Chapter 25
Chapter 25
ake mopping? Wai miyasa idan zaku yi abu baku yinsa tsakani da Allah, yanzu idan gidanku ne haka zaki yi, aikin nan fa biyanku za'ayi amman kuka abu da kissa kamar kyauta kuke yinsa haka sam be dace ba, yau da safen nan meeting zamu yi da manyan mutane yanzu idan suka shigo suka duba yadda kamfanin nan yake ai sai kuja mana ɓacin suna” Yadda ta runtse ido take min masifa kamar bata san wacece ni ba, tabbas na bar ruwa saboda ga gurin nan har yanzu be bushe ba, sai dai ba da gangan na yi haka ba, na yi mopping ɗin ne a lokacin da hankalina baya gurin, sai dai ban jidaɗin yadda take ɗaga min murya ba kamar wata uwata. “Ki yi haƙuri zan kiyaye a gaba” Na faɗa abunda yake har a zuciyata shine, ƙawata sai dai a nan kuma ita ce babba a gurin aikina, kuma dole ne na bita idan har ina son cigaba da aikin. “Better” Ta furta tana ƙoƙorin juyawa sai ga wani mutun ya shigo shima cikin shigar suit sai dai na shi blue ne tsaɓanin nata da suke baƙaƙe. Har ya buɗe baki ya yi magana sai kuma ya fasa sakamakon idonsa da suka sauka a kaina. Bakinsa a sake yake kallona fuskaraa na nuna alamun mamaki, hakan yasa kunya ta rufe ni domin tun da na shigo kamfanin a yau ban samu kaina da jin kunyar tufafin da ke jikina saboda damuwata ta mantar da ni komai. Sai dai kallon da yake min ya ya karantar da ni da akwai wani abu, wata ƙila ya daba ganina da Hijabi yau kuma ya gan ni babu Hijabi ko kuma dai yana mamakin yadda na ke aikin ne, tau tsaya ma wai ni ina na san shi balle na yi tunanin haka ni dai fuskarsa bata min kama da wanda na sani ba, wata ƙila dai shi ya sanni ne kai sai ka ce wata ƴar film ko mawaƙiya. Ni kaɗai na ke ta tsaƙe-tsaƙe na domin kuwa Zinatu ta daɗe da ficewa ɗakin, yanzu daga ni sai shi ne sai kuma Amina. “Newcomer?” Ya tambaya ni kuma sai na gyaɗa masa kai. “Your Name?” Ya sake tambaya. “Nawwara” Ya rausayar da kansa sannan ya sake kallon na from head to toe sai ya juya ya fice. “Shine mai kamfanin?” Ma tambayi Amina bayan ya fice, sai ta zaro ido. “Tab mai kamfanin zai tsaya tambayar sunanki, ai yana zuwa gurin nan zai ɗaukeki mari sai kin manta hanyar garinku” “Saboda me?” “Saboda wannan kuskuren da kika yi” Na taɓe baki. “Ni kan ba zan yarda ya wulaƙanta ni ba, saboda kawai ina aiki ƙarƙashinsa” “Aiko idan baki ɗauki wulaƙanci ba, baki shirya aiki a kamfanin nan ba, amman na ga mutumen kamar ya san ki” “Ni ban ma taɓa ganinsa sai yau, da alama shima a nan yake aiki ko?” “Shi ma babba ne a kamfanin nan, kuma ance suna shiri da mai kamfanin sosai wai amininsa ne, ko meeting ne idan be samu damar zuwa ba shi yake turawa” Haka muka fito tana ta labarta abubuwa da dama akan kamfanin da kuma ma'aikatan gurin cikin har da Zinatu da take ita sabuwar zuwa, sai dai ita ta rigani zuwa da wata huɗu, yadda take ta yabon kirki da kuma halin Zinatu har sai da abun ya ban tsoro wata ƙila duk wannan mugun halin nata mu take yi ma shi mu da muke tsofin ƙawayenta. Komawa na yi ɗakin na gyara sannan na dawo na cigaba da aikina, bayan na gama na fito na nufi gurin da ake rubuta suna na rubuta duk abunda ya kamata ina kamawa sai ɗaya daga cikin mutanen da suke reception ɗin ya miƙa min wata farar takarda, ya bani wani file wai na saka hannu, bayan na yi karɓa na nufo gurin da na aje Hijabi na ɗauka na saka sannan na kama hanyar fita daga kamfanin ina warware takardar. Naira ɗari biyar ce a ciki sai kuma sunan Bilal a jikin wata ƙaramar takarda, na san ya yi haka ne saboda na nuna masa bana son na ganni babu Hijabi. Ƙasaitaccen murmushi ne ya bayyana a fuskata murmushin da na manta rabon da na yi irinsa. Ƙamarar takardar mai sunansa na ɗauka na jeta a bakina na taune zuciyata cike da shauƙi Bilal. Wannan shauƙin shi ya kawar min da komai na damuwata har na isa gida. Da sallama na shiga Jamila da Noor suka amsa min domin sune a tsakar gida, Inna tana ɗaki tare da Habiba. “Miya hana ku zuwa makaranta?” “Noor ne ya ce ba zai je ba” Cewar Jamila kamin Noor ya karɓe mata. “A'a Wallahi ita ta fara cewa ba zata je ba, Anti Sakina ce kawai ta tafi” “Daman haka kuke so, idan bana a cikin gidan nan babu mai matsa muku kuje makaranta” Da faɗan na shiga ɗakinmu, sai na samu Habiba ita kaɗai kwance ƙasa ƙafafunta lulluɓe da ƙaton kuma tsohon Bedsheet ɗin Inna. “Habiba” Na kira sunanta a hankali, sai ta ɗago ta kalleni amman da dukan alamu kamar bata cikin hayyacinta, domin alamu sun nuna hakan. Hannu na kai na buɗe bedsheet ɗin dake rufe da ƙafafunta sai ga jini a gurin kamar an juye jalkar manja, ba shiri na saki bedsheet ɗin na yi baya-baya dafe da baki ido a waje, zuciya mugun bugawa kamar an ce min ga mutuwata nan kusa da ni.! NOT EDITED *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 1⃣8⃣ Na yi saurin rufe bakina idona cike da hawaye na nufi waje da gudu, ɗakin Inna na shiga ban sameta a ciki ba, ina fitowa waje Inna na fitowa daga banɗaki tana riƙe da buta. Kallo ɗaya ta yi min ta ɗauke kai ta nufi ɗakinmu, ni kuma na rufa mata baya hankalina a tashe. “Inna kin ga halin da take ciki kuwa?” Ya gyaɗa min kai. “Ko minti talati ba ki yi da fita ba, ta fara zubar jini ina jin cikin ne yake zubewa” Tsugunawa na yi a gurin na dafe kai ina hawaye. “Inna bata cikin hayyacinta” “Dole ne zata yi haka saboda wannan ne na farko kuma kinga yarinya ce, amman zata warke zata dawo lafiya ƙalau” “Inna dan Allah mu kaita asibiti” Na faɗa ina fashewa da kuka, sai ta ce “Babu inda zamu je Nawwara, zata warke” Ta janye bargon ta soma gyara mata jiki ni ko ina duƙe a gurin ina aikin kuka. Haka muka wuni muka kwana babu wani canji sai ma ƙari, tun ina ganin tausayinsa har zuciyata ta fara raya min wasu abubuwa marasa kyau. Ita kanta Inna ta soma tsorata ganin mun kwana da ita a haka babu wani canji, ni ko na kasa zuwa aiki saboda ina ganin kamar idan na je na barta zan dawo na tarar ta mutu, ina jin kamar idan ina kusa da ita babu abunda zai sameta. Can da yamma abun ya fara zuwa da sauƙi da har ina maganar ko Inna bata so sai na ɗauke ta na kaita asibiti saboda gudun kunya ba zan bar ƴar'uwata ta mutu ba. Jikin nata babu ƙarfi amman hankalinta ya dawo, har ma ta ɗan jiro hannunta kaɗan ta ɗora saman nawa, kasancewar ina
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119