Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 28

Chapter 28

Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Bilal ya kan shigo har cikin gidan saboda bana fita ya riƙa min nasiha yana jana da hira wai ko zan sake amman ina na kasa kai zuciya nesa, Jidda ma ta yi iya yinta har ta gaji ta sa min ido. Haka na kwashe sati biyu babu wani canji tsakanin ni da Noor domin shi ma idan yana bachi kiran sunanta yake, idan zai ci abinci sai ya ambaci sunanta saboda mun saba cin abinci tare, da an taɓa shi ya buɗe baki yana kiran Mama Habiba. Ranar da ta cika kwana goma shabiyar a ƙabarinta ina zaune waje ina karatun ƙur'ane Noor ya kwanto jikina yana kuka. “Momy miyasa idan aka mutu ba a dawowa?” Kallonsa na yi, da farko rasa na yi mi zaɓ ce masa sai kuma na yi ƙarfin halin ba shi amsa. “Haka Allah yaso, kuma duk wanda ya samu lahira baya ƙaunar dawowa duniyar nan, sai dai mu iskeshi” “Momy nima ina son na mutu naje inda Mama Habiba, kullum ina mafarkinta bana jindaɗi idan bata nan” Ya faɗa yana kuka, sai na rufe ƙur'ane na aje gefe na kwantar da kansa saman cinyata ina shafa kansa, shi kuka ni kuka. Na yi kuka sosai har sai dai na jawa kaina ciwon kan da ban taɓa irinsa ba, domin har cikin ƙashin bayana yaƙe sauko min, a ranar bana iya ko da motsin kirki har sai da aka kira wani nurse ya duba ni ya bani magani. Wasa wasa ciwo ya fara min yawa yau ciwo gobe lafiya tun abun be kama Inna ba har ya soma bata tsoro, sau biyar ana min ƙarin ruwa amman kamar zubarwa ake, duk nabi na rame na lalace farar fatata ta soma ɗuhu, gashi bana iya cin komai. Haka Inna zata saka ni a gaba tana kuka tana cewa ni ma rasa ni zata yi, damuwar da nake ganin tana ciki ne yasa na ragewa kaina tunani ta yadda zan samu na riƙa cin abinci ko da kaɗan ne, domin nurse ɗin ya faɗa min matuƙar ban daina tunani ba ba zan taɓa jin sauƙi ba, kuma ba zan taɓa iya cin komai ba, idan zan kwanta sai na shimfiɗa zanen da Habiba take shinfiɗawa na yi matashin kai da fillonta hakan yasa sai ma ji kamar tana kusa da ni. Da addu'o'i da ƙarfin hali na fara samun sauƙi, cikin sati ɗaya na koma normal sai dai ban iya maida jikina ba, lafiyata ma bata dawo gaba ɗaya ba, amman Alhamdulillah na dawo cikin hayyacina ma miƙa lamarina ga Ubangijina, har na kan fita naje gidansu Jidda saboda rage kewa, Bilal kuma ya yi min sallama na fita mu gaisa na tattara komai na adana a zuciyata, na tabbatar da ace ana buɗe zuciya da tawa zuciyar idan aka buɗe ba za a tarar da komai ba sai damuwa, baƙincikin, tunani, da kuma hudu na rashin RAI BIYU da na yi. Walwalar da nake tasa Noor ma ya sake har yana sawarsa da yara, sai dai duk da haka idana ka masa wani abu sai ya shigo yana kuka ko ya ce da Mama Habiba na nan da yanzu ta rama masa, Sakina ce ta ɗauke halin Habiba a gidanmu duk wani aiki da Habiba take Sakina ce take yinsa a yanzu, Noor ma idan aka masa wani abun itace kan gaba wajen magana, sosai take ɗauke min kewar Habiba daman suna kama sosai da Habiba ta fuska da kuma ta magana, inda suke da banbanci Habiba tana da tsawo ya yinda Sakina take gajeruwa sai dai ba can sosai ba. A kwana a tashi hasarar mai rai! Wasa-wasa kwanaki suka soma ja, har Habiba ta haura wata ɗaya da rasuwa, a zuwa yanzu kan mun fara sabawa da rashinta, sai dai duk da hakan kewarta bata bari na bachi har sai na kwantar akan shinfiɗarta. Ranar da Inna ta fita wanka, wato ta gama taƙaba sai mutuwar Habiba da ta Baba ta dawo mana sabuwa. Mutane da dama kama daga ƴan'uwa, maƙota abokan arziki suyi ta shigowa suna mana barka da fita wanka da Inna ta yi lafiya. Sai dai babu Family Bilal ko ɗaya da ya zo mana barka da fita wanka, hakan be bani mamaki ba daman can na san ƴan gidansu ba son alaƙar dake tsakanin mu suke ba. Bilal kan sai dare ya zo, ya kawo ma Inna atamfa vilisco ta dubu biyar da kuma wax ita ta dubu biyar da Hijab mai kyau yadi huɗu, sai turaruka da man shafawa da kuma kayan ciye-ciye da tanɗe-tanɗe, abunda yan uwan Babanmu suka kasa yi, ko atamfar roba ka rasa wanda zai siyo ya kawo ma Inna da suna ta saka na fitar wanka saboda rashin haɗin kai da kuma halin ko'in kula nasu. Duk yadda Inna ta so ta rage kaya sai Bilal yaƙi yarda wai idan har ta mayar masa hakan na nufin bata ɗauke shi ɗa ba. A bakin ƙofar gida muka tsaya muna fira da shi, a nan yake min zancen aikina wanda ni har na watsar da lamarin. “Ya kamata ki koma kin ga idan kina fita zaki fi sakewa, kuma ita kanta Inna zata ji daɗi” “Amman Bilal ni aikin ya fita daga raina ma” “Aiko yanzu ne ya kamata aiki ya shiga kanki domin Sakina da Jamila da Noor suna da buƙatar taimakonki, ga kuma Inna” Gaskiya ya faɗa tun da bamu da wasu ƴan'uwa masu son taimako dole ne mu tashi mu nemi namu, daman hausawa na cewa ‘indan ma ɗan'uwa nemi naka’ Ajiyar zuciya na sauke na kalleshi duk da kasancewar ba zan iya ganinsa ba saboda babu hasken farin wata, ita kan wutar nepa na manta rabon dana ganta a gidanmu domin an daɗe da yanketa, sai dai idan maƙota sun kunna wuta hasken gulob ɗinsu na haska gidanmu musamman masu gidan samman nan dake kusa da mu, sai dai yau basu kunna ba sakamakon babu wutar gaba ɗaya a unguwa. “Amman basu kore ni ba? Na daɗe ban zo ba” “Na basu rahoton cewar baki da lafiya, dan haka idan kin shirya zuwa kije kawai” “I will try” Na faɗa ina tsotsa lips ɗina. Bayan zancen aiki sai kuma muka ɗora da wani zancen na daban, ba laifi na saki jiki mun yi fira har da dariyata kamar ba ni ba, da wannan na yarda cewar zuciyata ta fara zaurancin son Bilal domin ina jin nishaɗi a duk lokacin da muke tare da juna, ko sunansa na tuna sai na samu kaina cikin hauƙi da murmushi. Bayan kwana biyu da faruwar hakan na shawarci Inna akan maganar aikina, na yi zaton zata hanani ne ko tace wani abu sai naga ta nuna farinciki sosai har tana ce min wai na fara dawowa a mutun ɗinta, farincikin dana gani a tattare da ita ne ya ƙarfafa min guiwa na yi jimmar wanke uniform ɗina na zuwa aiki. Washe gari na shirya tsaf na ɗauki Hijabina na saka, sai kuma na buɗe jakar da nake aje tarkace na na ɗauko ƙaramin hoton Habiba na saka a aljihu, hakan zai kwantar min da hankali kuma zai ƙarfafamin guiwa domin a duk lokacin da nake kusa da wani abu da ya danganceta ina jin

Table of Contents

Chapters

119 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});