Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 72

Chapter 72

Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel 1,197 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

saba'in. “Ka sake ni ko na maka ihu” “Ko kin yi ihu babu wanda zai zo” Ya fada idonsa a lumshe yana kara kwamtar da kaina a kirjinsa. “Kina jin yadda zuciyata take bugawa ko Naj saboda ke” “Idan baka sake ni ba zan sake zuwa aikin nan ba, daman saboda ka rika min haka ka tirsasani yin aiki a tare da kai ko?” Ya dora kansa saman kaina. “Ina ma zamu dawwama a haka” “Ba zan sake zuwa aikin nan ba” Ya yi saurin saki na. “Ina son ki sosai Naj ina miki irin son da wani da namiji be taba miki ba” “Ni kuma bana son..” Na kasa karasa saboda hannunsa da yasa ya rufe min baki, sai kuma ya duka kasan guiwoyinsa ya hade hannayensa. “Dan Allah dan Annabi Naj ki yafe min abunda na yi miki, dan Allah ki manta da komai” “Na manta da komai saboda ka san ka zalince ni ko? Mugu bakin azzalumi” “Ki kirani da ko wane irin suna zan karba miki, ki ayyanani a duk kalar mutumen da kike gani zan dauka, ki ci mutunci a gaban kowa zan jure matukar hakan zaisa ki yafe min” “Ba zai taba sa na yafe maka ba” “Fada min abunda zan yi ki yafe min Naj, ni kadai na san irin abunda na ke ji a zuciyana, na kan tsani kaina idan a duk lokacin da na tuna abunda na aikata miki, tunaninki ya haddasa min ciwo da damuwa, rashin kulawar nan taki ina jin kamar yana kokarin rabani da rayuwata ne, i will die soon Naj mai yuyuwa a wannan lokacin zaki tausaya min ki zo gaban gawata ki yafe min” Hawaye yake irin hawayen nan dake nuna tsantsar abunda ke zuciyarsa, ga nadama da damuwa nan ƙarara a fuskarsa. “Lokaci meeting yana wuce” Na fada tare da daukar takardun na nufi kofar fita. A ranar meeting hudu muka yi uku a cikin kamfanin daya kuma a wani kamfanin da muka je tare, sai dai sam babu walwala da sakewa a fuskar Jibril da ma yadda yake maganarsa da mu'alama da mutane, dukan abunda zan yi hankalinsa yana kaina, da muka dawo na yi sallah shi kuma ya dora alwala ya fita zuwa sallah a masallacin da ke kamfanin ni kaina ban taba sanin akwai masallaci a kamfanin ba sai yau, bayan na dawo ya cilasta min zuwa cin abincin rana kamar jiya, da muka shigo office ya dauko wasu takardu ya aje min wai na yi typing dinsu a computer shi kuma ya nemi wata kujera ya aje gaban teburina yana kallona har na yi aikin na gama. Tare da shi muka shiga mota, ya kawoni a inda ya aje jiya sannan ya mika min wata sabuwar laptop, wai da ita zan dinga zuwa office kuma na je gida ta aiki ce sai kuma na bukaci na kwashe duk abunda ke cikin wacan computer ta office na saka a laptop din, ni dai ban ce masa na gode ba balle sai anjima na fito na yi tafiyata. Ko da na isa gida yamma ta yi lis saboda yau na dade sosai a gurin aikin, na darar da gidanmu cike da mutane suna ta mana murna wai Sakina ta ci gasa an bata gida kuma wanda yasa gasar ya dauki nauyin karatunta sannan ya yi mata kyautar dubu dari biyu da hansin, ita kanta kamar zata hade kanta dan murya. Jibril kawai zuciyata ke raya min ya saka gasar nan, sai kuma daga baya na soma tunanin Mustapha domin shine a unguwar ya fi kowa sanin inda Sakina take karatu, har dare mutane nata shigo mana, Inna ta siye minti ta yi sadaka, bayan sallah isha'i Bilal ya kirani a waya na ki na daga sai ya aiko min da sako wai yana kofar gida, nan ma ban mayar masa da amsa ba jim kadan sai ga yaro ya shigo wai ana sallama da Nawwara, sai na yi karaf na ce “Je ka ce ba zata zo ba” Inna ta saki baki. “Ba zaki zo ba? Ba kyau wulakanta dan adam fa, Wallahi ki kama kanki, ni bana son yawan zuwan da ake ama miki sallama, wallahi ko aikin nan da kike zuwa hankalina be kwance yake ba, bani da kwanciyar hankali idan ba aure kika yi ba” “Inna Bilal ne fa” “To dan me ba zaki je ba?” “Wai birthday yayi yau shi da Zinatu suka yanka cake din kuma a gurin aikinmu wai har da kirana dan na gani” “Kishi kike kenan, ashe ana kishin abunda ba a so?” “Ni ina son shi” “Kina son shi kike nuna baki son shi? Kina son shi miya hana ki aure shi? Yanzu ke kina ganin zaki samu namijin da zai so ki kamar yadda Bilal yake son ki? Babu abunda ba a fada masa ba a kanki amman ya toshe kunne ya ce yaji ya gani shi dai son ki yake, kuma kina da ɗa shi yana saurayi kuma a haka yake son ki, babu irin kulawar ta cusa kai da be nuna miki ba amman kiki bashi dama, sai yanzu dan ya kula wata zaki ji haushi har ki zo kina kishi? Wane iriin zama kike son ku yi da shi? Shi dai aure yake son ki idan baki bashi dama ba ai dole yaje inda wacce zata bashi dama, Idan har son Bilal kike da gaske tau ki bashi dama ya ga magabatanki, sai ki yi kishi mai dalili, amman yanzu ai cin amanarsa zaki yi ki hana shi aurenki kuma ki ce ba zai kula wata ba?” “Amman Inna ai kin san yan gidansu basa so na, ni bana son na yi aure inda zan wahala ni da Noor” Na fada ina kuka, sai ta ce “Zaki wahala dai ke, Noor kan ai ba zai zauna tare da ku ba, duk son da Bilal yake nunuwa Noor ana daura miki aure dole a gida zaki barsa sai dai ya rika zuwa yana ganinki, saboda Bilal Saurayi ba mai mata ba, da ma ace yana da mata da zakiniya zuwa da danki ya rika shi, amman wannan kan ai sai ya kara kiyayyar ki ga yan uwansa kuma jama'a ma sai su zageni ace na bari aka je da yaro ya takura masa, ina tunanin ba a gidansu zai aje ki ba ko da ya aureki, dan haka yan uwansa su daina damunki ba akansu zaki zauna ba, indai mijinki na son ki babu wanda ya isa ya taka ki, sai dai ki shiryar fuskantar kalubale daga garesu” Na kara fashewa da kuka, ni dai har ga Allah ina son Bilal dina, kuma bana jin zan iya auren wani namiji bayan shi. *** *** *** Washe kamar marar lafiya haka na tashi jiki babu dadi zuciya ma babu dadi, bayan mun gama karyawa suka tafi makaranta ni kuma na gyara gida sannan na shiga na yi wanka ina fitowa na shirya cikin wata bakar abaya, da mayafinta, sannan na dauki laptop din da jakata na nufi dakin Inna ina mata sallama. “Amman dai ina tsoron ki rika wannan abun a hannu, kin san garin ne ko maza ya suka kare balle mata” “Ai kin ga a ciki jaka take ba wanda

Table of Contents

Chapters

119 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});