Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 93

Chapter 93

Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kasheki kuma a kashe Noor saboda Noor ya ga fuskarsa lokacin da ya yi kokarin kadeshi da mota, ya yi nadanar hakan kuma ya ji bakinciki sosai da Noor be mutuba, daga baya kuma sai ya wani tunanin ya zo masa cewar miyasa be sa wani ya aikata ba sai shi ya aikata? Wannan ya tabbatar da cewar nan gaba ba da kansa zai je kashe ki ko Noor ba wani ko wasu zai sa su yi, yana tunanin idan ya yi haka shikenan ya gama da rayuwar Jibril sai kuma ya yi amfani da cocaine ya karasa halaka shi. Na san zaki yi mamakin jin haka ko kuma ki yi mamakin a ina na san duk wannan ko? Na sani ne saboda Siraj ya fada min, yana amfani da ni ne a matsayin wacce mahaifin Jibril ya yarda da ni, ya ce min zai aureni kuma duk abunda ya samu zai raba rabi ya bani rabi abunda yake kokarin yi yanzu ya mallaki nasa kamfanin ta karshin wannan kamfanin, a yanzu haka mahaifin Jibril ya sauke Jibril ya dorashi akan kamfanin kin ga ya fara samun dama kenan, ni kaina rayuwata tana cikin hadari domin mugun mutum baya yarda da kowa, ni kaina xai iya cutar da ni idan ya samu abunda yake so, saboda yana ganina kamar ba bahaushiya ba yasa yake son ya yi amfani da wannan damar ya cilla burinsa saboda yana ganin kamar muna da son kudi kuma idanuwana a bude suke, na masa na amince ne saboda na san idan har na ki amincewa zai iya kashe ko ya kulla min wani sheri saboda ya san na san sirrinsa, kuma a matsayin na wacce ke aiki karkashin Jibril ba zan iya fada masa wannan ba, bana da wata hanyar sai ta ki, ke kadai ce zaki iya hankaltar da shi domin ceton rayuwarki da ta danki da kuma ta Jibril har ma da tawa gaba daya, ki kuma tsirarta da Bilal daga sherin da yake kokarin laka masa, kin san idan wani abu ya samu Noor dole Jibril ya zargi Bilal kuma ba zai taba kyaleshi ba” Hannu nasa na rufe bakina sai kuma na sauke ajiyar zuciya, kaina ya yi nauyi sosai kalamanta sun min hawa har na rasa wanne zan fara tunani balle na samu abunda zan ce mata, ji na yi ta dafani. “Nasan yana da nauyi Nawwara, ki yi tunani akai, ban san abunda ya raba ki da Jibril ba, amman yana da kyau ki shiga rayuwarsa ko dan gaba ko kuma na ce ko dan danki, abu na karshe da zan fada miki shine Jibril yana son ki sosai da sosai, domin lokacin da Siraj ya sanar masa cewar kin mutu ya yi kamar na haukace, ba sai na gargadeki akan karki fadawa kowa wannan sirrin ba saboda ina ganin a mace mai tunani da hangen nesa na barki lafiya” Da ido kawai na bita har ta fice, sannan na dawo duniyar mamaki da aljabi anya zan iya wannan aikin kuwa? Mi ma zai kai ni taimakon mutumen da ya nemi salwantar da tawa rayuwar? Abu na farko da ya zo min a rai shine Inna dole ne na fada mata komai ko dan neman shawararta, cikin hanzari na tashi na fita waje gurin Inna. [11/8, 9:37 PM] +234 703 352 5246: *RAI BIYU...♥🖤* Wattpad @KhadeejaCandy 5⃣1⃣ Inna ta tsorata sosai da abunda na fada mata hankalinta duk sai ya tashi. “Taya zaki iya shiga cikin wannan lamarin Nawwara?ke fa mace ce ba namiji ba, kuma irin wadannan mutanen hatsarine rabarsu” “Nima abunda na ke ta tunani kenan! Ona ganin aiki zan sa Jibril ya koma sai mu koma tare kin ga duk wani taimako zan iya bashi ta nan kuma ina lurar da shi akan wasu abubuwan” “Gaskiya Nawwara ina jin tsoro, karki je ki janyo mana wani abun na daban kuma” “Babu komai Inna ba zan fito kiri da muzu na fada masa abunda yake faruwa ba, ta dabara zan yi” “Kina tunanin hakan ba zai haifar da wata matsala ba?” “Inshallah ba zai haifar ba” Ta kawar da kai ba dan ta yarda din ba, ni kuma ina ganin bana da wata mafita sai wannan. JIBRIL POV. Lokacin da Noor ya ji cewar Momynsa ba zata zo ba sai duk yanayinsa ya canja ya koma cikin jin bakinciki da damuwa, duk yadda Jibril ya so kar ya bata rai sai da Noor ya bata kuka ma sai da ya yi. A gado daya suka kwanta under one bedsheet, misalin biyu da rabi na dare Jibril ya farka ya shiga bedroom ya dauro alwala ya fito ya shinfida carpet ya soma sallah nafila da a yanzu ta soma zame masa jiki. Kuka ya yi sosai yana neman yafiyar Allah akan abubuwan da ya gabatar marasa kyau sannan ya roko Allah bukatunsa tare da neman shiriyar Allah. Be san yadda zai karanta qur'ane ba but yasan yadda zai yi iistigifari da hailala da kuma tasbishi da kuma salatin Annabi. Yana zaune saman carpet din har aka yi asalati sannan ya tashi ya fita zuwa masallaci. Misalin takwas da rabi Noor ya farka a lokacin Jibril na kitchen yana hada musu breakfast, ko da Jibril ya fito ya samu Noor tsaye bakin kofar bedroom yana ta kallon falon. “Good morning Noor” Sai kawai ya saka dariya kamar ba shine ya kwanta da fushi jiya ba, kuma ya rufe ido wai yaji kunya an gaishe shi. Jibril ya aje kayan da ke hannunshi saman dinning sannan ya nufo Noor ya duka daidai shi ya kama hannayensa ya rike. “Ka tashi lafiya?” “Lafiya kalau, Dady na manta ban tashi ba sai yanzu” “Yeah ai kara ka yi bachi mai kyau ka samu ka huta ko?” “Momy da wuri take tada ni na yi sallah” “Yanzu ma ai lokaci be kure ba muje bedroom ka yi sallah” Tare suka shiga bedroom din Jibril ya taimaka masa ya wanke bashinsa sannan yaa yi masa wanka ya yi alwalah sannan ya daura masa tawul suka fito yana dauke da shi. Ko da ya fito wayarsa na ringing da sauri ya dauka ya kara a kunne. “Assalamu Alaikum Malam, okay gani nan fito” Sai ya zaunar da Noor saman gado. “Jira ni a nan ina zuwa” Number Rabi ya nemo ya tura mata sakon daga bisani ya yi mata transfer na kudi i zuwa account dinta dan ta siyoma Noor tufafi, ko da ya fito Malamin na tsaye waje kusa achabansa yana jiran fitowarsa, cikin girmamawa Jibril ya mika masa hannu suka gaisa sannan ya dora masa da. “Na san yau ya kamata ace mun fara but yau ina tare da yarona kuma yanzu idan mun gama karyawa zan kaishi gida, so ina baka hakuri zuwa gobe sai mu fara, kuma in fa hali ina son bayan mun yi da safe mu yi da yamma” “Ba matsala, zamu iya farawa gobe din Allah ya kaimu amman kamar wane lokaci?” “Irin takwas na safe haka, da dare kuma tara na dare nasan bayan wannan lokacin ina gida, sai salarinka nawa ake biyanka per month?” “Aa ranka ya dade bana son sisinka, zan koya maka komai saboda da Allah” “Kai amman ina godiya sosai Allah ya saka

Table of Contents

Chapters

119 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});