Chapter 13
Chapter 13
isa gida na labartawa Habiba abunda idanuwana suka gani da kuma ji. My page is depend on your comments, ku da kuke cewa ina short page don't blame me, blame your comments 😂 Idan an gama karatu sai ku zo ki siya garin ɗan wake, da kuma ƙwaryar kwaliyar ɗaki ko falo da faifai duk domin ƙawata ɗakinki. Ga mai sha'awa sai a ku nemi number nan 08036126660 muna aikawa ko'ina a arewa cin ƙasar nan. Tau Lemme come and be going 🚶.... *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 1⃣1⃣ Tun da na baro kamfanin sai komai na titi ya riƙa burgeni, idanuwana har yanzu kallon komai suke kamar kamfanin wata ƙila saboda labarin da ke ƙumshe a bakina ina son na labarta musu Habiba da Inna yadda gurin ya ke da kuma aikin shi kansa. Tunawa da zancen Bilal ya sani dariya tare da furta sunansa a fili. “Bilal kenan wai zan sha fama da kishi” Ajiya zuciya na sauke ina tuna irin kallon da Mutune yake min ɗazu, lallai da akwai abunda Bilal ya faɗa masa akaina. “Sauke ni a nan” Na faɗa ganin Mai Napep ɗin yana ƙoƙari wucewa ta har cikin unguwarmu, ba kasafai na ke son napep ko achaɓa ya sauke ni ƙofar gida ba. “Ba ni canjin” Ya buɗe akwatinsa na kuɗi dake cikin napep ɗin ya ɗauko ɗari uku ya miƙa min, ni ko na ƙi karɓa. “Haba Malam ya zaka ɗauko ni daga Koko road ka kawo nan kawo nan arƙila kuma ka ce zaka cire har ɗari biyu” “Haba Hajiya kuɗin nan fa Mai gidane ya bada su ba ke ba, miyasa ku mata kuke son tauye mu ne wai” Hannu ya kai ya ɗauko naira hansin ya miƙa min, ina ƙoƙarin karɓa na ji takun mutun a bayana yana katsawa mai napep ɗin tsawa. “Kai wane irin mahaukaci ne zaka kawo mashin ɗinka a nan ka tarewa mutane hanya nonsense mtssssss” Juyowar da zan yi sai idanuwana suka yi arba da Mustapha, mutun na biyu da na tsana a duniya, ba da ni yake maganar ba amman sai na ji kamar da ni yake saboda tsanar da na yi masa da kuma sanin yadda baya ɗaukar kowa da mutuncin a unguwarmu. Tassss na wanke masa fuska da mari sannan na katsa mashi tsawa kamar wata uwarshi. “Haka kuke ba ku ganin kowa da mutuncin, kowa a gurinku wulaƙantaccene, uban kowa baka ganin mutuncinsa a unguwarnan, sha-sha-sha marar tarbiya” Mamaki da al'ajab ya kafe shi a gurin ya kasa ko da motsa idonsa balle ya yi wani motsi. Ni ko a zuciyata tsoro fal marata har ta cika da fitsari, amman a zahiri kallonshi na ke kamar yadda shi ma yake kallona sam ba zaka kalli fuskata ka gano akwai alamar tsoro a tare da ni ba. Matsowa ya yi kusa da ni ya ɗaga yatsansa ya nuna kamar zai yi magana sai kuma ya cige bakinsa ya yi ƙwafa ya juya koma cikin motarsa, ribas ya yi ya koma inda ya fito da alama ya fasa shiga unguwar ma. Sai a lokacin na samu sa'idar sauke ajiyar zuciya na juyo gurin mai Napep ɗin na karɓi hansin ɗin da yake miƙa min. “Kai amman ke wannan ƴar bala'i ce, Allah ya raba mu lafiya” Ba shi kaɗai ba ko mutanen da ke kusa da mu sun yi mamakin yadda na wanke mutun kamar Mustapha da mari, ni ba mafaɗaciya ba, kuma kowa yasan halin Mustapha a unguwarmu, ni kaina sai a yanzu na ke jin kamar ba ni ce na mareshi ba, wata ƙila kuma saboda na tsane shi ne shiyasa har idona ya rufe haka. Sai dai mamakina yadda ya ƙyale ni be rama ba, yaron da harararsa ma baka isa ka yi ba saboda yana taƙama ubansa wani ne a cikin garin sokoto. Da wannan tunanin da kuma mamakin dalilin ƙyaleni da ya yi na iso gida, duk wani ɗuki da na ke na labartawa su Inna gurin aikin sai ya kau saboda wannan abun da ya faru tsakanina da Mustapha ya tsaya min a rai. Ko da na shiga na samu Habiba tana da fa shimkafa da wake, Sakina na daka barkono (Yaji) Inna kuma na ɗaki kamar kullum. “Har kin dawo ashe ba a daɗewa” Cewar Habiba tana ƙara tura itacen murhu. “Eh kin san da yake ba aikin ba ne, takardun ne kawai za a kai” “Allah ya baki sa'a ya sa su ɗauke ki” “Amman Babban Kamfanine Habiba, ba lallai ne su ɗauke ni aiki ba” “Zan riƙa tufa musu fatiha a tsakar dare” Na yi murmushi, kana na doshi ɗakinmu dan cire mayafina. Bayan na fito na doshi ɗakin Inna, ita na fara labartawa yadda kamfanin yake kamin Habiba ta shigo mana da abinci mu soma ci gaba ɗayanmu, ko lokacin da Baba na dai baya ƙwanar ya ga mun raba abinci daga manyan mu har ƙanana, sai dai kowa ya wanke hannunsa a ci a guri ɗaya, yana yawan faɗa mana cin abinci tare yana saka zumuncin da nishaɗi da kuma son juna, kuma ta nan zaka iya karantar halin mutun da lurar shi irin cin abincin da ya dace ya yi. Hakan yasa suka muka saba bama iya raba abinci inda wanda za a ci ne, ko da ɗayan mu baya nan sai mun jira ya zo ko da kuwa Jamila ce ita da ta kasance ƙaramarmu, balle kuma Noor da ko ina muka je baya cin abinci sai da ni matuƙar ina gurin. Na bijiro musu da zancen marin da na yi ma Mustapha, a take hankali Inna da Habiba ya tashi har ma da Sakina “Ina ruwanki Nawwara ai ba da ke yake ba, kuma ko da ke yake ai kya shafa kanki lafiya ki bashi haƙuri, yanzu wannan abun da ya faru da mahaifinku be isheki ishara ba? So kike ki ƙara jawo min wani?” Cewar Inna. Habiba kuma ta ɗora da cewar “Da ma ba ki mareshi ba Nawwara, kar ya ce kuma zai miki wani abun, kin san halinsa idan ma ya ƙyale iyayensa ba za su ƙyale ba” Ganin yadda hankalin Inna ya tashi ƴasa ni yin ƙarya. “Ke wasa na ke daman kawai ina son naga yadda zaku yi ne, ban mare shi ba kuma da ya zo yana faɗa da mai Napep ɗin ma na bashi haƙuri” “Da Gaske?” Na gyaɗawa Inna kai ina dariya saboda ta yarda. Sai dai na lura da Habiba kamar bata yarda da ni ba, har muka gama cin abincin ban ga yanayin Inna ya dawo dai-dai ba. Bayan sallah la'asar Jidda ta shigo gidanmu, a lokacin ina zaune waje ni da Habiba Inna kuma tana ɗaki, Sakina da Noor da Jamila suna islamiya. Kusa da ni ta zauna ina kallin bakinta na san da akwai magana, sai dai tana tsoron furtawa ganin Habiba na kusa da ni. Murmushi na yi na ce “Saki jikinki Jidda faɗa min ko minene ai Habiba kamar ni ce, dukan abunda kika sani nawa to Habiba ta rigaki saninsa, abunda duk na ke iya faɗa miki to Habiba ce ta fi cancanta na fara faɗawa, ni da ita abu ɗaya ne bama ɓoyewa juna abu” Sai ta yi ƴar dariya. “To ai ban sani
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119