Chapter 116
Chapter 116
wahalar samu. A yanzu ya zama mutum kawar kowa ciwon da yake jin kamar ba zai barshi ba, gashi yanzu ya samu sauki tun bayan jinyar da yayi a india, he can now read Quran daga fatiha har bakaqa and Nawwarar tana tare da shi da Noor what else zai roka bayan godiya ga Ubangijinsa? A masallacin da ke unguwarsu Sama road ya yi sallah la'asar sannan ya shigo cikin gida, a hankali ya yi parking dan baya son ta ji tsayawar motarsa. Yasan by this time Noor yana makarantar islamiya dan haka Gimbiyarsa ce kawai a gidan, yana fitowa daga motar ya leka window kitchen hangota da yayi tsaye gaban fanfan yasa shi jindadi sai ya dawo kofar shiga falon ya tura kofar a hankali ya shiga, amman hakan be sa ya tsira ba, sai saukar ruwa ya ji a jikinsa. “Haba Madam miyasa baki min adalci babu ne?” “Adalcin kenan kai waya ce ka jikani” “Amman dai dazu da kayan bachi a jikinki na jikaki, ni kuma shadda ce kuma gurin zan ce zan je fa” “Fade kawai kake amman babu wata mace da zata kulaka” “Inji wa? Kin ga yadda ake rushing din na kuwa kai ni fa handsome guy ne irin na bugawa a jarida ma” Ta ji haushi har da zuba masa ragowar ruwan gorar a jiki. “A haka din duk ka wani tsufa ai ni kadai zan iya da kai” “Ko yanxu ina driving wata har kashe min ido daya take” “Karuwa ce” “Wane irin karuwa kuma? Kin ganta kuwa kyakkyawa ga dogon hanci ga karamin baki gata fara kuma ga katon ciki haihuwa yau ko gobe sai shegen matsifa ta fitini kowa ta hana kowa sakewa” Ta jefa masa gorar ruwan tana ƙaƙarin kuka ita ala dole ta yi fushi da gaske, yayi saurin kai hannu ya rika ya juyo da da ita sai ya risina ya kara kunnensa dai dai cinin cikinta. “Yi hakuri Babe na fada min ya Baby yake?” “Ban sani ba” Ta fada tana kokarin ture kansa daga cikinta. “Ni dai Allah yasa karki haifo min fitininayar yarinya, Wallahi Nawwara kin cika masifa” “Au haka ma zaka ce” Ya yi saurin rufe bakinsa ya mike tsaye. “Mantawa na yi” Ya jata ya zauna saman kujera sannan ya zaunar da ita saman cinyarsa. “Fada min miye na wannan fushi? ” Ta kara turo baki. “Baka siyo min komai ba” “Daga gurin budurwata na ke kin san kuma...” Be gama ba ta ja masa kunne har sai da yayi yar kara. “Wace budurwa kuma ba zaka daina jana ba?” “Wallahi ba wasa na ke miki ba, akwai wace ta dauki min hankali sosai, bana son jin muryar kowa sai nata bana son ganin kowa sai ita sunan kawai idan na ji raina fari yake” “Nawwara ce” Ya fada da fuskar zolaya sai ya maida ita kirjinsa ya rumgume suna dariya. Hannunsa ya kai ya shafa cikin ya lumshe ido. “Ban tsammaci zan kara samu wani dan ba bayan Noor but look at us right now” Murya kasa kasa yake mata maganar kamar mai rada, har kasan ruhinsa yake jin son Nawwara da duk wani abu da ya dangance ta, more especially ma cikinsa da take dauke da shi a yanzu bayan ya cire rai daga haihuwa tun bayan a abunda ya faru da shi amman gashi yau Nawwararsa tana dauke da cikinsa. A yanzu ba shi da wani buri da tunani sai na Nawwara, ko da wasa baya son abunda zai bata mata rai, idana yana zaune tare da ita a gida har baya son fita ita kuma ya yi nisa da ita suna makkale a waya, tunaninta ta dinga addabarsa kenan kamar yadda ita tuaninsa yake hanata sukuni, lokatu da dama idan zai anbaci sunan wata sai ya kira Nawwara shi da kansa wani lokacin yana mamakin kansa, a lokacin da ya fahimce cewar tana da ciki sai ya kasa sukuni kuma ya kasa zaune ya kasa tsaye saboda murna da jindadi. Yau ma kamar kullum Jibril be sake fita ba tun da ya dawo, tare suka karasa girkinsu na dare, around six direba ya dauka Noor daga islamiya, da gudu ya shigo yana sallama tare da fadin. “Daddyna ya dawo” Yana shigowa Jibril ya safkeshi ya yi sama da shi. “Oyoyo dan daddynsa” Dauke da shi ya shiga bedroom dinsa wato dakin Noor dakin da aka kawata da kayan wasan yara da duk wani abu na jindadi. “Ka cire uniform ka zo muje masallaci an kusa sallah” Ya fada yana direshi saman gado. “Okay Daddy” A nan jibril ya juya ya shiga bedroom din Nawwara, a gaban madubi ya sameta tana gyara kayan da ke gurin, a jikin kofa ya ya jingina yana kallonta har sai da ta kammala sannan yaje ya rumgume ta baya ya dora kansa saman wuyanta. “Ke baki gajiya da aiki ne? Ba na ce ki bari sai gobe mu gyara ba” “Haka kake ce min tun shekaran jiya ai, Noor ya dawo” “Eh ya dawo yana dakinsa uniform din islamiya zai cire” “Ya cire ya zo nan sai na masa duka ai” “Mi kuma yayi miki?” “Da ya gama cin abincin rana haka ya bar min plate a falo ya wuce islamiya kuma na sha fada masa ya daina min haka amman ya ki” “Saboda wannan zaki dakeshi” Ta yi shiru, sai kawai ya yi dariya ya kara rumgumeta, domin a yanzu ya saba da halin abu kadan zata ce sai ta hukunta shi ko Noor ko da kuwa abun be kai ya kawo ba, tun da ta dauki cikin nan ba wani zaman lafiya, kullum da kalar fitinar da take masa shi da Noor. A bakin kofar bedroom din Noor ya tsaya ya leko kansa dan yasan laifin da ya yi ya ce “Daddy muje an fara kira” Suna hada ido da Nawwara ya yi saurin komawa yaja kofar. “Ni gaskiya sai na dakeshi ko kuma kai na hukunta ka” “Hukunci ai ba zai wuce na cewar ba zamu ci miki abinci ba, ni kuma sai na dauki da na muje restaurant mu ci abinci mai dadi” “Ba dai irin nawa na” “Har ya fi naki dadi ga waiters din da iya tarbon baki” Ya fada yana kanne mata ido daya. Ita kuma ta dauki filo ta jefa masa ya gwace yana mata dariyar keta. Washe gari ma haka ta tashe da masifar ta kamar kullum, sassauci daya ta samu bayan Noor ya wuce school ya dora kanta saman cinyarsa ya bude suratul kaffi yana karanta, ita kuma tana saurare har bachi ya dauketa, bayan ya gama ya dauke kanta ya maida saman matashin kai ya shiga kitchen ya shirya musu abun karyawa, bata farka ba sai kusan goma na safe. Da taimakonsa tayi wanka ta saka abaya black, sannan suka dawo falo suna karyawa. Shi yake feeding dinta ita tana feeding dinsa kamar yadda suka saba har a gaba ko da kuwa Noor yana nan. Basu gama karyarwa ba aka danna door bell amalar akwai wani a bakin kofar, har ta kai je zata tashi sai ya zaunar da ita. “Bari na duba” Yana bude kofar ya karbi sakon da ke hannun mutumen sai ya maida kofar ya rufe, ya dawo yana
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119