Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 33

Chapter 33

Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

lokacin da ya dawo daga makaranta, yana ta tambayar ina Momy nace mishi kina gurin aiki amman daker ya yarda ya tafi islamiya, ɗanki yasan zafin rabuwa da mutun yasan idan aka tafi ba a dawowa shiyasa saboda ya rabu da Habiba dan haka ba zamu iya jure rashinki ba” Tana faɗar hakan tasa kai ta fice idonta cike da ƙwalla, ni kuma na jingina na lumshe ido ina sauke ajiyar zuciya, wani irin tausayinta ne ya rufe ni. Jin wayata tayi ƙara yasa na buɗe ido na nufi inda wayar take, tun kamin na ɗauka gabana na faɗi saboda saƙone daga One-On-One Limitless Company, ji nayi bana da buƙatar sanin abunda saƙon ya ƙumsa, dan haka na danna delete na goge shi ba tare da na karanta ba. Sai da na gama rama sallah azahar sannan na gabatar da sallah la'asar, sai na zauna na ci abincin sai ba sosai ba saboda bana jindaɗin abinci a yanzu, sai dai shigowar Inna yasa na zage dantse na yi ta auna abinci domin nasan zata damu idan ta ga banci da yawa ba. Na yi ƙoƙarin ganin na danne damuwata amman mahaifiya ta fi gaban wasa ita da kanta ta tsinkayi hakan a cikin idona. “Nawwara kamar akwai abunda yake damunki, idan dai dan maganar aikin nan ne ki kwantar da hankalinki Allah zai sake baki wani kamar yadda ya baki wannan” Kai kawai na iya ɗaga mata domin na gansu maganar aikince kamar yadda take hasashe, domin idan har ta tiƙe ni ban san mi zan faɗa mata ba. Tashi tayi ta fita jin wata maƙociyarmu ta shigo, ni kuma na rafka uban tagumi ina kallon ƙasa amman hankalina yana can gurin rayuwata ta baya. FLASH BACK. _“Yau za'ayi ina fatar zaka samu zuwa kai da madam, tau ya yi sai kun ƙaraso”_ _Haka na ji ya faɗa a waya, sannan na miƙe tsaye yana min wani gumun kallo ya ce._ _“Wallahi duk kika sake abokaina suka zo gidan nan kuma kika fito sai na halakaki, kinji ni ko?”_ _Da sauri na ɗaga masa kai hawaye na zuba a idona, sai ya kaɗa kai fuska babu annuri ya nufi ɗakinsa yana wani irin jinkansa, ni kuma na zube a gurin ina kuka saboda zafin ruwan zafin da ya watsa min a hannu kuma ya hanani kuka saboda tsabar zalumci. Ina a gurin ina aikin kuka har ya shirya ya fito sai ƙamshin turare yake ya tsaya a kaina ya nuna ni da yatsa_ _“Ki shiga cikin ɗaki ki kulli kanki karki yarda ki fito”_ _Na amsa masa da tau jikina na rawa ina ta ƙoƙarin haɗe kukana nasan idan har na yi kuka a gabansa zai iya dukana, kamar yadda ya umarce ni haka na shiga cikin ɗakin na rufe kaina wanda hakan ya bani damar tausayawa kaina da kaina. Can zuwa dare na soma jin hayaniyar abokansa ta hirar da suke na iya gane ashe muƙamine ya samu amman ya gagara faɗa min saboda ƙiyayyar da yake min, haka yake duk lokacin da wani abun ya sameshi sai dai na ji a waje ba dai ya faɗa min ba. Har suka yi abunda zasu yi suka gama ban fito ba, bayan fitarsu da minti ashiri na ji an buga ƙofar ɗakina, yanayin yadda aka banki ƙofar ne ya fahimtar da ni cewar Jibril ne yake buga ƙofar, cikin hanzari naje na buɗe saboda na san baya son jira, sai nayi arba da yatsunsa biyar a kuncina, ma'ana wanke min fuska da mari yana faɗin_ _“Ke kiƙa faɗawa Abbah zanje meeting ba dake ba ko?”_ _Baya-baya na yi ina girgiza masa kai_ _“Na rantse da Allah ban faɗa ba, Wallahu ba ni bace”_ _Na faɗa cikin kuka, sai ya watsa min harara, yace na canja tufafi muje amman duk na masa kuka cikin mutane sai ya ɓanlani, jin wannan yasa hawayena ya yanke tun kamin ma mu fita domin na san haƙinsa ne sarai zai iya ci min mutunci a gaban kowa, sai dai ban daina jin zafin marinba har muka isa gurin da ake tare, gurine dake cike da manyan mutane an ƙawata gurin anyi masa kwalliya gwanin sha'awa. kowa da mazauninsa, an kasa mutane daban-daban wasu na tare da matansu wasu kuma na tare da familysu. Tare muka shigo da shi amman muna shiga harabar gurin sai yayi kamar be sannin ba tare da gargaɗina akan karna yarda na nuna cewar ni matarsa ce. Guri na samu kusa da wasu baƙin na zauna, bayan an gama jawabin da akeyi aka kirashi aka karramashi, sai yaje ya karɓi Award ya yi jawabi godiya, a lokacin Abbah da Hajiya basa nan dan haka babu wacce zai kira bayan su sai ni da nake matarsa, amman abun mamaki sai ya kira sunan budurwarsa Asiya ko kuma ma nace karuwarsa, haka ta miƙe tsaye tana ta karairaya ta haura gurin tana taya shi murna. Ni kuma ina daga nan zaune ina hawaye_ _Wani mutun ne ya miƙo min tissue yana min kalaman da mijina abokin rayuwata be taɓa min ba_ _“Kuka be cancanci kyakkyawar fuskarnan taki ba dan Allah karɓi ki share hawayenki”_ _Kallonsa na yi amman na kasa karɓa saboda idon Jibril na kaina, haka mutumen ya matsa min amman naƙi kula shi har aka tashi taron, a gurin da zamu shiga mota ya tare mutumen ya riƙa bugar masa baki wai ya yi magana da matarsa, babu kalar baƙar maganar da saurayin be faɗa masa ba, sannan aka rabasu ni kuma ya sakoni gaba muka dawo gida, kamar jira yake mu iso ya sakani gaba da duka wai na kula wani namijin har wani huci yake kamar zaki..._ BACK TO STORY Shigowar Noor ne ya katse min tunani, sai ya yi saurin aje allon dake hannunsa ya nufo yana share min hawayen da ban san sun zubo ba. “Momy miyasa kike kuka? Shiru shiru shiru kinji Allah ya miki albakar, yi shiru shiru faɗa min waya taɓa ki?” Shine abunda yake faɗa tare da saka haɓar rigarsa ya goge min fuska, ina kallonsa gabana ya faɗi fuskar Jibril ce shimfiɗe a fuskarsa babu inda ya ragoshi tun daga kan hancinsa har ido da baki da fari komai na ubansa ne, rumgumeshi nayi muka kwanta saman kafitar da nake zaune. _“Ba cikina ba ne...!”_ Shine abunda ya faɗo min a rai, sai na ƙara ƙanƙame Noor kamar ance za a rabani da shi. Bachine ya kwashemu ni da shi bamu farka ba sai da Sakina ta shigo tana tashina wai anyi magariba. Bayan Sallah isha'i Bilal ya kirani a waya yace min yana ƙofar gida, nasan daman zaizo tun da yau ban karɓi kuɗin da ya saba bani ba. Sai dai na sha mamaki lokacin da fita muna fira da shi. “Miyasa kika fita Kamfani ɗazu kina kuka?” Shine abunda ya fara tambayata, nasan wata ƙila wani ne ya faɗa masa, ni kuma sai na masa ƙarya da cewar saboda sun ƙoreni yasa ni kuka, ya nuna min damuwarsa sosai har ma ya yi alƙawarin zai yi wani abu wajen ganin an maidani aikin, amman na nuna masa bana so. Sai tara da rabi muka rabu ban faɗa masa cewar na suma a titi ba duk na san nan gaba kaɗan

Table of Contents

Chapters

119 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});