Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 29

Chapter 29

Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kamar ƴar'uwata tana kusa da ni. Sai da na yi ma Inna sallama sannan na fita bayan na yi addu'ar fita daga gida. Bana baƙinciki ba farinciki na isa gurin aikin, kamar yadda nake a baya, sai da na fara zuwa na rubuta sunana da lokaci na aje hijabina da wayata a inda aka tanada domin aje irin waɗandanan abubuwan sannan na domin sai sannan na nufi gurin aikina, ina cikin aiki na ji muryar wani namijin yana faɗin “Khadija Musa Kafinta you're fired” Da sauri na juyo na kalli mai maganar yana sanye da black suit hannunsa riƙe da file. “Saboda me?” Na tambaya cike da mamaki. “Saboda rashin zuwa da kika yi, shugaba baya son haka, kuma ya ce be yarda da rahoton da aka bada cewar baki da lafiya ba” A take raina ya ɓace sosai, taya zai ce be yarda ba shi beda uzurine hala! Sai da na fara aiki za a ce an koreni, ni ko ba zan yafe haƙƙina na kwana biyu da na yi ina aiki ba. “Na ji an koreni amman a bani kuɗina na aikin da na yi na kwana biyu da rabi” “Kwana biyu da rabi?” Ya maimaita fuskarsa a haɗe. “Ee ai na yi aiki sau biyu a wannan kamfanin kuma yanzu na yi rabin aikin, dan haka a biyani haƙƙina” Ta yadda na yi masa maganar ya fahimci ina cikin zafin raine, domin a hasale nake ina katsa masa tsawa, yasan duk ya yi wasan sake ce min wani abu zan haukace masa ne. “Kije hawa na biyar bi faɗawa mai kamfanin, ba ni zaki faɗawa ba” Ya faɗa yana juya ya fice, ni kuma na bishi da bala'i ina cewa. “Ai kai ya aiko dan haka kai zan aika” Can kuma na soma tambayar kaina, wai shi wannan mai kamfanin wane irin mutun ne, miya ɗauki mutane ne? Aiko Wallahi ba zan iya yafe masa haƙkina ba ko da be bani kuɗin ba sai na faɗa masa marar daɗi sannan na bar kamfanin. Haka na kuɗiri aniyar sai na nuna masa ahi ba kowa ba ne, kai ina ma son ganin shi wane irin hallita ne da yake wulaƙanta ɗan adam, wato shi wannan yana tunanin kamar ba zan iya ba shiyasa na ce naje ko? “Aiko zan baka mamaki” Na faɗa a fili, sai na saka ƙafa na yi shuri da bokitin da nake mopping ɗin ruwan suka watse a ƙasa na fice a fusace. Kai tsaye na nufi gurin da lifted take na danna ta buɗe sai na shiga na danna 5. Gadan-gadan na fita daga lifted babu tsoro ko kaɗan a tare da ni, wannan gurin ma kamar wacan yake sai dai wannan ko wane office a kulle yake, an yi rubutu an laƙa a saman ƙofar. Ɗaya bayan ɗaya na riƙa bin ɗakunan ina duba wai ko zan ga wanda aka yi wata alama ta mai kamfani amman ban samu ba. Har na juyo sai ga wani mutume ya fito daga wani ɗaki riƙe da files, tsaidashi na yi ina tambayar office ɗin mai Kamfanin. “Lafiya kike nemansa?” “Shi ya aika ya ce yana nemana” Wani kallo ya yi min daga sama zuwa ƙasa sannan na kalli sunana dake rataye a wuyana. “Sai kin hau Excavator can, zaki ga Office guda uku jera, a na tsakiyar zaki tsaya akwai wani maɓalli a gurin sai ki danna” Sai da ya gama min kwatancen sannan na lura Excavator ɗin dake can gefen dama da offices ɗin. “Na gode” Na faɗa inanufar gurin, shi kuma ta bi bayana da kallo. Ni ban kula shi ba na hau Excavator ɗin. Ina kawowa sai na hauye saman tile ɗin na ƙarasa gaban offices dake jera, a na tsakiyar na tsaya, dama na ni na hango maɓallin da yake magana a kai na kai hannu na danna. Wata ƴar tsuwa na ji sai wata fitila ta hasko saman kaina. “What do you want?” Muryar namiji ce mai tambayar, kaina na ɗaga saman ina kallon camera dake ɗaukata. “Ina son ganin oganku ne” “Ur Name?” “Nawwara” Bayan na bashi amsa da kamar minti biyu sai ya ce. “You don't have an appointment with him” “Amman shi ya ce yana son gani na” Na faɗa a tsawa ce ina kallon camera kamar ance mutumem ne a gabana. “Sorry Ma'am you're not in the list” “But he's the one who tell me to come and meet him here” Na faɗa cikin turancina na yan ƙaramar makaranta. Sai kawai ƙofar ta rabu biyu ta buɗe min, da ɗan tsoro na kutsa kai ciki sai na gano ashe cikin wani ɗan kumbo ne na ke ciki, sai da kumbon ya gama scanning ɗina sai muryar ta sake min magana. “Keep your passport inside the box” Muryar ɗazu dai ce ta yi min magana, sai na saka hannu na ciro hoton Habiba na saka cikin wani ɗan ƙaramin akwati dake gefena, sannan ƙofar ta buɗe min tana min WELCOME. Wani ɗan madaidaicin Office ne na samu kaina ciki shi ba babba ba kuma ba ƙarami ba, an ƙawatashi da kayan alatu, da gangan na hana idona kallon wasu abubuwa na office ɗin saboda karna manta abunda ya kawo ni. Matashin Saurayi ne zaune saman kujerar dake office ɗin, laptop biyu a gabansa a daga gefensa kuma desktop computer ce a aje, can nesa da shi kuma an jera wasu desktop computer har biyu da kujerarsu daban. Can a farko shigowa office ɗin an jera kujeru masu kyau na san ba zasu wuce na zaman baƙi ba. Matsawa na yi kusa da shi da jimma na fara masa masifa domin a haukana na ɗauka shi ne mai kamfanin, sai ya rigani magana. “Stay where are you, i have to call him first” Telephone ɗin dake kusa da shi ya ɗauka ya fara danna wasu numbobi, hakan yasa na yi janzarin ƙarasawa kusa sa shi sosai. “Sir a young lady... ” Yana fara magana na fisge telphone ɗin na fara tawa maganar domin nasan idan har ya faɗa masa zai ce shi be san da zuwana ba, ba zasu bani damar magana da shi ba. “Azzalumi macuci, ka koreni ai sai ka bani kuɗin aikin da na yi na kwana biyu da rabi kuma kaima baka wuce Allah ya ɗora maka ciwon ba-” “Nawwara...-” Ɗaga can cikin wayar ya ambaci sunana. Tun da muryarsa take daki kunnena yawun bakina suka tsinke, kaina ya fara jiri wani abu na ji na tsikareni tun daga saman kaina har cikin ɗan yatsan ƙafata, gaba ɗaya jikina sai ya mutu. Mutunen nata ƙoƙarin fisge telphone ɗin daga hannuna sai na saka masar na juya da gudu na nufi inda na ke hango wata ƙofa dake can dama da teburin mutumen amman nesa da shi. Da gudu na banki ƙofar na shiga, sai na samu kaina cikin wani irin ƙaton office mai cike da sanyin ac. Yana hakimce saman kujerar alfarma wani irin ƙaton tebur mai takardu da kayan kawata teburin office haɗi da system na gabansa. Ji na yi kamar ana zooming ɗina a take hawaye suka fara bin fuskata, na san idona ba gizo suke min ba, ba mafarki na ke ba. Daga saman kujerar da yake zaune ya ɗagawa

Table of Contents

Chapters

119 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});