Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 26

Chapter 26

Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

zaune ne kusa da ita saman tabarma. Numfashi take wahalce gaba ɗaya idanuwanta sun canja kamar wata tsohuwa. “Sannu Habiba” Na faɗa cikin muryar kuka ina mai tausayin ƴar'uwata, sai ta yi min murmushi hawaye ya fito daga gefen idonta. “Ina Inna?” Ta tambaya daker cikin muryarta na marar lafiya. “Taje maƙota zata samo miki lafiya dubu” Ta yi shiru tana lumshe ido, hakan yasa na tashi na ɗebo mata ruwa, na ɗan ɗaga kanta na kai mata kofin a baki, ba laifi ta sha da yawa kamar zata haɗe kofin har mamaki na yi na ce. “Na ƙaro miki?” Sai ta girgiza kai alamar a'a, sai ta rufe idonta tana numfashi a hankali. Ganin haka yasa na miƙe tsaye domin naje na kira Inna sai na ji ta kira sunana. “Nawwara...” Sai na koma na zauna ina kallonta. “Na'am” Na amsa ina kallon idonta dake rufe. “Ance mace data mutu gurin haihuwa ana kyautata mata zaton samun aljanna saboda ta yi shahada, tau idan kuma mace ta muru gurin zubar da cikin banza fa?” Ji nayi kamar jiri ya ɗibeni, hawaye uku-uku ya soma sauko min, ta farkon ido da kuma tsakiya, sai kuma ta gefen ido. Me Habiba take nufi ne? Wannan wace irin tambaya ce take min haka? Bakina a sake nake kallon yadda take numfashi. Ina haka Inna ta shigo, da fari gabanta ya faɗi ganin hadda hawaye suke min zuba sai dai ganin Habiba ta buɗe ido yasa ta ɗanji sanyi har ma da yin murmushi ta zauna kusa da ita tana nuna mata kulawa irin ta ƴa da uwa. Ta tsorata lokacin da takai hannu ta gwale idon Habiba, ya yi ɗorawa kamar marar jini, sai ta kalleni. “Kamar bata da jini” Kai kawai na iya gyaɗawa mata, sai ta miƙe tsaye da sauri tana kiran Sakina. “Sakina zo ki siyo mata maltina da madara ta sha kamin muje asibiti” Da gudu ta shiga ɗaki ta ɗauko kuɗi ta bada a siyo mata maltina uku da madara ta bata, sai kuma ta dawo ta zauna kusa da ita tana kuka. “Na yi wauta Habiba yanzu zan kai ki asibiti, ban ɗauka abun har ya kai haka ba, kin zubar da jini da yawa” A wahalce Habiba ta soma magana. “Karki kai ni asibiti Inna, ko kin kaini mutuwa zan yi, kuma mutane zasu ji, na barku da damuwa, ƙara baki je ɗin ba domin Wallahi mutiwa zan yi-” Na yi saurin kai hannu na rufe mata baki, sai ta lumshe ido, Inna ta tashi a firgice ta fita daga gidan tana kuka, kamar jira take na janye hannuna daga bakinta sai ta ce. “Nawwara zan tafi na barki ke kaɗai...” Na sake rufe mata baki ina kuka. Sai ga Inna ta shigo. “Riƙata ga Napep can na na tsayar zamu kaita asibiti” Kamar waɗanda suka ɗauki takarda haka muka ɗaga Habiba, jikinta ya yi sanyi sosai ƙwayar idonta baƙar ta ɓata ɓat sai farin kawai kake gani. Cikin hanzari muka saka mata wasu tufafin muka saka mata Hijabi muka ɗauketa sai gurin mai Napep. Muna shirin shiga Napep ɗin Sakina ta dawo daga siyen madara da maltuna, tsabar hankalin Inna ya ɗauku bata ko iya karɓa ba muka kama hanyar asibitin uduth dake gawon nama, duk da da kasancewar mun san asibitin ta kuɗi ce. Gudu sosai mai napep ɗin ke yi amman kasancewar tsakanin unguwarmu da asibitin uduth akwai ƴar tazara sai da tafiyar ta yi mana nisa. Muna isa bakin gate ɗin asibitin, Habiba ta sauke wani irin ajiyar zuciya ta kwanto da kanta dake jikina zuwa jikin Inna, rai ya yi halinsa ƴar'uwata ta amsa kiran mahaliccinta...! I will updated 19 tomorrow morning. RIJF Habiba😭 *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 1⃣9⃣ Inna ta kai hannu ta kwanto da fuskarta zuwa saman hannayenta tana murmushi. Haske sosai fuskar Habiba take goshinta ya soma taruwa da gumi. “Allah ga yata nan, ta aikata kurkure kuma na yafe mata, ina roƙon ka Allah ka yafe mata, ka karɓi baƙuncinta, Allah ka zama gatanta bata da gata sai naka, yau ƴata ta koma gareka Allah kuma nasan ba ka yi dan ƴata ba, kuma ba kayi ƴata dan ni ba, Allah ga ƴata nan ta dawo gareka, ƴata mutuminyar kirki ce dukan abunda ta aikata ta aikata ne saboda mu, Allah ka yafe mata, haƙiƙa kai mai yawan gafara ne” Inna ce take maganar tana shafa fuskar Habiba, hawayen idonta na zuba a fuskar Habiba. Sai kuma ta ɗago ta kalleni. “Kin ga abunda na aikata ko Nawwara? Saboda gudun kunya na kashe ƴata, ba a tambayar Allah miyasa ya aikata abu, abunda ya ga dama shi yake aikata a sanda ya so ga kuma wanda ya so, amman da ace ni ce na mutu a wannan lokacin zai fi, ko ba komai ni naga duniya Habiba ko yanzu take tasowa, Habiba ƴarinyar kirki kin samu rana, mutane da yawa suna fatar mutuwa a cikin wannan ranar ta jumma'ah-” Tsakanin Habiba da Inna sai na rasa wanda zan tausayawa, Habiba da ta bar duniya da ƙirciyarta ko kuwa Inna da zata shiga wani tashin hankalin a dalilin rashinta? “Na rasa *RAI BIYU* Ran mahaufinku da kuma na ƴar'uwarku, na mahaifinku saboda zalinci na ƴar'uwarku kuma saboda talauci, Allah na gode maka” Mai napep ɗin ya juyo ya kalletaa dai-dai lokacin da ya faka napep ɗinsa bakin ƙofar emergency,idonsa cike da ƙwalla ya ce “Ta mutu ne?” Sai ta ɗaga masa kai. “Juya mu koma gida daman ta ce karna kawo ta asibiti” “Da kin bari an dubata ko dogon suma ta yi” “Jikina ya bani ƴata ta tafi har a bada, sai idan na iskota” Shi ne ya matsa har aka fita da ita aka shiga da gawarta emergency, likitoci biyu suka dubata suka tabbatar mana da cewar ta mutu, sannan suka saka mana ita a motar ɗaukar gawa na asibiti saboda tausayin halin da suka ga muna ciki, mai Napep ɗin kuma ya ƙi karɓar kuɗinsa sai kuka yake kamar ƴar'uwarshi ce ta mutu. Ni dai bana iya aikin komai sai na kuka har muka iso gida. Jiniyar motar asibitin ce ta ɗago hankali kowa izuwa gidanmu, kan kace kwabo maza da yawa sun taru ƙofar gidanmu cikin har family Babanmu na babban gida, sai kuma family Inna maza da mata wanɗanda suke unguwar da kuma waɗanda bama da wata tazara mai nisa tsakanin unguwarmu da ta su. “Miyasa ta? Tun yaushe ne bata da lafiya?” Shine abunda kowa yake ta tambaya, masu kuka na yi, ciki har da kawayenta na makarantar islamiya da boko, tsakanin Sakina da Jamila bana iya banbance waye ya fi kuka a tsakaninsu, babu abunda ya fi bani tsoro kamar Noor da ya koma gefe ɗaya ya zauna ya natsu sosai ya kasa ko da guntun hawaye. Jidda ce ta shigo gidan da gudu tana ihu kamar zata tashi gidan, kuka take sosai tana kiran sunan Habiba kamar zata dawo da ita. Inna kan hawaye kawai take iya yi kamar yadda nima nake. Can kuma sai muka ji muryar Noor ya saka kuka ya yi waje da gudu yana kiran sunanta. “Wayyo Mama Habiba-” Ɗana ƙarami ne amman yasan mutuwa, yasan duk wanda ya tafi baya taɓa dawowa yasan ya

Table of Contents

Chapters

119 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});