Chapter 41
Chapter 41
Haba son miyasa zaka riƙa wahalar da kanka kana damuwa ga abunda har ga Allah baka da laifi? Bafa kai ka kashe yarinyar nan ba dan mai zaka damu kanka su suka kashe ƴarsu da kan su” Juyowa ya yi ya kalleta. “Momi ke kika siye gidansu Nawwara?” “What why would i?” “Lokacin da naje gidansu Nawwara ta yi wani furuci da ke nuna an siye gidansu kuma an basu kwanaki kaɗan su tashi ke ce ko Momi?” “Wato Mustapha har gidansu yarinyar nan kake zuwa fira? Yarinyar da basu da tarbiya ga shegen hassada ya yi musu yawa, dan Allah ka cire yarinyar nan a ranka Wallahi ba ajinka ba ce” “Da ace ni na sakawa kaina son ta da na cire shi cikin sauƙi ba tare da kanki kin sani ba, na yi iya ƙoƙarina na ganin cewar na gujewa soyayyarta amman sai na kasa, babu yadda za'ayi na sakawa kaina ƙaunarta Momi Allah ne ya saka min” Ya miƙe tsaye ya zuba hannayensa a ajihu. “Please Mom ki maida musu da gidansu, kuma karki sake yin wani abu da zai takurawa rayuwarsu, idan har baki tayani neman yafiyarsu ba to be kamata ki ƙara ɓata min suna a gurinsu ba” Yana kaiwa nan ya nufi ƙofar fita cikin yanayi marar daɗi, Hajiya ma miƙewa ta yi tsaye ta bishi da kallo har ya fice sannan ta ce “Wato revenge ɗin da zata ɗauka ta haɗa ni da ɗana ko? Uhmm Wallahi Nawwara kin deɓo ruwan dafa kanki, duk kika ce zaki shiga tsakanina da ɗana bake ba kaf ɗanginku sai na hana musu zama lafiya, kuma Wallahi ɗana ba zai taɓa aurenki ba ƴar matsiyata kawai” faɗa take tana huci tsabar jin zafin ɗanta ya kamu da son Nawwara. Ɗakin ta nufi tana da bala'i har su Zarah da Ikram suka fito ɗaga ɗakinsu jinyo muryarta tana matsifa. *** *** *** Around eight am kowa ya hallara a dinning ɗin cin abincin safe ban da Mustapha, hakan be damu Hajiya ba domin ta san halin da ɗanta yake ciki, sai kawai ta cigaba da jera kayan abincin tare da su Ikram da kuma Ma'u mai aikinta. Fitowar Alhaji ne yasa Zara dake ɗaki fitowa domin yin breakfast ɗin, ganin babu kowa a kujerar Mustapha yasa Alhaji ya kalli uwargidansa ya ce “Yau ma ba zai yi breakfast ɗin ba?” Ikram ta yi karaf ta ce “Ai daman sai tara yake karyawa” Hajiya kuma ta taɓe baki tana cigaba da haɗawa Mijinta tea ta ce “Ai ina ganin tsakanin jiya da yau in ban da ruwa babu abunda Mustapha ya ci, ko jiya be fita aiki ba sai sha biyu na rana be dawo gida ba sai da isha'i” Kallon rashin fahimta Alhaji ya yi mata yana ɗaukar tea da ta aje masa ya kurɓa “Saboda mai?” “Uhmm saboda yarinyar nan mana” Wani dogon tsaki Alhaji yaja ya kalli Ikram a fusace ya ce “Jeki kira min shi wannan ai iskancin banza ne” Da sauri Ikram ta tashi ta nufi ƙofar fita, bata ɗauki dogon lokaci ba sai gata ta dawo falon tare da Mustapha dake cikin shigar kayan bachi. “Good morning Dad” Ya faɗa murya can ƙasa-ƙasa kamar wanda baya son magana. “Seat” Alhaji ya faɗa ba tare da ya amsa gaisuwar da ya yi masa ba, ba musu Musyapha yaja kujera ya zauna yana fuskarta Daddynsa, mahaifiyarsa taja kujerarta ta zauna tana kallon ɗanta a natse Alhaji ya fara magana ta yadda ɗan nasa zai fahimta. “Mustapha ka daina damunka kanka nayi imani har ga Allah baka da laifi akan wannan lamarin, saboda ba kai ka kasheta ba iyayenta ne silar mutuwarta. And a part from her sister ka aje shi a gafe domin ba tsararka ba ce, idan ma aure kake so ka nemo ko ƴar wani gidace ni zan aura maka ita amman ba dai wannan yarinyar ba” Sauke idonsa ya yi ya kalli tea ɗin da Ikram ta aje masa a gabansa sannan ya sake data kai ya kalli mahaifinsa ya ce “Dady ita kaɗai ce macce da nake so” “No Look Son yarinyar nan ba ƴar gidan mutunci ba ce sannan aurenta biyu fa kai kana sauranyinka ka ce zaka aureta, after that yaron dake hannunta yanzu ana zargin shege ne fa bashi da uba, wasu ma na cewa babu wani aure da tayi zaman banza ta yi abuja ta dawo da ciki sai wannan auren da ta yi na biyu, ba ƴar gidan tarbiya ba ce Mustapha ƙara ka auro ƴar mutunci kuma ƴar gidan mutunci” Mahaifiyarsa ya kalla domin yasan ita kaɗai ce zata iya faɗawa Daddynsa wannan maganar, kallon mahaifinsa ya sake yi “Amman ina fatar Momi ta faɗa maka ni na lalata ƙanwarta ko?” Alhaji ya yi saurin girgiza kai. “No no son ba kai ka ɓata ta ba, daman can yarinyar lalatacciya ce, mahaifinta ma ance sata ya yi da aka mashi aka masa shegen duka har ya mutu....” Zarah dake aikin tsire baki tayi karaf ta ce. “Wallahi sam yaran gidan nan basa da mutunci ko kaɗan” Tsawa Mustapha ya katsa mata. “Idan ana maganar tsakanin Uba da ɗa ki daina saka bakinki a ciki” Momi ma ta katsa masa tsawa. “Ta daina saka bakinta iya ba ƴar'uwarka ba ce? Wai mi yake damunka ne Mustapha?” “Nima ban sani ba, kawai ni dai abunda na sani zuciyata na son Nawwara” Ya amsa mata da cikakiyar gaskiyarsa, shi kansa a yanzu ba zai iya ayyana abunda yake damunsa ba, kawai dai yana samun kansa cikin wani kalar yanayi da be taɓa samun kansa a cikinsa ba. Alhaji ya buga tebur ɗin da ƙarfi “Ba zaka aureta ba Mustapha, ana nuna maka hanya kana ba haka ba, ka bar ganin kai kaɗai na haifa zan iya shafe labarinka a doron ƙasa matuƙar ka zaɓi yarinyar can ƴar nasara mutunci” Miƙewa ya yi tsaye ya nufi ƙofar fita ba tare da wata kalmar ta ƙara fitowa daga bakinsa ba. “Could you see this?” “Na gani, ni gani nake kamar ba banza suka barshi ba, dan ni ban taɓa ganin yarimyar da Mustapha ya zo ya ce min yana so ba duk wanda na gansu tare zai ce abokiyar aikinsa ce ko abokiyarsa, amman be taɓa buɗe baki ya ce min ga wacce yake so ba sai wannan zagalar, duk yabi ya canja saboda wata ƴar iskar yarinya, jiya ma haka ta zugoshi yazo ya rufeni da masifa wai na siye gidansu, ni kuma ban san na siye wani gida ba wata ƙila so take ya ɗauki maƙudan kuɗi ya ɗanka mata” “Bari ai zamu saka ƙafar wando ɗaya da shi” “Da shi kuma? Sai dai da su ai su suka susuta naka yaro, shi kaɗai fa Allah ya bamu idan ka saka ƙafar wando ɗaya da shi ai abun akan mu zai koma” Ƙwafa ya yi ya cigaba da shan tea ɗinsa yana ta huci. *** *** *** JIBRIL POV. Be bar kamfanin ba sai tara na dare, ko da ya isa gida jikinsa da mugun nauyi kamar wanda ya yi wani aiki, bathroom ya shiga ya sakarwa kansa shower ya lumshe ido yana sauraren yadda tsanyin ruwa ke ratsa jikinsa. ‘Nawwara will never ever ever forgive Jibril for
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119