Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 61

Chapter 61

Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ba zaki fahimce ni ba, kuma abun zai tsaya miki a rai ki riƙa tunanin wanda ni kuma ba zan so haka, Wallahi ban ɓoye miki da wata manufa ba bayan wannan” “Ƴaƴan mazani kenan masu yarda da ƙawaye fiye da uwaye, masu yin gaban kansu waɗanda suke ganin kamar tasu zata fisshesu” “Dan Allah Inna ki yi haƙuri” Na faɗa ina kuka. “Amman da gaske Jibril ya baki haƙuri kuma kika mare shi ya ƙyale ki” Sakina ta tambaya, ni kuma na ɗaga mata kai. “Idan har yafiyarki yake nema ba zai tsaya jiran ki kawo kanki ya nemi yafiyarki ba, sai dai na nemi inda kike ya zo ya baki haƙuri kuma ya nuna miki ya yi nadama” Cewar Inna, ni kuma na ce. “Bana ma son ya zo dan ba zan yafe masa ba” “Allah ma aka masa laifi aka roƙi ya yafe balle ɗan'adam? Idan baki yafe masa ba ai kya bashi ɗansa idan ya zo karɓar abunsa” “Haba Inna duk wulaƙancin da ya yi min ya ce ɗan nan ba nasa ba ne sai kuma na bashu Noor gaskiya ba zan iya ba” “Akwai hujjar da ta zata hana ni ganin ɗansa ne?, idan har ya dawo ya buƙaci ɗansa ki bashi kawai shine masliha a gareki da kuma mu, ku bar shi da Allah Nawwara idan har kika yi haƙuri sai ki ga kyakkyawan sakamako daga gurin Allah amman matuƙar kika ce zaki rama abunda ya yi miki Allah zai iya barinki da dabararki a ƙarshe sai ki cuci kanki, amman idan har kika barshi da Allah sai ya saka miki. Ma a son mace da irin zuciya da halinki Nawwara, duk da zata iya ɗaga hannunta ta mari namiji ta kuma tsaya ta ci masa mutunci akan abunda zata iya kawar da ido ana mata kallon marar tarbiya kuma marar mutunci da kamun kai, raunin zuciya tausayi kawaici kunya haƙuri abubuwa da aka fi samu sun gurin ƴa mace, Na san Jibril ya zalinceki Nawwara, amman ki barshi da Allah karki yarda ki ce zaki ɗauki fansa wannan ba halin musulmin kirki ba ne” Daker na iya tsayar da kuka da na ke har na furta. “Ni ba zan iya yafe masa ba Inna” “Ban ce ki yafe masa ba, amman ki bishi a hankali kuma ki yi taka tsantsan” “Kuma ba zan bashi Noor ba be cancanci zama ubansa ba, ni ba zan iya yafe masa ba” “Har gobe ina faɗa miki rufin asirinki ne idan har ya dawo ya nemi ɗansa, ni kuma ban ce ki yafe masa ba” Sakina ta dawo kusa da mu tana faɗin “Amman gaskiya idan har aka bashi Noor ya ci riba biyu” “Ba riba ya ci ba, Wallahi ina da tabbacin Allah ba zai barshi hakan nan ba, wata ƙila ya jarrabeshi ko zai jarrabeshi nan gaba, duk ɗa ai ƴaƴan maza ne ba na mata ba, itama wani auren zatayi ta haifi wasu ƴaƴan, ni dai abunda na ke so da ke ki yi min alkawari zaki riƙe mutuncinki kar kuɗi da ƙyaliƙyalin duniya ya yaudari zuciyarki ya kaiki ga faɗawa halaka” “Na miki alƙawari Inna ba zan sake sakaki hawaye ba” “Allah ya miki albarka, ki je gurin aikinki ki koma kamar yadda ya buƙata, amman karki taɓa nuna masa saboda Bilal kika dawo, kar ki nunawa Bilal saboda shi kike aikin, ko wannensu ki nuna masa saboda kanki kike yi kuma zaki iya dainawa a ko wane lokaci, idan har kika bar aikin yanzu zai kori Bilal kamar yadda ya faɗa, wanda hakan zai jefaku ciki wani halin, kuma baki san ta wace hanyar zai ƙara ɓullo miki ba” “Amman Inna ina ganin kamar yana son ya yi amfani da damarsa ne ya sake cutar da ni” “Ba zai sake cutar da ke ba, waya sani ko saboda ke ya dawo garin nan da aiki? Wanda ma yake likita miya kawo shi aikin kamfanin? Baki taɓa tambayar kanki ba?” Na yi shiru ina nazari, sai Sakina ta yi karaf ta ce “Wata ƙila yasan ta samu aiki a kamfanin shiyasa ya zo” Inna ta amsa mata. “Nima haka na ke tunani, ƴaƴan manyan masu kuɗi basa ganin irinmu talakawa da mutunci, yana ganin kamar ƙasƙanci ne a gareshi yazo neman yafiyarkin kai tsaye, bana tantama shi ne ya aiko mana da ɓarayin nan kuma ya siye gidan nan saboda ki matsu ki koma aikin a kamfanin kamar yadda yake buƙuta ta yadda zai iya kyautata miki har ya nemi yafiyarki cikin sauƙi, da ace cutar da ke yake son yi da wata hanyar zai ɗauko ba wannan ba, kuma kin ga idan har yana da wata niyar ta daban akanki babu yadda za'ayi ya ki mareshi a bayanar jama'a ya ƙyaleki har ma ya risina ƙasa yana baki haƙuri, wannan saboda yana ganin bashi wata mafita sai ita ne shiyasa ya ɓullo miki ta hanyar Bilal” “Amman ina tunanin be san da Noor ba ko?” Sakina ta tambaya. Sai Inna ta amsa ta “Ya san ya barki da ciki, sai dai be sani ba ɗan yana raye ko baya raye, wata ƙila ma yasa an masa bincike akan haka, amman ki yi tunani Nawwara dukan mutumen da ya yi miki wannan wulaƙanci yana kunyar ya tunkareki kai tsaye ya nemi yafiyarki, kuma ta hanyar aikin nan da zaki yi a ƙarƙashinsa zaki iya fahimtar irin rayuwar da ɗan ki zai yi idan har ya zauna gunsa, ke da shi duka ƙurciya da wauta tana cinku” Shiru na yi ina ta nazarin maganganun Inna akwai hiƙima da kuma ƙamshin gaskiya a duk abunda ya faɗa, ni kaina na san da Jibril be yi nadama ban iya na masa irin wannan cin kashin a gaban ma'aikatansa ba, kuma babu dalilin da zai ya riƙa bibiyata har yana neman na dawo aiki. Ajiyar zuciya na sauke nasa hannu ina share hawayena, Inna kuma tana amsa sallamar da almajiri yake yi. “Assalamu alaikum wai ance ana sallama da Nawwara a waje” Da fari gabana ya faɗi na fara tunanin mai min sallamar. “Waye ne?” Na tambaya a cikin muryata mai amon kuka a cikinta. “Haka ya ce wai bawon Allah ne” Zan ƙara tambayarsa sai ga Noor ya shigo da gudu ya miƙa min wayar. “Momy ga Uncle Bilal ya ce na baki” Ina karɓa na kara a kunne already Noor ya yi picking. “Nawancy gani nan akan hanya” “Ka ce ma ka iso” Sai kawai ya yi dariya ya kashe wayar, jin haka yasa na ce da almajirin ya ce ina zuwa, wayar na miƙawa Noor ni kuma na tashi na je waje na wanke fuskata na shigo na shafa mai sannan na saka Hijabi na fita. Mustapha na tarar ƙofar gida sanye da jallabiya yana kallon ƙofar gidan, waigawa na yi gabas na duba yamma ban ga mai kirana ba hakan ya tabbatar min da cewar shi ne yaƙe kirana. “Miya kawo ka nan kuma? Kamin nan dai bari na fara taya ka murna ka yi nasarar haɗa ni da ƙawata ta faɗa min har abunda ban zaci zata iya faɗa min ba, burinka ya cika” “Ba burina kenan ba, burina ki yarda na tuba kuma ki yafe min” “Akwai aiki a gabanka babba

Table of Contents

Chapters

119 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});