Chapter 109
Chapter 109
bakinsa kumshe da sallama. Ina kallonsa nasan ba lafiya ba “Baba ina kwana?” “Lafiya kalau ina mahaifiyarki?” “Tana daki. Inna fito ga Baba” Na kwara mata kira bayan na bashi amsa. Sai ga Inna ta fito sanye da Hijabinta ta zauna bakin baranda tana gaisawa da shi. “Na ce masa ko akwai abunda ya shiga tsakanin Bilal da Nawwara ne?” Na tsayar da wankan da nake ma Noor na kalleshi gabana na faduwa. Sai Inna ta ce “Miya faru” “Ya aiko yanzu nan wai a bashi kayan aurensa ya fasa kuma wai ya yi magana da ita ya fada mata yace ta fada mana zai aiko ya karba” “Sulaiman ai gaka ga yarka waka a bakin mai ita ta fi dadi” Inna ta fada tana nuna masa ni. “Ke Nawwara ya aka yi?” “Jiya ne da yazo ya ce wai mahaifiyarsa ta ce bata yafe masa ya aureni ba, shine ya ce ya fasa aurena...” Na fada ina kokarin fashewa da kuka. “Daman Wallahi sai da muka raya a haka dukan mu sai da muka yi maganar nan, daman nasan irin rigingimun da suka faru ba zata bari ya aureki ba, Yakunbo ma sai da ta ce haka, amman matar nan ba ta yi tunani ba sam” “Ni kaina na zargi hakan ganin irin maganganun da suke ta fada gabana” “Ni kaina ina jin wasu abubuwan sai dai ka toshe kunnenka tun da ba a taruwa a zama daya, kuma a unguwar nan ma har a abunda ya kai unguwarmu babu abunda mutane basu fada ba, kuma kin san mutane da zuga Allah yasa haka shi ya fi alheri” “Amin, nima haka na ce kuma in mijinta ne babu wanda ya isa ya shiga tsakaninsu” “Tau Allah ya kyauta daman dai na ce sai na ji ta bakinta ne kamin mu bada kayan, Allah ya baki wani” Ya fada ganin irin hawayen da nake, sannan ya mike tsaye ya fice cike da damuwa, daman kayan ba a nan suke ba, tun da aka kawo lefen aka maida shi can gurin Yakunbo kasancewar nan gidan ba Namijj kuma ina tsoron kar a biyo dare a tararda mu. A gaskiya na ji babu dadi na ji ni a cikin wani kalar yanayi mai kamar an yi min mutuwa, ban tabbatar da cewar Ina son Bilal sai a wannan lokacin, yanzu shikenan an raba mu kenan? A wunin ranar kasa sukuni na yi a cikin gidan mu, ana kiran la'asar na dauki Hijabi na nufi gidansu Jidda. Ina shiga na fashe musu da kuka daga ita har Maman Nura wato mahaifiyarta sai da hakalinsu ya tashi, sun tausaya min kuma sun nuna min rashin jidadinsu a fili lokacin da na labarta musu abunda ya faru. “Yanzu duk soyayyar nan da kuka yi da Bilal ace be aureki ba gaskiya abun be yi dadi ba” Cewar Jidda, sai Mahaifiyarta ta ce. “Ni daman Wallahi ban dai fada ba ne, amman na san ba duka iyayene zasu iya bari dansu ya auri bazarawa ba, ko mai aure daya balle mai biyu kuma har da da, yanxu kuma ga abunda ya faru” “Amman ni Wallahi da zaki min wani abu da kin auri Jibril ko dan mahaifiyarsa ta ji haushi, kuma ga Noor sannan mutumen yana son ki sosai, kin ga sai ma ya maiye gurbin kwanakin da suka rage a daura miki aure da shi” Jidda ta fada, sai mahaifiyarta ta karba nata. “Ni dai haka na gani, wani lokacin abunda kake so ba lallai ne ya zama alheri a gareka ba, kuma so da yawa kana kin abu ya zama shine alheri a gareka, ki baiwa Allah zabi kawai” Wani irin abu na ji ya daki zuciyata, sam bana jin zan iya kara zaman aure da Jibril, indai har ban aure Bilal ba to be cancan na auri Jibril ba, taya ma zan yi zaman aure da mutumen da ya wulakanta ni ya nuna min ba ni muhimmanci a rayuwarsa. “Na baiwa Allah zabi kuma na san zai zaba min abunda duk yafi zama alheri a gareni, amman ina jin kamar ba zan iya zaman aure da Jibril ba” Jidda ta dafani. “Zaki iya Nawwara, tunda kina son Noor kuma kina son farincikin danki, karki damu da rashin son da kike masa, abu mai muhimmanci shi yana sonki kuma so mai tsanani, kuma kinsan hausawa na cewa mai son ka be ganin ramarka, kuma kara ka auri wanda sonshi ya fi na ka yawa zaka fi jindadin zaman aure fiye da wanda ke kika fi sonshi, zan cigaba da miki addu'a kamar yadda na ke yi ma kaina Insha-Allah” Hawayena na share na gyara zamana, ita kuma ta tashi ta fita saboda kiranta da aka yi a waya. Sai kusan magariba na baron gidan na dawo gida. Bayan na yi sallama magariba na zauna ina ta karanta lahaula wala'kuwwati da carbi adadin da zan iya, saboda tana yaye damuwa kuma matukar kana cikin damuwa ka lizinci karanta ta Allah zai maka mafita. Can kusan sallah isha'i na kira wayar Bilal sai suka nuna userbusy haka na yi ta trying suna amman na kasa samu daga karshe na gane ya saka number ta a blacklist ne. Wasa wasa aka kwana uku a haka na kasa cin abincin kirki saboda tunani, ba damuwa ce ta dame ni ba damuwar Bilal ce ta dame ni domin na san yana so na, kuma mutane da yawa zasu masa dariya idan har be aureni ba, duk na bi na rame kamar marar lafiya, jikina babu wani kuzarin kirki kasancewar bana iya cin abinci mai nauyi sai fura ko koko ko tea. Ranar da aka kwana hudu da faruwar hakan ina zaune, da misalin biyar da rabi na yamma sai ga Asiya yar wajen Baba Sulaiman ta zo kiran wai na zo Baba Sulaiman da Baba Dahiru suna kirana, gabana ya fadi da farko kuma naji tsoro sai dai ance karka ji tsoron kira ka ji tsoron laifi da ka yi, kuma ina tunanin addu'a ta ce Allah ya amsa wata kila iyayen Bilal ne suka dawo a gyara maganar. Sai da na fadawa Inna sannan na dauki Hijabi na saka muka fita tare. Muna shiga zauren gidan gabana ya fadi ganin Baba Sulaman da Baba Dahiru da kuma Baba Audi wato kanen mahaifina da yayyensa a zaune saman tabarma tare da Mahaifin Jibril da abokinsa wanda suka zo tare lokacin da wadancan abubuwan suka faru da kuma Yayan Jibril da wasu mutane maza da ban wayancin fuskarsu ba a zazzaune. Sallama na fara yi bayan sun amsa gaishesu sai Baba Sulaiman ya nuna inda zan zauna, ba musu na zauna kaina a kasa gabana sai faduwa yake ina jiran jin dalilin kiran. “Jibril ne ya aiko da iyayensa su nema mishi aurenki kuma ya ce kun yi magana da shi akan cewar zai aiko kin amince, amman mu baki fada mana ba, hakan yasa na ce ba za a yanke hukunci ba sai an kiraki an ji ta bakinki” Na yi shiru ban ce komai ba, still kaina a kasa zuciyarta cike da tsanar Jibril. Sai Baba Audi ya katsa min tsawa. “Ki bude baki ki yi magana mana, dukan mu ba yara balle ki tsaya yi mana wasa,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119