin da yake gidan nan, a yau na yi nadamar haihuwarta, baƙincikinta zai kasheni, ni ma nice na tafi ba mahaifinku ba, Allah be ƙaddara ya ga wannan abun kaico da wayyo a rayuwarsa ba sai ni, Habiba kin cuce mu...” Duk wannan furucin da Inna take akan kunnuwan Habiba saboda tana jikin ƙofa tsaye ne, sai da Inna bata iya ganinta saboda ta bata baya ne. Muna haɗa ido da ita sai ta bar jikin ƙofar ta nufi ɗakinmu. Da sauri na tashi na bita saboda irin hawayen da na hango suna zuba a idonta. Ko da na shiga na tarar tana ta saurin cire uniform ɗin jikinta ta saka wasu tufafin. Jin motsina yasa ta juyo da sauri ta kalleni. “Nawwara guduwa zan yi, ba zan zama dalilin mutuwar Inna ba, ba zan rasa Baba kuma na rasa Inna ba-” Ta juyo ta cigaba da haɗa kayanta. Ƙarasa na yi kusa da ita ya miƙar da ita tsaye na kama hannyenta da ke zafi sosai saboda zazzaɓi na riƙe gam, ina kuka kamar yadda itama take yi har ɗayanmu baya iya yiwa ɗan'uwansa magana. GOOD NIGHT.... 🤧 *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 1⃣6⃣ Haƙiƙa akwai ƙurciya a rayuwar Habiba, yana ɗaya daga cikin dalilin da yasa ta aikata abunda ta aikata, wanda take tunanin kamar mafitane, sai gashi ya zame mana matsala, yanzu kuma tana ganin kamar guduwa ta bar gida shi ma mafita ne, ni ko nasan duk yarinyar da ta gudu ta bar iyayenta lallai tana tare da na sani da kaico a rayuwarta. Ba zan bari ƴar'uwata ta aiwatar da wannan ƙudirin nata ba, ko da kuwa haka yana nufi salwantar rayuwar mahaifiyata ne, ba zan bari ta sake aikata wani kuskuren ba. Ƙoƙari nake na tsayarda kuka ta yadda zan ƙarfafa mata guiwa da rarrashi amman hawayen da ke min zuba sun ƙi bani haɗin kai. Idan har ban yi ƙarfin halin shiga tsakaninta da wannan kuɗirin nata ba, lallai zamu iya rasata wanda na san hakan zai iya sama sadiyar rasa Inna. Hannayenta na saki na share hawayena ina kallonta, cike da ƙarfin hali na ce “Babu inda zaki je Habiba, irin wannan tunanin na ki ne yaja miki kika jefa mu cikin wannan halin, yanzu kuma zaki sake aikata irinsa? Kina tunanin aikata wannan abun shine mafita? Ba zai canja komai ba, sai dai ma ya ƙara ɓata ran Inna har ta kasa yafe miki, mu kuma ki ja mana ɓacin suna, haka kike so?” Ta girgiza kai alamar a'a, muryarta a shake ta ce. “Ta ce ta yi nadamar haihuwata ni ce ajalinta, ba zata yafe min ba” Hannu na kai na sake riƙe hannayenta. “Zata yafe miki Habiba, ni ma uwace na san halin da Inna take ciki, akwai zafi idan wani abu ya samu ɗanka musamman mace, idan wani abu ya sami Noor bana iya yafewa kaina, bana iya controlling kaina bana iya juriya, kin san saboda me? Saboda Ina ƙaunar Noor, a duk faɗin duniya babu wacce zata gwadawa ɗa so kamar uwarsa, duk abunda Inna ta yi miki saboda tana ƙaunarki ne ke kanki kin san Inna tana son ki, karki yarda ki gudu idan har kika gudu babu ni babu ke har abada!” “Ba zan gudu ba, ba zan je ko'ina ba na miki alƙawari, ko da kuwa Inna zata yanka ni ne” Ya faɗa cikin kuka. Sai na zaunar da ita ina share mata hawayenta, tare da yi mata wasu kalaman da zasu ƙarfafa mata guiwa. Ban bar ɗakinba sai da na tabbatar kuka da take ya tsagaita, sannan na fito na shiga ɗakin Inna. Gurin da barta a nan na sameta sai wannan karon tana daga kwance ne, gurin da fuskarta take ya jiƙe da ruwan hawaye kamar an zuba ruwa a gurin. Daga inda na ke tsaye na soma mata magana ciki da ƙarfin hali. “Habiba ta aikata abunda ta aikata ne saboda tana tunanin kamar hakan shine mafita, ta aikata abunda ta aikata saboda Baba da ke da kuma mu duka, kin yarda da ƙaddarar da ta samu Baba har kika riƙa bani haƙuri, shin miyasa ba zaki yarda da wannan ƙaddararba...?” Tashi tayi zaune ta kalleni a tsawace ta amsa min “Saboda ita ta kai kanta” Na matsa kusa da ita “Akwai ƙurciya da tare da ni balle kuma Habiba, hankalinta da tunaninta be kai inda kike tunaniba, babu banbanci tsakanin wannan ƙaddarar da kuma wacan dukansu ƙadarori ne, babu wanda ya dace ya nunawa Habiba soyayya a yanzu fiye ke, babu wanda zai mata magana hankalinta ya kwanta fiye da ke” “Habiba ta ɗauko wata rayuwa wacce bata gidan nan ba, sam wannan ba tarbiyarmu ba ce” “Wannan kaɗai ya isa ya tabbatar miki da cewar ƙaddarace, ashe ko haka ya isa yasa ki rumgumeta ki nuna mata kina tare da ita” Ajiyar zuciya ta sauke kana ta kalleni “Kina da ƙarfin zuciya Nawwara, haƙiƙa Muhammad Noor ya yi sa'ar uwa” “Ƙarfi guiwata taki ce Inna, kin rigani zama uwa kin fini sanin komai a rayuwa” Wani dogon numfashi taja ta sauke tana cige baki ta ce. “Wani lokacin kaina ya kan kulle har na yi tunani ba dai-dai, Allah ya kan jarrabi bawa da abubuwa da dama har bawa ya ga kamar Allah baya sonshi” “Zamu jarrabeku da yunwa da tauyewar ƴaƴan ittatuwa da rayukan da dokiyoyi, ka yi bushara ga masu haƙuri (Masu jure waɗannan jarabce-jarabce) Waɗanda idan masifa ta samesu sai su ce (Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un) Mu ɗaga gurin Allah muka fito kuma a gare za a maida mu, kyakkawar yabo ya tabbata agaresu daga Ubangijinsu, haka Allah ya faɗa a ciki alƙur'ane mai girma, akwai kuma inda Allah yake cewa ‘Ko wane tsanani yana tare da sauƙi har ya sake maimaitawa Haƙika ko wane tsanani yana tare da sauƙi, sai kuma ya ce Fasbir sabaran jaamila wato ya kai Annabi ka yi haƙuri haƙuri mai kyau, Allah yana tare da masu a haƙuri. Inna duka waɗannan Allah ne ya faɗa. Kin tuna lokacin da na yi aure? Na fuskanci wulaƙanci da ƙalubale kala-kala a gidan aurena, har na fito na haifi Noor cikin baƙinciki da damuwa, na sake wani auren har na fara jindaɗi sai Allah ya karɓe abunsa, na sake dawowa cikin wannan wahalar, sa'anina da wanɗanda muka yi makaranta tare da su, duk sun zama manyan mutane har basa son abota da ni, ni kuma ina nan, amman hakan be taɓa saka ni na yi tunanin ko Allah baya so na ne ba ko da sau ɗaya, da ace Allah ya yi ni kafira da zan yarda Allah baya so na saboda komai na tara a duniyarnan zan mutu na bar shi naje ƙiyama na shiga wuta, amman kin ga yanzu zan iya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119