Chapter 47
Chapter 47
ba zaka taimaki rayuwata ka faɗawa mahaifinka cewar baka so na ba” Still bakinsa a mere ya miƙe tsaye yana zuba hannayensa a aljihu ya nufi window. “Ban san ko sau nawa zan faɗa masa ya yarda ba, Wallahi na faɗa na ƙara duk wata mace da ba Aisha ba bana son ta, amman mahaifina ya tsaya kai da fata akan sai na auro wata, ya neman min auren ƴar Alhaji Dahiru ne saboda yana yaba tarbiyar gidan kuma yana son zumuncinsu ya ƙara ƙulluwa, after that you're not his biological daughter, jin wannan yasa Mahaifina ya ɗaga min ƙafa, amman Alhaji Dahiru ya dage akan shi yana son ayi, har da cewar wai baya son auren ya ɗauki lokaci. Aurena da ke baiwar Allah ba alheri ba ne, domin ni dai har ga Allah bana son ki, lemme ask you some questions, shin zaki iya auren namijin da ya taɓa kusantar wata mace kamin ke? Zaki auren Namijin da ya taɓa sanin wata mace kamin ke? Zaki iya zama da namijin da zuciyarsa da gangar jikinsa duk na wata macen ne? Could you?” Na girgiza masa kai. “No i couldn't, ba zan iya auren namijin da ba be san ƙimar zaɓin iyayenshi ba” Ya matso kusa da ni cikin ɓacin rai, ya riƙa fuskata ya soma magana cikin murya mai amsa amo biyu. “how dare you, ke iyayenki sun san ƙimarki ne zasu barki hannun wani saboda ƙwadayin abun duniya, bayan baku haɗa komai da shi ba daga gadi! Wallahi duk kika aure kin saka rayuwarki cikin matsala sai kin ƙwammace kiɗa da karatu, duk wanda ya ce zai raba ni da Aisha ba zai sha da daɗi ba” Ya ciro wayarsa da ɗayan hannunsa ya nuna min hotonta da ke gaban wayarsa, yana matsar min fuska iya ƙarfinsa, a nan na fara kokuwar kuɓucewa amman na kasa. “Wannan matar ta fiye min ke sau dubu ɗari, dan haka karki yaudari zuciyarki kar kwaɗayin abun duniya yasa ki salwantar da rayuwarki ni da ke kamar RAI BIYU ne wuta da ruwa ba zamu taɓa haɗuwa ba, you bitch...!” Yana kaiwa nan ya wulgar da ni saman manyan cushion, ya yi ficewarsa cikin zafin rai. Ni kuma na tashi zaune da sauri ina taɓa bakina da nake tunanin yama fara jini saboda zogin da yake min. Na kusan minti goma a falon sannan na fito ina ta ƙoƙarin ɓoye abunda ke fuskata. Ban tararda Salima a falon ba, sai Hajiya Zainab da yaranta ƴan mata da ke ta min kallon uku saura kwata. “Direba zai maida ke gida, Salima ta koma tuni saboda an kira Daddy ku ba lafiya” Gabana ya faɗi sosai, miya samu Daddy ina ta tambayar kaina har na fito harabar gidan na nufi inda direba yake, na shiga bayan motar sai ga wata budurwa ta zo da jakunkuna ta saka min a motar sannan direba ya kama hanyar gida da ni, tun kamin mu isa gida na fara hawaye saboda tunanin abunda ya sami Daddy da kuma baƙin cikin abunda Jibril ya yi min. **RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 3⃣0⃣ Ganin Motar Anty Mairo da Zubaida wato manyan ƴaƴansa guda biyu a harabar gidan ya ƙara tayar min hankali, cike da fargabar abunda ya samu Daddy na fita motar na nufi cikin gidan. A falon Momy babu kowa sai ƴar aikinta Suwaiba, ban tsaya komai ba na nufi part ɗin Daddy. Mamaki ne ya maye gurbin tashin hankalina, sai ya zo akasin tunanina da kuma furuncin step mother ɗin Jibril cewar Daddy ba shi da lafiya. A sanyaye na shigo falon idona kan Daddy dake making call yana murmushi, ban ankaro da ban yi sallama ba sai da Anty Zubaida ta hankarar da ni ta hanyar amsa min da. “Wa'alaikissalam” Saurin share hawayen fuskata na yi na yi sallamar duk da kasancewar na kai tsakiyar falon. Sai duk suka haɗa baki gurin amsa min ciki har da Momy. Cike da mamaki na zauna kusa da Anty Zubaida ina cigaba da kallon Daddy. “Nawwara har kin dawo?” Cewar Momy. “Eh ko da na fito Salima ta dawo gida ko da na fito Hajiya tace min Salima ta wuce wai Daddy ba lafiya” “Ee na kirata na ce ta dawo gida jikin Daddynta ya tashi amman da sauƙi daman jinin ne ya hau amman ya sauka” Ajiyar zuciya na sauke na kalli Daddy da ya aje waya a kunnensa ina masa ya jikin. “Alhamdulillah, ya kika baro can ina fatar kina son shi?” Har na buɗe baki na yi magana sai Momy ta yi karaf ta karɓe. “Kana maganar tana son shi Alhaji wace mace ce zata kalli Jibril ta ce bata son shi, ai Hajiya ta kirani ta faɗa min sun fahimcin junansu sosai kuma shima ya yaba da ita sosai” Ƙasa na yi da kaina saboda bana son ƙaryatata ko kuma na kunyata ta a gaban ƴaƴanta akan wannan zancen da ba haka yake ba. “Maa Sha Allah, haka muke so Allah ya tabbatar da alheri a ciki, mahaufinsa ma ya faɗa min yana son a ɗaura masu aure kamin ta koma makaranta albashi idan ta kammala sai ayi bikinsu” Jin wannan maganar ta Daddy yasa idanuwa cika da ƙwalla. Anty Zubaida da Anty Mairo suka shiga tsokanata har ma da Salima, ban san lokacin da na fashe da kuka ba na tashi da gudu na bar falon. Ɗakinmu ma dawo na zauna bakin gado ina ta kuka, wata zuciyar na raya min na kira Baba na faɗa masa wata na cewa a'a, tabbas a lokacin ina son Jibril amman rashin aurensa shi zai fi min alheri tun da har ya nuna min akwai wacce yake so. Ina ta tunanin mafita sai ga Momy ta shigo ɗakin tare da Salima tana faɗin. “Kun saka min ƴa kuka bari na rarrashi abata” Tana zaunawa kusa da ni sai ta kore Salima daga ɗakin da sunan zata rarrasheni, Salima na fita sai ta canja fuska ta kalleni “Iyakar halacci Nawwara mun miki ke da iyayenki, ashe ko ba mu cancanci komai ba sai kyakkawan sakamako, kin dai san Alhaji ba zai miki zaɓin da zai cutar da ke ba, kuma wannan auren da kike gani idan har kika aureshi ke da danginku duk kun warke, ƙin yi wannan auren zai ɓata abotar Daddynku da shi na tsawon shekaru ashirin, idan kuma kika yarda kika aureshi tam kamar kin zuba babban jari ne a dukiyar gidan nan da kuma ta gidanku, domin mahaiɗinsa na cikin masu kuɗin da ake ƙirgawa da su a africa ba ma Nigeria kaɗai ba” Na ɗaga kai na kalleta cikin muryar kuka na ce “Amman Momy baya so na yana da wacce yake so, kuma ya faɗa min matuƙar na yarda na aureshi sai na yi nadama” “Ai nasan baya son ki, daman taya za'ayi Namiji kamar Jibril ya so mace irin ki? Yaron da yake ganin ƴaƴan turawa da larabawa, kuma ɗan da magana kawai zai yi ma kuɗi su faɗo ƙasa sai kalli ƴar talaka irinki ya ce yana sonta? Ke ni fa Salima na so a bashi amman Alhaji yaƙi wai wani ya riga ya bada ita ba zai ce ya fasa ba saboda wannan, amman idan kika yi haƙuri da sannu
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119