Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 74

Chapter 74

Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ba” Ya amsa masa yana saka Laptop din a mota, juyawa Jibril ya yi ya koma ciki gurin mutumen dazu. “Please ko kaji inda zata je? Ko kuma inda hadarin ya faru?” Mutumen da dan yi shiru sannan ya daga masa kai. “Ee na ji ta ambaci Specialist Hospital gaskiya ina jin ko can aka kai yaron ko kuma can hadarin ya faru” “Thank you” Ya juyo da sauri ya nufi gurin motarsa, driver seat ya nufa ya ce direban ya fita ya hau achaba shi akwai inda zai je, @360 ya fisgi motar kamar zai tashi sama, wani irin vibration jininsa yake yana jin kamar ya runtse ido ya gansa a cikin asibitin. “Dan ta...” Yana ta maimaita hakan ya iso Abuja road sai ya dauke hanyar da zata sada shi da Specialist, gudu yake sosai kamar dan shi aka yi titi ko kuma ance masa babu ababen hawa sai nasa kadai. Lokacin da zai kunna kai a gate din Specialist din sai da ya yi kamar zai buge wani magidanci da ke kokarin fitowa. Ko fakin din kirki be yi ba ya fito yana ta waiwagen inda zai shiga, tsabar rude daman can sau daya ya taba shigo asibitin loacin da yake farkofarkon zuwa sokoto sika yi wata mata tiyata. Da sauri ya nufi emergency wajen yan hatsari, har ciki ya karasa ya karasa inda Nurses suke ya muna masu id cart dinsa sannan ya soma tambayarsu ko an kawo wani. “Eh an kawo mutun daya yanzu” “Zai kai minti nawa?” “Ten haka yanzu yanzu” “Babba ne ko yaro?” “Gaskiya dattijo ne” “No wanda na ke nema karamin yaro ne yana tare da mamansa ina jin za ayi awa daya yanzu da kawo shi” “Eh an kawo wani yaro dazu, yana ciki bayan shi ma an kawo wani” Dayar Matar ta fada. “Bari na duba” Ya nufi ciki da sauri ya soma bin dakuna, sai gashi ya hadu da wani likita abokinsa. Shi ya rike Jibril dan hankalinsa gaba daya sama yake baya ganin kowa. “Jibril” “Dan Allah wani yaro na kr nema wanda aka kawo ya yi hatsari dazu” “Yaro ne sosai?” Ya dan yi shuru yana tunanin ta yadda zai amsa tunda ba sanin yaron ya yi ba. “Yeah yeah yaro ne” “Akwai wanda aka shiga tiyata da shi yanzu akwai kuma wanda ya rasu dazu, amman ba a fita da gawarsa ba saboda basu biya hospital bill ba” “Wait...” Ya fada sai ya fiddo wayarsa ya kira Nawwara duk da yasan ba zata bari ya karaso ba, ringing biyu aka daga da muryar Sakina tana masa sallama. “Ina Nawwara?” “Bata da lafiya” “Wacece ke?” “Ni kanwarta ce” “Kuna ina ne Nawwara tana ina” “Muna nan asibiti?” “Wani waje?” “Dakin Balaraba” Ya katse wayar yana kallon likitan. “Ina ne sashen balaraba?” “Ta can ne, ko shine yaron da ake neman jininsa aka zo diban na uwar ta suma?” Jibril ya rike. “Please zan iya ganin yaron” “Yes this way, amman an shiga tiyata da shi gaskiya ba zaka iya ganinsa yanzu ba sai dai a jira ya fito” Tare suka karasa sashen da ake yan tiyata, jikin Jibril sai rawa yake sosai ya so ya shiga amman likitan ya hanashi saboda tiyata ake masa kuma yasan irin matsalar da zai janyo matukar ya ce zai shiga yanzu. “Ka yi hakuri da sun fito zaka ganshi” Safa da marwa kawai jibril ya ke yana matsar hannunsa. “Jini ma ake nema garin bada jinin ne Mahaifiyar yaron ta yi ta amai daman da kuka ta zo, sai gashi ta sume mana dole muka kaita sashem Balaraba, kakarsa taje ta siyo” “Please Doc Ismail muje ka gwada nawa idan zai yi” “Okay yaron ya ji ciwo sosai gaskiya ya zubar da jini, amman yaron ka ne ko naga kuna da kaman sosai kuma yadda ka tashi hankalinka haka...” Be gama maganar ba Jibril ya rike shi “Da gaske muna da kama? Da gaske?” Ya gyada masa kai cike da mamaki, ko da suka karasa lab Jibril be sani ba saboda hankalinsa yana can gurin tunani. Sai da aka dibi jininsa kadan aka gwada ya bada result iri daya da na Noor sannan Doc Ismail ya kawo masa, Jibril na ganin takardar hawaye suka fara masa zuba jikinsa ya yi mugun sanye, sai da ya karantar result din ya fi a kirga sannan ya yarda da duniya yake, fashewa ya yi da kuka sai kuma ya yi saurin guntse bakinsa tunawa da inda yake, saman table ya aje takardar ya nufi wani bangare na lab din hannayensa a baya yana jin wani irin abu marar misaltuwa. “Doc Jibril ko ka fasa bada jinin ne?” Sai ya juyo da sauri ya dawo yana share hawaye abunda ya bawa kowa mamaki, sai dai su abunda suke dauka saboda yaron ya ji rauni sosai ne yake hawayen, har wasu na cewa wai kamar ba namiji ba namijin ma kuma likita wanda be kamata aga yana kuka saboda sun saba ganin tashin hankali. Dakin da ake dibar jiki ya shiga ya kwanta a saman kujerar nan mai kamar gado, aka saka masa abun diban jinin aka tasti leda biyu sannan ya tashi yana fadin. “Doc Ismail muje yanzu ko sun fito” “No Doc kai kansa kasan dole ka dan zauna yanzu na ga kamar a hankalinka a tashe yake” Tashi tsaye Jibril ya yi da zimmar tafiya, ganin hakan yasa Doc Ismail ya bishi suka koma gurin tare sai suka tarar ba a fito da shi ba har yanzu. Sai kawai suka zarce inda Nawwara take domin itama yana da bukatar ganinta, basu sha wahala wajen nemanta ba saboda farko farko take. Irin dakinnan ne da ake jera masara lafiya dama da hadu, tana kwance saman gadon asibiti idanuwanta a rufe kamar tana bachi ga drip an daura mata a hannu, Sakina na zaune a kujerar da ke kusa da ita tana ta hawaye. Kallonta yake sosai cike da tausayinta a nan Sakina ita ta samu damar kallonsa a take ta raya a zuciyarta cewar tabbas wannan baban Noor ne domin kamar har ta ba ce. Zaunawa ya yi gefen gado yana ta kallon fuskar Nawwara kamar yau ya fara ganinta, can kuma ya dago ya kalli Doc Ismail dake ta faman kallonsa da mamaki ya ce “A sama mata daki inda zata zauna ita kadai ta samu kulawa, if babu zan so ka mata transfer zuwa asibitina” “No nan din ma akwai” Gurin Nurses din ya nufa ya yi magana da su sai suka zo suka canja mata daki zuwa wanda take ita kadai sai dai shi kudinsa da daban ne. A nan ma ya dade yana kallonta sannan ya cire rigarsa yar sama kasancewar suit ne a jikinsa ya lulluba mata saman jiki. “Ki kula da ita please” Ya ce da Sakina sai kace ita Nawwara wata karamar yarinya ce. Tare suka fito da Doc Ismail har suka hadu da wani likitan Jibril dai be bi ta kansa ba dan hankalinsa yana can gurin dan da aka ce na Nawwara ne. Sun yi sa'a suna isa ana fitowa da shi dakin tiyata, Sai Doc Ismail ya tsayar da su saboda abokinsa ya samu ganin yaron, mutuwar tsaye Jibril ya yi a gurin

Table of Contents

Chapters

119 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});