Chapter 69
Chapter 69
kofa na tsaya na cire tufafina sannan na saka wasu su kuma na rabasu gefen kofa har ruwan ya dauke. Wayana ma ruwa ya shiga ciki ya taba shi sai dai na yi sa'a be yi komai ba. Saman kujera na zauna sai Noor yanzo kusa da ni ya zauna ya jingina kansa da jikina. “Momy ki ara min wayarki na yi game” “A'a kai baka da aiki sai game” “Momy dan Allah” Ya fada kamar zai yi kuka, ni kuma na hana shi domin wayar babu carji sosai a ciki, sosai na maida hankalina kan Sakina da ke ta rihazar din sira da zasu yi gasa a kai, Inna kuma ta dauko kur'ane tana karatu. “Inna ki min addu'ah Allah ya sa na yi ta daya” Cewar Sakina ganin Inna tana addu'a bayan ta gama karatun kur'anen. “Yaushe ne ma?” “Gobe kuma?” “Eh daman kwana biyu aka bamu ai” “Allah ya bada sa'a” Na fada tare da tashi na fita waje dan yi alwalar la'asar. Bayan na gama sallah ne Inna take tambaya ya aikin na amsa mata da Al-hamdilillah, sannan na dauki wayata na kira Bilal sai ta saka min user busy, haka na yi ta har biyar na yamma ta yi amman bata shiga ba, hakan yasa na fahimce cewar na saka numberta a blacklist ne, amman mi na masa har haka ne? Ko dai yana fushi da ni ne? Sallama muka ji da bakuwar murya, duk kokarin da na yi na rike Noor sai ya ci tura domin tuni ya kai bakin kofa shi da Jamila daman rigangan suke gurin amsa sallama ko leke aga wanene. “Nawwara na nan?” Na ji kamar muryar da na sani, hakan yasa na yi wuf na fita waje, Rabi ce tsanye da gown ta dora rigar sanyi sama fuskantar dauke da murmushi kamar kullum, sai dai ba ni take kallo ba Noor take kallo cike da burgewa, hakan yasa na maida shi bayana sai ta kalleni tana cigaba da fadada murmushinta, kamin ya matsa jikin kofar gidanmu ta ce “Bismillah” Sai ga wasu maza su biyu suna ta shigowa da kayan abinci da kuma manyan akwatuna guda uku suka dora saman barandar dakin Inna. Ni dai kallo na bisu da su har suka gama ganin ta juya zata fita yasa na ce “Waya ce a akawo?” “Ke ma ai kin sani” “Dan Allah ki koma da kayan nan” “Ni ba zan iya ba, amman zaki maidawa da kanki” Inna da ke tsaye bayana ta ce “Malama jeki abinki mun gode kinji” “Nima na gode Mama, Handsome boy sai anjima ko” Noor ya daga mata hannu yana murmushi da ya fitar da dimples dinsa. “Okay Anti mun gode” Ji na yi kamar na buge masa baki. Bayan ta fice Inna ta kalleni ta ce. “Ba a maka alheri ka maida ko ya yake Nawwara, idan ma har kina jin ba zaki iya amfani da abunda ya baki ba, zaki iya kyautarwa, kuma idan har kika cigaba da nuna baki son abun hannunsa ba zaki karba hakan yana nufi har yanzu kina sonsa, amman idan har kika karba kika manta da komai kika nuna masa ba komai hakan zai kidimar da shi, domin zai gane cewa yanzu kina mu'ala ne da shi kawai ba ta so ba” “Amman ai kamar ina son sa ne idan na karba” “Ba daga nan take ba” Sakina taje ta bude akwatin tana duba babu komai a ciki sai tufafi da abaya da kuma gowns, sai atamfa da lace wadanda ba a dinka ba, “Amman gaskiya ba za a maida wannan kayan ba, ai ba mu muka ce ya kawo ba, mun ci banza” Cewar Sakina tana gwada wasu tufafin a jikinta. “Wallahi Anty ko ba zaki aureshi ba ki tatsi banza ko zafi ki rage” Ni dai ban kulata ba balle banzan zancenta, haka na zauna cikin rashin dadin rai har dare saboda Bilal be kira ni kuma na tura masa sako be maido min da amsa ba. Bayan sallah isha'i dpo ya zo gidanmu, ya yi wasu tambayoyi ni da Inna sannan na fada mana ya shigar da kara kotu kuma karshen watan nan ne za a fara zaman kotu, hakan ya faranta min rai sai na dan sake zuciyata ta washe. Washe gari ba mu karya da abunda muka saba karyawa ba, saboda Indomie da aka kawo mana ita Sakina ta dafa suka ci ita da Jamila da Noor shi kan har tsalle yake yana direwa kasa yana jindadi sun ci indomie. Inna kan kunu ta sha as usual nima shi na sha dan bana son ko warin indomie na ji balle kuma na kalleta har ya kai ni ga ci. Bayan sun wuce makaranta, ni kuma na soma gyara gidan, sai da na gama sannan naje na samo mai ruwa ya zuba mana jalka shida Inna ta bashi dari da hansi, sai na zuba na shiga wanka. Ina cikin bandaki na ji sallamar Baba Sulaiman da Baba Dahiru, wato kanen mahaifina da kuma yayansa, sai dai ga dukam alamu ba su kadai suke ba, domin Hayaniya ta yi yawa, ko da na fito Inna ta shimfida musu tabarma suna zaune ciki har da abokin Baba wanda ya sama masa aiki a Abuja da kuma Alhaji Bashir Makama wato mahaifin Jibril da wani dattijo tare da su. Na ji dadin da Allah yasa na shiga wankan da Hijabi da fitowa ta yi min wuya, karasa na yi na durkusa har kasa na gaishesu, sannan na wuce dakinmu zuciyata cike da maganganu kala kala. Ina cikin saka tufafi Inna ta kira hakan yasa na yi hanzarin saka kayan na saka wani Hijabin na fito na zauna kusa da ita. “Nawwara kin gane ni” Na dago na kalli Alhaji Bashir da ya yi maganar sannan na daga masa kai. “Zuwa na yi na baki hakuri akan abunda muka miki, hakika bamu kyauta ba, na sani amman dan Allah dan darajar iyayenki ki yafe mana, Wallahi har ga Allah Jibril ya canja kuma ya yi nadama, be san na zo nan ba ba shi ya turo ni ba, kuma bana son ya san na zo, na yi niyar yin haka tuntuni amman kunya da nauyinki yasa na kasa yi, yanzu ma sai da na biyo ta bangare Babanninki suka karfafa min guiwa sannan na samu na karaso ki dubi girman Allah ke da mahaifiyarki ku yi hakuri da abunda muka muku” “Ba fa kai ka yi ba” Cewar Baba Dahiru, sai ya amsa da “Ai da na ya yi kamar ni na yi kenan” Ni dai bance komai ba banda hawaye babu abunda na ke, Inna ce kawai take amsa masa, shi ma sai da su Baba Sulaiman suka saka baki, daga karshe ya yi magana agaisuwar rashin Baba, sai kuma ya tambaya yi Noor. “Sun tafi makaranta” “Amman Jibril be san yana da ba ko?” Kai na daga masa, sai ya soma labarta mana yadda Jibril yake son da da kuma irin halin rayuwar da ya shiga bayan rabuwarmu. Ya dauki kudi mai yawa ya bawa Baba Sulaiman da Baba Dahiru, sannan ya miko mana bandir din yan dubu daya. Sannan ya yi mana sallama yana cewa yau ya zo kuma yanzu zai koma daman saboda
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119