Chapter 8
Chapter 8
jima ko gobe” Cewar Jidda. “A'a Jidda tun da har Allah yayi mana mafita ƙara muje mu kai musu kuɗin, baki san halin da bawan Allah ya ke ciki ba” Na kalli Inna zuciyarta cike da tausayinta da kuma tausayin kaina da na Jidda, na san tun safe bata ci komai ba ga rashin kwanciyar hankali da ke damunta. Hijabinta da ke gabanta ta ɗauka ta saka ta miƙe jikinta har rawa yake ta saka talkaminta ta kama hanya. Na kalli ƙawata Jidda tare da yi mata godiya. “Na gode sosai Jidda” “Ba komai, ki yi magana da ƴar'uwarki Nawwara ki kwantar mata da hankali karta sake shiga wani hali, ni zanje gida kar Abbah ya dawo” “Na gode sosai Jidda” Tashi ta yi ta fita, ni kuma na tashi nayi alwala na yi sallah, shiru-shiru Inna bata dawo ba har bayan Isha'i, sai dai hakan be sani tsoro ba a tunani ko zasu ɓullo da wani abun ne na daban. Takwas da rabi Inna ta dawo ita kadai cikin yanayin damuwa. Sai dai ban tambayeta komai ba har sai da ta yi alwalah ta rama sallah magariba ta yi isha'i bayan ta sallame na matso kusa da ita na ce “Inna ya kuka yi da su” “Lamarin ƴan sanda nan yana ba ni tsoro Nawwara, basu bar mun ganshi ba, amman sun karɓi kuɗin wai zasu zo anjima su kawo shi da kansu, ni ban taɓa jin inda aka yi haka” “Ko dai ba zasu bada belin nasa ba ne?” “Ni ya zan sani, an ce dpo gurin ƙanen wacce aka yi satar ne, kin san kuwa sai yadda Allah yayi” “Baba Sulaiman be ce komai ba?” “Babu irin roƙon da ba mu musu ba Nawwara, Har Salisu da Dahiru duk sunje, amman sun ce ba zasu ba da shi ba sai dai su kawo shi da dare, shine su suka wuce gida ni kuma na dawo” “To ko wasu kuɗin zasu ce a ƙara musu kuma?” “Ban sani ba” Ta faɗa tana fashewa da kuka. Iya ƙoƙarin da nayi na danne kukana sai na kasa saboda ganin hawayen mahaifiyata yana zuba. Shiru-shiru har goma na dare babu wani labari, daga ni har Habiba da Inna muna cikin tashin hankali da zullumi, dukanmu hankalin sai ya tattara ya koma gurin ƙofa ko iska ya kaɗa sai muga kamar Baba ne za a shigo da shi. Sha ɗaya da rabi na dare na tashi zan rufe gida, izuwa yanzu kan mun sadaƙar ba zasu kawo shi. Ina kaiwa bakin ƙofa sai na hango motar ƴan sanda ta faka a ƙofar gidanmu ahankali, ta yadda ba za a ji ƙarar motar ba, fitar motar ma a kashe take. Ban ƙara tabbatar da ƴan sanda bane har sai da naga sun fara fito daga cikin motar. Da gudu na juya na koma cikin gida dan faɗawa Inna. “Inna Inna ga su can sun zo” Ba Inna kawai ba, har Sakina da Jamila da ke bachi sai da suka farka duk muka ɗunguma muka fito waje da gudu. Sai dai abunda muka yi karo da shi ya faɗar da gabanmu dukanmu. Baba ne suka aje gefen icce sai wasu ƴan sanda uku kusa da shi ɗayansu ya ƙaraso kusa da mu yana mana bayanin da ban gane kansa ba. “Zuciyarsa ce ta buga, ku kai shi asibiti da safe” Yana faɗar hakan ya juya da sauri suka fice daga gidan. Mu kuma muka ƙarasa gurin da Baba yake kwance, hannu na kai na girgiza shi be motsa ba, na kira sunansa be amsa ba, na jijjiga amman be yi wata alama ta mai rai ba. Firgice na nasa hannu na yaga rigar yadin da ke jikinsa, sai ga ƙirjinsa da dukan jikinsa da jini, tashin hankali ya mantar da ni cewar dare ban san lokacin da na kwala ihu ba, na yi tsalle na dire na faɗi ƙasa na mulmula na mulmulo ina kuka, Habiba kuma ta faɗo kaina sumammiya. YAWAN COMMENTS YAWAN TYPING. 🙌 *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 7⃣ Cikin tashin hankali na kwantar da Habiba da ta faɗo kaina, na nufi Inna da ke baya-baya tana nuna Baba da yatsa. Ina riƙata sai ta cafki hannayena jikinta na karkarwa. “Gawa suka kawo mana Nawwara, sun kasheshi, miya musu? Basu yarda zamu biya kuɗin ba? Ko dan sun maida mu talakawa? Saboda ba mu da galihu? Akan ƴan kunnen zinari da wayoyi suka ɗauki rai? Miyasa za su kawo mana shi? Saboda muma mu taru mu mutu ko? Sun maida mu mahaukata...” Daga kalaman da take na fahimcin ƙoƙarin fita hayyacinta take. Riƙata na yi na zaunar, Sakina da Jamila da ke kuka na tura su ɗaki. Sai kuma na dawo tsakar gidan na yi tsaye ina kallon Baba, kana na kalli Habiba da ke sume, sai kuma Inna da ke zaune tana kallona, neman kukana na yi na rasa ashe akwai ranar da zaka buƙaci kukan ya ƙi zuwa maka, idona gaba ɗaya na ƙafe kamar hawaye be taɓa taruwa a ciki ba, yawun bakina na bushe kaina kuma yayi mugun nauyi kamar an ɗora min dala. Ban damu da rashin mayafi da babu a jikina ba da kuma takalmi na fita da gudu zuwa babban gida. Gudu na ke amman gani nake kamar ƙara maida ni baya ake, tsakaninmu da su babu nisa amman yau sai ya koma min kamar gari da gari. “Keeeeeeee” Na ji an kirani sai dai hakan be sani tsayawa ba, har sai da na ji an harba bindigar mahalba. A firgice na juyo ina ɗaga hannuna sama yayinda su kuma suka tunkaroni suna nuna ni da bindigar, ɗaya daga cikinta da dalla min fitila mai tsananin haske da kashe ido. “Nawwara miya fito da ke cikin daren nan?” Jin muryar Baban su ƙawata Ruƙaiya yasa na gane cewar ƴan sitirine masu yawo da zarar dare yayi domin kama ɓarayi. “Babanmu ne aka kawo shi ne zan je na faɗawa Baban Sulaiman, Babban gida zani” Na faɗa cikin wani irin mugun haƙƙi da sarƙewar murya. “Tah koma gida zanje na faɗa musu, Ibrahim rakata” Ya ƙarasa yana kallon ɗaya daga cikin yaransa. Wanda aka kira da Ibrahim ɗin ya saka ni gaba shi ya rakani har ƙofar gida sannan ya koma. Ko da na shiga na samu Inna zaune gaban Baba ta zuba masa bokiti biyu na ruwa sai fifita take masa da ɗankwalinta, atunaninta ko ya yi doguwar suma ne wata ƙila idan ta yi masa haka zai farko. Ƙarasa na yi ƙusa da ita na ɗauki ragowar ruwan da ke bokitin na juyewa Habiba sai gata ta farka a firgice tana haƙi kamar na fitar rai. A nan Inna ta juyo ta kalleni fuskarta a taɓe tana shirin fasa kuka. “Shi wannan ya mutu kenan?” Wani irin uhu Habiba ta saka iya ƙarfinta tana shurin ƙafafunta, tana danƙar ƙasar tana watsarwa. Ni kuma na yi zaune a gurin bana kuka kuma bana iya bawa ɗayansu haƙuri daga ita har Inna da ke kuka, ƙaɗan-ƙaɗan juri yake ɗibata ina jin sautin kukansu kamar a cikin bachi. Kan kace kwabo maƙota sun cika gidanmu kamar ba dare ba, masu taya Inna kuka na yi wasu kuma na girgiza kai, shigowar su Baban Sulaiman ne yasa kowa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119