Chapter 52
Chapter 52
sokoto amman mutumen kebbi ne, acan yake zaune da duk familynsa, sai ya bar ni nan, ita kuma yana zuwa can inda take a kebbi. Iyayensa basa jindaɗin zama da matarsa irin matan nan da basa ragawa uwar miji da ƴan'uwanta ko kaɗan duk da ba guri ɗaya suke ba, wannan dalilin yasa mahaifiyarsa ta buƙaci ya maidani kebbi kusa da ita saboda ta yaba da tarbiyata a ɗan zuwan da muke ina gaisheta. Sai ya tattara ya maida ni a kebbi tare da Noor, su kansu family ɗinsa suna son Noor kamar ɗansa yan'uwansa haka, ga mahaifiyarsa tana mugun so na ni da ɗana saboda ina kyautata mata sosai, ɓari na biyu a gidan Faruk amman Allah be bani haihuwa ba, aiko ranar na ga gata a gurin danginsa da shi kansa kamar su haɗeni saboda tausayi. Muna haka kwatsam labarin mutuwarsa ta same mu sanadiyar haɗarin motar da ya yi a hanyarsa ta zuwa sokoto gurin aikinsa. A ranar nima sai da na yi kamar zan mutu saboda kuka, a nan gidan na yi taƙaba na gama familynsa suka riƙe Noor kamar yaron da muka haifa saboda sun ga babu yaro a tsakaninmu kuma basa son alaƙarmu ta yanke gashi Noor ya ɗaukesu a matsayin yan'uwan mahaifinsa. Bayan na gama wankan taƙaba na dawo gida. A duk lokacin da suka samu lokaci sukan kirani ko kuma su zo duba Noor, bayan na dawo sai Bilal ya maida Noor kamar abokinsa kullum zai zo gidanmu kiran Noor da wannan alaƙa mai ƙarfi ta shiga tsakaninmu muna girmama junanmu sosai ni da shi, sai dai iyayenaa basa son alaƙar da ke tsakaninmu ko ƙaɗan saboda sunan ganin ni bazarawa ce kuma da ɗan da ake zargin shege ne shi kuma saurayi mai mutunci, wannan dalilin yasa na ƙi bashi wata dama da zai nuna min soyayya. Har kuma tsawon lokacin Momy bata taɓa kirana ba, ni ma kuma ban kira ta ba, Ya Jamal ma sau ɗaya ya taɓa kirana be ƙara ba, Salima ce kawai muke yawan gaisawa akai akai ita kaɗai ta san na haifi Noor kuma na nemi ta min alƙwarin ba zata faɗawa kowa ba, duk da nasan sai ta faɗawa Momy amman Jibril be san yana da ɗa ba da ni ba. BACK TO STORY.... Tuna irin rayuwar da na yi aba ya hanani bachi har garin Allah ya waye. ‘Baka cancanci yafiya ba Jibril kuma hanyar da zan rama abunda ka yi min ita ce ta hanyar yin aiki tare da kai kamar yadda ka buƙata’ Shine abunda zuciyata take ta raya min ni kuma ina nanatawa kaina cewar ba zan taɓa yafe masa ba... YANZU LABARIN ZAI FARA...😄 *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy *Dedicated to My Asmee* 3⃣3⃣ MUSTAPHA POV. Bayan ya baro part ɗin Hajiya sai ya dawo ɗakinsa ya zauna saman kujera ransa a jagule ya dafe kansa yana sauke ajiyar zuciya. Shi kansa yasan Nawwara ba zata taɓa kula shi ba, yasan ba zata taɓa ƙaunarsa ba, gani yake ya cancanci ko wace irin jarrabawa amman ban da ta son Nawwara, yarinyar da ya wulaƙanta ƙanwarta sai kuma yanzu ya zo ya ce yana son ta. Miƙewa ya yi tsaye ya nufi gaban madubi ya tsaya yana kallon kansa, tunani yake abunda zai aikata wanda zai cire masa son Nawwara amman ko sunanta ya tuna sai gabansa ya faɗi. “Allah na san na aikata laifi mai girma Allah kaine mai yawan gafara mai tausayi Allah ya yafe min, Allah ka musanya min wannan jarabar ta son Nawwara zuwa wata Allah indai wannan ba ita ce ajalina ba” Shine abunda ya ke faɗa idonsa cike da ƙwalla. “Son...” Ya juyo da sauri jin motsin mahaifiyarsa, sai ya zauna gefen gado, ita ta ƙaraso kusa da shi ta zauna ta dafa shi “Son ka yi haƙuri da abunda Daddynka ya yi maka ka kwantar da hankalinka ka ji?” “Bana da kwamciyar hankali Mom tun daga lokacin da Allah ya jarrabe ni na zama silar mutuwar wata kuma Allah ya jarrabe ni da son macen da ba zata taɓa so na ba, kullum kuma ina tunanin abunda zai faru da ni gaba, ina jin kamar ajalina yake kusa da ni saboda wannan tunanin da rayuwar da na shiga ba zata taɓa bari na rayuwa mai tsowo ba” Ta yi saurin rumgume shi tana ƙoƙarin kuka. “No Son no ka daina zancen mutuwar nan, ka daina saka kanka damuwa akan abunda ba kai ka aikata ba, yarinyar nan ba kai ka akasheta ba su suka kashe ƴarsu so stop blaming yourself, Nawwara kuma ka cireta a ranka ba ta dace da kai ba, so kawai take ta yi amfani da wannan damar ta wulaƙanta ka” Be damu da hawayen da ke zuba a idonsa ba ya ce. “Mom Wallahi ba ni na sakawa kaina son yarinyar nan ba, ban san yadda aka yi son ta ya shiga raina ba duk wata hanya da zata cire min son ta nemanta na ke amman na kasa samu” “Zamu samu Son ka kwantar da hankalinka” Ya ɗago yana share hawayensa tare da ɗaga mata kai. “Bari Ikram ta kawo maka abinci ka karya anjima za mu yi magana” Nan ma kai ya gyaɗa mata, sai ta shafa masa kai cike da so da kuma ƙaunar ɗan ta. “Allah ya maka albarka” Ta tashi tayi ta fice, bayan kamar mintuna goma sai ga Ikram ɗauke da kwanonin abinci ta shigo ɗakin da sallama ta aje masa a gabansa. “Ba zan iya cin abincin nan ba Ikram” Ya faɗa yana kwantar da kansa saman gadon saboda zazzaɓin da yake jin ya fara taso masa. “Idan baka ci Mama zata damu” Cewar Ikram tana buɗe wasu plates, sauƙowa ya yi ƙasa ya zauna ya tsurawa Ikram ido kamar mai karantar abu a fuskarta. “Ikram zaki iya aurena...?” Ɗago kai ta yi da sauri ta kalleshi har ta buɗe baki zata yi magana sai kuma ta yi shiru ta ɗaga masa kai alamar Ee. “Amman miyasa Nawwara ba zata iya so na ba” “Ni da ita akwai banbanci, ni na rayuwa a cikin gidan nan ita kuma ta rayu a gidansu, kana da kyau da isar da kowace mace zata ce tana son ka, sai dai ita a halin yanzu ba soyayyace a gabanta ba, duk macen da aka yaudareta ko aka yaudari wani nata ita ma zata ga kamar wani zai yaudareta ne, babu yadda za ayi Nawwara ta kula balle ma har ya kai ga ta so ka, saboda abunda ka aikata ma ƙanwarta, kullum da wannan abun zata riƙa kallonka ko da kuwa wata mace ka yi ma balle kanwarta. Sannan akwai banbancin tarbiya a tsakanin kai da ita da kuma gata, kaga duk wannan abun da aka aikata iyayenka goyon bayanka suke suna ƙoƙarin nuna maka baka da laifi, i'm sorry to say idan har ka biyesu zasu iya rabaka da Ubangijinka duk da kuwa suna iyayenka, saboda suna kallo kana aikata zina kuma suka ƙyale saboda gudun ɓacin ranka, ƙara ma Momy wata rana tana maka magana amman baka ji, Allah ya ce kar mu kusanci zina balle har mu aikata ta, kai ko ya aikata adadin da baka san iyaka ba, kasancewar nan da muke ɗaki
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119