Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 62

Chapter 62

Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Mustapha, yafiyar Ubangiji ta fi cancanta ka nema ba tawa ba” Sai ya kirana sunana a hankali. “Nawwara idan na kai kaina kotu aka min hukunci zaki tafe min?” “Allah ya rufa maka asiri karka tonawa kanka” “Ina ma ace zan iya raba zuciyata biyu ki karanta ki ga abunda yake raina” “Kasan zaka nemi yafiya ka aikata?” “Ƙaddarata ce ta zo a haka, an rubutoni a cikin ƙaddarar Habiba kamar yadda aka rubutoki a cikin ƙaddararta, Wallahi da nasan Allah zai jarrabe ni da sonki da ban yarda ba kalli Habiba balle har wani abu ya shiga tsakanina da ita” Ya faɗa yana ƙwalla, har na buɗe baki na sake masa wata maganar sai na hango Bilal tafe, sai na tattarahankalina na maida gurinsa gudun kar ya zargi wani abu, hakan yasa Mustapha waigaya ya kalleshi. Tsayawa Bilal ya yi cak sai kawai ya ɗago min hannu daga can inda yake ya juya ya koma. “Ka gani ko? Ka hana masoyi ya ƙaraso kusa da ni” Na faɗa a tsawace. “Yi haƙuri” Sai ya yi saurin juyawa ya bar gurin cikin sauri, na daɗe tsaye bakin ƙofar wai ko zan hango Bilal ya dawo amman har na gaji ban dawo ba hakan yasa na juya na koma cikin gida raina a jagule. Assalamu alaikum habibaties. Ina nan lfy kalau sai dai phone dina ce ta ci screen amman yanzu an gyara, Alhamdulillah. A cigaba da gashi... *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy *Dedicated to My Asmee* 3⃣8⃣ MUSTAPHA POV. Be taɓa tattabar da cewa yana son Nawwara ba sai yanzu, wani irin abun yake jin yana dibarsa masar misaltuwa, kalamar da ta furta ga waninsa na masoyin da ta kira Bilal yake jin kamar ace shi ne. Kai tsaye ya wuce part ɗinsa sai ya kwanta rairai ƙasan carpet ya lumshe idonsa, babu abunda yake tunani sai halin rayuwar da ya jefa kansa, da ace be kasance mazina ci ba da babu abunda zai hana Nawwara ta so shi, tunani yake abunda zai faɗawa Allah idan har ya mutu a yau ba tare da ya tuba, son nawwara yasan jarabawace Allah ya ɗoro masa gashi tana da ɗawainiya da shi ta hanashi sukuniina ga ya mutu? Tabbas zai yi ƙoƙarin juye rashin Nawwara amman azabar Allah fa zai iya jureta? Wacan azabar da za'ayi ma mazinata ba da irin wannan jarabawar ba ce da wuta mai kamar kunu za a ƙona fatarsa bayan azabar da za a gada masa cikin ƙabari. Buɗe ido ya yi sai ya ɗaga hannunsa sama yana kallon farar fatar hannunsa, sai ga hawaye sun gangaro daga idanuwa zuwa gefen kuncinsa, unƙurawa ya yi da zimmar tashi zuwa alwala ya yi sallah ya ƙara nemi yafiyar Ubangijinsa, sai dai hango Mahaifiyarsa da yayi jikin ƙofa tana kallonsa tana hawaye yasa shi yin zaune tana share nasa hawayen. Ƙarasowa ta yi kusa da shi ta zauna kana ta riƙa hannunsa tana kallon fuskar ɗanta cike da tausayinsa. “Son kuka kake yi?” Ya yi shiru be ce komai ba. “Zan je na nema maka yafiyarta, in har hakan zai faranta maka rai, damuwarka damuwata ce a duniyar nan bana da wani farinciki sai naka, amman ina son ka sani ba kai ne ka kashe yarinyar nan ba” “Ba ni na kasheta ba Mom na sani, amman ina jin rashin kyautawa a abunda na aikata, sannan Allah ya jarabeni da abunda ban taɓa tsamani ba, son yayarta, kuma kun kasa fahimtar hakan balle ku goya min baya” “Na yi magana da mahaifinka zamu nema maka yafiyar Nawwara, da kuma aurenta matuƙar hakan zai kwantar maka da hankali” Ya yi saurin kallonta kamar be yarda ba. “Mom da gaske?” “Kai kaɗai na ke da a duniyar idan ban faranta maka ba wa zan farantawa? Bana son na rasa ka” Ya kwantar da kansa jikinta yana murmushi tare da sauke ajiyar zuciya. “Thank you so much Mom i love you” “Love you more” Ta faɗa tana hawaye, har ga Allah ba dan tana son nawwara zata nema masa ita ba sai dan kawai ɗanta ya samu salama hankalinsa ya kwanta, amman ita har gobe gani take ɗanta be dace da nata kamar Nawwara ba. Sun daɗe a haka sannan ta sake shi ta fita shi kuma ya shiga banɗaku dake falon ya wanke fuskarsa ya canja Jalabiyar da ke jikinsa ya zuwa wata jalabiyar black sannan ya fito a compound ya nufi gurin da motarsa take ya shiga horn ɗaya mai gadin ya buɗe masa gate ya ɗauki hanyar gidansu Jidda. Tun kamin ya ƙarasa ya kirata ya faɗa mata ta fito gashi ƙofar gida, sam ba zaka ganshi a yanzu ka ce mutumen ɗazu ne ba, farinciki ya mamaye masa zuciya ji yake kamar da Momy taje ta bawa Nawwara haƙuri haƙura zata yi ta kulashi. Yana zaune cikin motar har Jidda ta fito sanye da Hijab tana tafiya kamar marar laƙƙa, jinginawa ta yi jikin motar yana miƙa masa gaisuwa shi kuma sai ya kashe motar ya fito yana murmushi. Gabanta ya faɗi zuciyarta ta fara bata wani tunani na daban kar dai ya cutar da ƙawarta, mutumen da tasan yana cikin damuwa yanzu kuma har da murmushi a fuskarsa. “Naje na yi magana da Nawwara amman har yanzu bata fahinta ba, har na faɗa mata maganar da be kamata ba, amman na san nan gaba zata gane kuma zata yafe maka ni dai abunda na ke fata karka cutar da ita dan Allah” Ya sake yin murmushi yana kallonta fuskarsa da annuri. “Zan iya cutar da kaina ban cutar da Nawwara ba, da kin san yadda na ke sonta da baki min wannan zargin ba, amman na san duk mutumen da yasan wanene dole zai zargeni, faruncikin da kika gani a fuskata na zo ne na faɗa min cewar Mom ta yarda har ma ta ce zata taimaka min wajen neman yafiyar Nawwara” “Wow amman na yi farinciki, Allah ya shiga cikin lamarin kuma ya sa ta kula ka” “Amin nima fatana nan” Ya faɗa yana kallon hawayen da suka zubo mata, wanda hakan yasa shi wani tunanin na daban. “Hawaye kike?” “Ni?” Ta yi saurin kai hannu ta share hawayen, da alama bata san sun zubo mata ba. “Kawai ina farinciki ne” Ya mata murmushi as respond ba dan ya gamsu hawayen nata na farinciki bane, ita kanta bata san hawayen mi take ba, iya abunda ta sani zuciyarta na yaudararta ne da son cuta mata abunda ta san ba zai taɓa yayuwa ba. ‘i'm very stupid taya zan so mutunen da ke son ƙawata?’ A fili kuma sai ta kalli Mustapha ta ce “Zan shiga ciki” Nan ma kai ya ɗaga mata yana murmushi da iya fatar baki kawai ya tsaya masa. Har ta juya sai ya kirata. “Jidda...” Ta juyo tana kallonsa “Thank you” “Anything for Nawwara” Sai da ta shiga gida sannan ya juya ya shiga motarsa zuciyarsa na raya masa wani abu da baya son kawowa akansa, he's happy at first amman yanzu sai ya nemi farincikin ya rasa tunanin hawayen da Jidda take ya tsaya masa a rai. Ko da ya isa gida part ɗin Mom ya fara shiga sai dai be sameta ba saboda bata gidan, Ikram ce kawai a falon tana

Table of Contents

Chapters

119 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});