Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 20

Chapter 20

Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

min kyautar murmushi. “Da alama ke baƙuwace a nan” “Haka ne, yau zan fara” “Haba shiyasa” “Mi kika gani hala?” “Naga kin yi sallama ne, ai a nan ba a sallama ba a gaisuwa saboda mai Kamfanin baya buƙata, idan kika ga ana fira da juna tau angama aikine ko kuma an fita can waje” “Tau shi kuma haka yake” Ta yi dariya tana nuna min camera. “Ki yi a hankali, Camera tana ɗaukar komai” Security camera ce daga gabanmu tana ɗaukar komai, sai na yi saurin gumɗe bakina na ɗauki kayan aikina na yi gaba. Na ji wuyar aikin sosai wata ƙila saboda ina farkom farawa ne, ko kuma saboda ɗakunan da aka haɗani da su suna da girma sosai, ga kuma gyara kofuna da jerawa bayan na gama ƙirgasu, sai da na gama sannan naje gurin da ake rubutawa na rubuta ko nawa na tarar sannan na nufi gurin aje kayan aikin na aje, na aje na kaiwa mutumen jiya wanda yace na kawo mashi ƙananan hotona, ɗaya ka karɓa ya saka a file sannan ya karɓi ɗayan na saka min a katin sheidata na rataya a wuya sannan ya ce min. “Idan kina da account ki rubuta a nan, idan kuma baki da shi zan cika miki wata takarda sai ki riƙa karbar albashinki hannun kashiya” “Gaskiya na daɗe ban yi amfani da shi ba, ina tunanin yanzu ma baya aiki” Wata takardar ya ɗauko ya yi rubuce-rubuce sannan ya bani na saka hannu sai ya maida takardun ya aje, ya ce “On 25 zaki riƙa zuwa gurin kashiya kina amsar kuɗin albashinki 12k” “Tau na gode” Na juyo duk da ban tambaye shi iya kashinyan yake ba, na fito daga gurin gaba ɗaya. A ƙaton agogon da ke reception na ga 12:14pm, lallai na daɗe ina aikin nan, sai da na saka hannu kuma na rubuta lokacin da na gama aikin sannan na nufi gurin da Hijabi yake na ɗauka, ina sakawa na ji mutun a bayana. “Nawancy” Da sauri na juyo na kalleshi. “Ka ganni ne kamin na saka Hijab?” Sai kawai ya ƙyalƙyale da dariya ya ɗora min ɗari biyar a lokar dana ɗauki Hijabina. “Allah dai ya bar min ke, ga wannan ki hau Napep, a sauka lafiya” Sai ya kama gabanshi ya yi tafiyarsa. Cike da kunya na fito na daga cikin kamfanin ita tunanin anya zan iya aikin nan zuwa? “Sannu ƴar'uwar yau nima na ti latti gama aiki” Na kalli mai min maganar da ke gefena na dama fuskarta ɗauke da murmushi, yarinyar ɗazun ce, sai dai wannan karon ita ma tana sanye da Hijabi, hakan yasa nima na yi mata murmushi. “Da wuri kike gamawa kenan?” “Eh gaskiya ten na ke gama aikina. Sunana Amina ke fa?” “Nawwara” “Suna mai daɗi” Sai duk muka yi dariya, muna ta ɗan taɓa fira da ita kamin motar da ta wuce mu ta dawo dai-dai mu ta tsaya. “Nawwara” Jin muryar Zinatu yasa na yi saurin kallon motar, ita ce hakimce a motar idonta sanye da baƙin gilashi. “Zinatu Ya kike?” A maimakon ta amsa min sai kawai ta jefo min tambaya. “Me kike a nan?” “Aiki” “Aiki aiki aiki wane irin aiki?” “Mopping” “Nice amman yau kika fara ko?” “Eh” “Good kowa zai ji muna aiki a guri ɗaya Sai dai ba level ɗaya ba, and people may not know the different, congratulations” Ta tashi gilashin motarta ta kunna kai zuwa harabar da aje motoci. Maganar ta sosa min rai har Amina ta lura da hakan. “Kin santa ne hala?” “Eh tare muka yi primary school” “Allah sarki” Kamar ta ce wani abu sai kuma ta yi shiru, muka cigaba da tafiya. A gurin hawan Napep muka rabu ni na ɗauki hanyar gidanmu ita ma ta kama hanyar na su gidan. Kamar kullum a inda aka sake sauke ni na sauka na ƙarɓi canjina na nufi gida, zuciyata cike da tunanin kalamin da Zinatu ta yi min, bana son fassarata da wata fuskar da kuwa da kasancewar na san halin na tsanar mutane irina da ta yi wato talakawa, haka kawai na samu kaina da faɗuwar gaba wata ƙila na tunanin da nake ne, sai da na shiga gidanmu na fahimcin faɗuwar gaban bana tunani ba ne na abunda zan tarar ne. ______________ SHARE, COMMENT AND VOTE. Sauran na ji wani ya ce short page ne na buge masa baki 😎 BEST REGARDS 🌹 Khadeeja Candy💜.. *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 1⃣5⃣ Habiba ce kwance tsakar gida amai na gefenta da alama yanzu ta gama shi, domin Inna ta ɗauki makwashi da tsintsiya ta je ɗebo ƙasa. Da sauri na ƙarasa kusa da ita jikina a mace na dafata. “Sannu Habiba mi ke damunki” “Wallahi kaina ne ke ta ciwo ban ma iya dawowa daga makaranta ba sai da malaminmu ya kawo ni, sai faman aman na ke, kuma bakina babu daɗi” Samun kaina na yi da kuka marar sauti, hawaye na bin fuskata kamar babu gobe. Na samu kaina cikin wani irin tashin hankali wanda ban taɓa samun kaina a ciki ba. “Ai zata samu sauƙi ina jin malaria ce bata sake ta ba” Inna ta faɗa ganin ina kuka, sai faman rufe aman take. “Allah yasa malaria ce, Allah yasa ta tabbata malaria ce ba ciki ba” Maganar ta fito daga bakina kamar antseni. Hakan yasa Inna ta kalleni “Nawwara, akwai abunda ya kamata na sani ne?” Na yi saurin girgiza mata kaina hankalina a tashe. “Babu babu komai” Ta saki tsintsiyar hannunta, ta kalli Habiba da ta soma kuka daga inda take kwance. “Akwai abunda kuke ɓoyewa ne?” Na girgiza mata kai alamar a'a. Amman bata yarda ba. Ta soma ƙirga da hannunta. “Tsaya dakata, Habiba tana da ciki kenan?” Habiba ta yi saurin tashi zaune ta matsa gefena kamar zata shige jikina tana girgiwa Inna kai. “A'a Inna” Ta faɗa cikin kuka, kamar yadda nima na ke kuka. Sai ina ta kalleta idonta cike da hawaye ta nunata da yatsa. “Kina da ciki Habiba, na lura da haka domin yanayinki ya canja gaba ɗaya, amman saboda karna munana zato a gareki yasa ban bari zuciyata ta ƙawata min wannan ba, ashe yaudara kuke ke da ƴar'uwarki, na shiga uku na lalace ina kika samo shi?” Ta ɗora hannu saman kai ta nufi ɗaki tana kuka. Hakan yasa na cire Hijabin da ke jikina na aje a gurin tare da wayata na rufe mata baya. Safa da marwa na tarar tana yi a cikin ɗakin tana kuka, kamar jira take na shigo sai ta rufeni da maganganu marar daɗi. “Kun cuce ni Nawwara, wannan ba tarbiyar gidan nan ba ce, ina kuka ɗaukota? Kun ƙara shafa mana baƙin fenti acewa mahaifinku ɓarawo ku kuma a kiraku ƴan iska, wayyo Allah na” Ta faɗi tsakar ɗaki tana kusar kuka. Kusa da ita na ƙarasa na ɗafa ina kuka na ce “Wallahi ba mu watsar ba Inna, ita ma yaudararta aka yi” “Waya yaudareta? Faɗa min waya rusa mana ɗan farincikin da ya rage mana?” A nan na feɗe mata daga biri har wutsiya akan abunda ya faru, sai dai ban labarta mata cewar Mustapha ne ya aikata mata haka ba, saboda bana tabbacin cikin nasa ne ko ba nasa ba

Table of Contents

Chapters

119 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});