Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 30

Chapter 30

Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

secretary sa dake ta kokuwar fitar da ni hannu, ya yi masa alama da ya fita sai ya juya ya fice yana ja ƙofar office ɗin. Shi kuma ya taso da sauri ya doso inda na ke yana kira sunana muryarsa har rawa take. “Naaa...Naww...Nawwarraa....” Tafin hannuna na kama taɓa sai ya yi saurin kai shi gefen fuskarsa ya lumshe ido, sai hawaye suka zubo masa. Fisge hannuna na yi ina yin baya-baya, Tabbas shine, shine mutumen da ya yi nasarar canja ni daga mutum zuwa mutum mutume, shine mutumen da ya ce yafi ƙaunar ganin mutuwarsa sama da ni, shine mutumen da ya kirani ƴar talakawa marar daraja, shine mutumen da daya wulakanta ni ya sani a rana kuma yasa duniya ta zargeni, shine muteme da ya yanke min duk wani jindaɗi ma rayuwar duniya, shine mutumem da ya fara saka ni a ɗakin kuka da baƙinciki. Kai na nake girgizawa ina cigaba da yin baya-baya shi kuma yana matsowa kusa da ni, duk ya rikice kamar zai cinye ni, idonsa har sun soma canja kala, jikinsa na ta rawa hawaye kuma na ta aikinsu a fuskarsa. Muna haka Mutumen da ya taɓa tambayar sunana a wacan lokacin da na ke aiki ya shigo, shi ya kai hannu ya dafe masa ƙirji saboda kar ya ƙaraso kusa da ni, ni kuma na juya da gudu na fice ina kuka, ina jiyo sautin muryarsa yana kiran. Da kuka na sauko ƙasa na ban tsaya saka sunana ba na nufi gurin da Hijabi ya ke tare da wayata na ɗauka na saka na fice ɗaya ɗaga cikin mutanen da suke reception na ta kirana wai na zo ga saƙo amman nayi banza da shi ina ta aikin gudu da kuka. Sai da na yi nisa da kamfanin sannan na fara tafiya ina hawaye, tare da tambayar kaina wasu tambayoyin da ba ni da amsar su. ‘Shi da yake likita miya kawo shi nan? Daman ƙamfanin na su ne? Daman shi ne mutumem da Bilal yake faɗa min, miyasa ban gane shi ba a lokacin da Bilal ya faɗa min suna da Asibiti? Na taɓa jin ƙamshin turarensa miyasa ban ga ne shi ba? Ya faɗa min yana da tattoo miyasa ban ga ne shi ba?’ “Lallai ke wawuyace Nawwara” Na furta a fili hawaye na min zuba, yau kan ƙasa na kama hanyar gida duk kasancewar akwai tazara mai tsawo tsakanin unguwarmu da kuma inda kamfanin ya ke, amman baƙincikin da ke raina ba zai bari na iya tsayawa na tari abun hawa ba. Ƙarar tsayawar motarsa ce ta riƙa ta dawo min kamar a yanzu ne abun ya ke faruwa, irin yadda ya fisgoni ya jefar gefen titi ne ya riƙa min yawo a ƙwaƙwalwa. Wani irin jiri ne na ji na ɗibeni sai na ji ƙafafuna kamar an cankesu an ja ni, duhu na soma gani, ko kamin na kai ƙasa numfashina ya daɗe da barin jikina. ___________________________________ Dogon shafi kamar yadda kuke bukata 😂 Dan haka nima dogon comment na ke son ji idan ba haka ba next chapter sai nan da one week kuma short chapter 🤷 Ko wanenen wannan mutumen ne? Bari nima na bi Nawwara na sha labari 😉 #COMMENT #VOTE #SHARE *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 2⃣1⃣ JIBRIL POV (Point of view). Sanyi da yaji a tafin hannunta ya tabbatar masa da ita ɗin ce, hawaye ke zuba a idosa ba tare da ya san suna zuba ba, baya-baya take tana hawayen da yake jin ɗigarsu har cikin ransa, a hankali ya ke maye duk wani footsteps nata da take backwards, ga wani irin abu da ke jansa na ɗimaucewa da al'ajab ɗin ganinta kamar zai fita hayyacinsa he just can't believe Nawwara ce yau a gabansa. Shigowar Siraj ya bata damar fita da gudu, shi kuma ya yi hanzarin binta sai Siraj dakatar da shi, ta hanyar ɗora hannunsa saman ƙirjin Jibril. “Calm down Jibril” Be saurari abunda ya ke faɗa ba ya ƙwala ma Nawwara kira da dukannin muryarsa yana mai jin kamar ya yi tsalle ɗaya na fisgota. Ya sauke idonsa da suka yi ja suka rine akan Siraj yana ambatar sunan Nawwara cikin wata irin murya mai cike da ɓacin rai. “Nawwara ce fa” “I know” Siraj ya amsa masa yana ta matsar da shi baya har ya zaunar da shi saman tebur burinsa. “Nasan zaka haɗu da ita tun ranar da na yi arba da ita tana aiki a kamfanin nan, ni ma dan bata san ni bane yasa ta zauna da ace ta san kamfaninka ne ba zata yi aiki a nan ba” Cewar Siraj Hannayensa akan kafaɗar Jibril, sai ya ture masa hannaye yana masa kallon mamakin furucin da ya taɓa masa a can baya. “Miyasa ka ce min ta mutu? Kasan iya shekarun da na ɗauka ina nemanta? Saboda ita na aminta na yi aiki nan saboda kawai ta taɓa rayuwa a nan garin, Siraj kasan yadda take da muhimmanci a gurina kuwa?” “Na sani wannan dalili ne yasa na ce maka ta mutu, saboda ka yi focusing akan abubuwan da ke gabanka, na yi nemanta har na gaji ban samu ba, amman tun daga lokacin da na ganta a kamfanin tana aiki nasan wata rana zaku haɗu” “So kasan tana aiki a nan kuma ka ƙyale baka faɗa min ba? Ban taɓa sanin kai maƙiyina ba ne Siraj sai yau” “Na ganta sau ɗaya lokacin da muke duba ɗakunanan ni da Zinatu” Miƙewa Jibril ya yi cike da ɓacin rai, ya nufi ƙofar zimmar fita, sai Siraj ya bishi da kallo yana faɗin “Ina keka tunanin tafiya? Gurinta? Ai ba zata taɓa saurarenka ba ko ka manta irin wulaƙacin da ka yi mata?” Tsayawa ya yi cak hawaye na ta cigaba da masa zuba kamar ba shi ba, abun ka da farin mutun har fatar idonsa ta yi ja. Tabbas ba zata saurareshi ba ba ma cancanci Nawwara ta kalleshi ba balle har ta saurare abunda zai fito daga bakinsa. ‘What can i do now? Oh God...’ Ya juyo cikin rashin kuzari ya zauna saman kujerasa ya dafe kansa yana lilo da kujerar. “Take this” Siraj ne ya yi maganar yana aje masa farar takarda mai ɗauke da Cocaine saman tebur. Jin ƙamshinta yasa ya buɗe ido ya kuma sauke idanuwansa akan cocaine ɗin, hannu ya kai ya yagi gefen takardar ya fara mata aiki kamar ba gobe, sosai ya shaƙeta ko da ya ɗago ƙasa da kuma gurin tsinin hancinsa ya yi ja sosai. Yana san cocaine ne kawai saboda ta zame masa jiki ba wai dan tana masa aiki ba, tun lokacin da tunani Nawwara ya sashi gaba ya addabe shi yasa ya fara shanta, saboda ta ɓatar masa da hankali, da wasa-wasa ta kamashi har ta zame masa jiki ta yadda idan ransa ya ɓace sai ya shata yake jin sawaba, izuwa yanzu kan ta daina masa aiki ajiki saboda sabon da ya yi da ita, ko ya sha baya jin komai sai dai kawai ya sha dan ta zame masa kamar a abincin. Miƙewa ya yi tsaye yana tsotsar pink lips ɗinsa sai wani numfashi yake kamar zakin da ya yi faɗa ya gaji, hannu ya ɗaga ya daki teburin da ke

Table of Contents

Chapters

119 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});