Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 3

Chapter 3

Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel 1,225 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

da tsohon rediyonsa. “Allah gamu gareka, ka iya mana” Cewar Inna tana sauke ajiyar zuciya. Ni kuma na miƙe tsaye ina faɗin “Bari naje na shirya na koma can na gani dan jiya sun ce min na dawo da safe” Baba ya ce. “Sun ce zaki samu aikin ne?” “Inshallah zan samu, saboda gurin Babansu naje kuma yana da mutuncin sosai” “Wai aikin me ne?” Inna ta tambaya tana daga kwance. “Sharar ti'ti ne kuma kullum ake biya” Ta yi saurin tashi zaune. “Wane irin sharar ti-ti kuma Nawwara? Wannan sam ba mutuncin ki ba ne, Wallahi zaginki za a fara daman sun saba” “Dukan masu zaginmu Inna babu wanda ya taɓa ɗauko Naira ɗari ya bamu ya ce mu siye wani abu, kuma na muku alƙawarin kare mutuncinna, Hijab zan saka idan har na samu aikin nan” “Ba irin wannan aikin ya dace da ke ba Nawwara, ni nafi kowa dacewa da na yi shi” “Baba ka san kana da Asma ba zai yiyu ka yi irin wannan aikin ba, kuma na maka alƙawari da zarar ka samu wani aikin zan daina wannan” Ya girgiza min. “Ba zaki yi ba Nawwara, sai dai ba zan hana ki bincikar wani aikin na daban ba, shi ma kuma kamin na samu wani abun yi” Na ɗaga masa kai cike da ladabi. “Tau Baba zan koma Candy Restaurant ko Allah zai sa a dace, amman Baba dan Allah ban da turin baron nan da ka taɓa yi kasan yadda zuciyarka yake idan ka ɗauki abu mai nauyi, ni Wallahi bana son kana dakon nan” Na faɗa kamar na yi kuka, dan har ga Allah nafi tsanar dako fiye da komai a duniyar nan. Baba yayi murmushi irin nasu na manya sannan ya ce “Nawwara kenan, ni dai ina jan hankalinki kan tsare mutuncinki da kuma na mu gaba ɗaya, Nawwara ke rai biyu ce mai maka da rai dubu a gurin mu, dukan abunda zai zubar da mutuncin ɗan ki da ni Mahaifinki karki kuskura aikata shi, ki riƙa tuna ke uwace, kuma ɗiyar wani wacce idan kika yi abun assha za a zagi Ubanki, ɗan ki kuma ayi masa jawabi, ni dai na san irin tarbiyar da na baku Wallahi ko cikin maza dubu zaki shiga matuƙar baki watsar da tarbiyar gidan nan ba, nasan zaki fito lafiya. Ni da kan ɗan ki rai biyu ne a gareki Nawwara, abu kaɗan kika aikata zai iya saka zuciyata ta buga, ɗan kuma zai tsanake ni ya riƙa nadamar da kika kasance uwarsa, saboda haka ki riƙe mutuncin ki, Allah ya muku albarka” Ni da Inna muka amsa da Amin. Haka yake min a duk lokacin da zan fita neman aiki ko wani abu makamancin wannan, waɗannan nasihohin suna tasiri a gareni matuƙa, sukan katangeni daga duk wani tayi da wasu suke min na siyar da mutuncina, ko kuma musanya mutuncina da takarɗun aiki. Comment on every single line. *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 3⃣ Bayan na baro ɗakin Inna na ɗibi ruwa a shiga ban ɗaki na yi wanka. Atamfata ta sallar bara na ɗauko na saka, akwai da son saka gyale duk da kasancewar Baba baya son haka, daman ba ko waɗanne uwane suke son ƴarsu ta saka gyale ba, sai dai nawa gyalen ba irin na barbarɗaɗɗin ƴan mata nan ne ba, me zai kai ni saka ƙaramin gyale bayan ina da ɗa kuma ba budurwa ba ce ni, duk da yake wani lokacin Jidda da Habiba har da mutanen waje kan faɗa min babu wanda zai kalleni ya ce ni bazawara ce har sai idan ni na faɗa, wani lokacin ko da na faɗa ba a yarda har sai idan waɗanda suka san ni ne. Ina da kyau jiki dai-dai gwargwado wannan yasa mutane basa yarda idan har na faɗa cewar ni Bazawara ce har da ɗa, wannan baya rasa nasaba da auren wuri da aka min, a lokacin da nake ganin kamar ban isa auren ba, auren da ya gurɓata min rayuwa ya canja ƙaddarata daga mai kyau zuwa mummuna. Atamfata miyan goro ce mai ratsin ja, hakan yasa na saka jan gyale saboda atamfar ta ƙara fita, talkamin Habiba na ɗauka na saka masu launin ja. Fes na fito sam baza kalleni kace ina da wata damuwa a wannan lokacin ba, idan ba ka birkice atamfata gaka ta roba bace sai ka ɗauka ni ƴar wani shegen mai kuɗi ce, ba laifi ni kaina ina sarawa kaina indai babin kwaliyana ne na iƴa fito kamar matar minister. “Inna zan tafi” Na faɗa ina tsaye daga jikin ƙofa, kai na jingine da ƙofar ina kallon Baba da ke unƙurin tashi. “Tau Allah ya kiyaye” Inna ta faɗa, Baba kuma sai ya ce “Ni ma bari na shiga kasuwa na ga abunda Allah zai yi” Salamar Maniru muka ji wato almajirin Hajiya Murja, maƙociyarmu masu babban gida, matar babban soja wacce bata taimako sai idan da dalili. Ni da Inna muka haɗa baki gurin amsa masa, Baban kan ya amsa masa da. “Bata nan taje makaranta” Domin yasan Jamila take nema, takan aiko kiranta a duk lokacin da wani aiki ya sha gabanta, domin kawai ta taya ta aikin sai ta sammata wani abu daga abincin rana ko dare da aka yi a gidan. Bayan Maniru ya fita Baba ya haɗe fuskarsa saboda mu ɗauki zancensa da muhimmanci, ya saba mana a duk lokacin da yake hanin mu kan aikata wani abu ko kuma ba mu umarni. “Bana son zuwan da Jamila take a gidan Manjo Faruku, kowa ya tsaya inda Allah ya aje shi” “Ni kaima bana son zuwanta a gidan domin yaron gidan nan ba shi da tarbiya, sannan yunwa babu abunda bata sawa musamman ga waɗannan da suke yara” Na faɗa cike da jin zafin tuna irin satar da ta taɓa ɗorawa Sakina a kwanakin baya. Inna dai bata ce komai ba bayan ajiyar zuciya da ta sauke. “Na tafi nidai ayi min addu'ah” “Tau Allah ya bada sa'a karki daɗe dai, kuma ki kula.da irin mutanen da zaki yi hulɗa da su” Cewar Inna ni kuma na amsa da tau na kama hanya ina addu'ar fita daga gida wato. _Bismillaahi, tawakkaltu 'alallaahi, wa laa hawla wa laa quwwata ‘ illaa billaah._ _بِسْمِ اللَّهِ تَوَكَّلْـتُ عَلَى اللَّهِ، وَلاَ حَوْلَ وَلاَ قُـوَّةَ إِلاَّ بِاللَّهِ_ Babu ko ƙwandala a hannuna ƙasa na kama hanya duk kuwa da kasancewar unguwar akwai ɗan nisa da ta mu. A bakin ti-ti na haɗu da Bilal wato abokina ko kuma na ce mutumen da muke mutunci da shi sosai har mutane suke raɗin-raɗin wai akwai soyayya a tsakanin mu. “Nawancy” “Bilal ya gida?” “Lafiya ƙalau Wallahi Ina zaki je haka?” Bana son faɗa masa ainahin inda zanje, ba kasafai nake son mutane su san ina zuwa aiki ba nafi son aji na samu aikin kawai, musamman Bilal da yake yawan nuna min baya son neman aikin da na ke. “Nan zan je gawon nama gidansu wata ƙawata Zinatu” Ya matso da mashin ɗinsa Honda “Hau na sauke ki” “A'a na gode” Na faɗa ba dan bana son hawan ba sai dai bana son yasan gurin da zanje. “Dan Allah ki hau mana, t-t ne balle ki ce kina jin kunya an mun fito

Table of Contents

Chapters

119 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});