Chapter 90
Chapter 90
kamin ya aureni, sai ya zamo baya ganin kimata kuma rashin yarda ta shiga tsakaninmu har ta kai shi da kansa yake cewa ko ya aureni ba zai samu natsuwa ba domin zuciyarsa tana raya masa bayan shi zan iya taraiya da wasu mazan, ina ji ina gani Jibril ya auri wasu matan ya bar a lokacin na ko sunana baya son a kira, ni kuma na gagara samun wani mijin aure na kirki saboda kowa kallon yar iska yake min, saboda na riga na gama zubar da mutunci na tun a yanayin suturata, duk wanda yanzo ba da aure zai neme ni ba sai dai da lalata ko kuma soyayya, wadanda suka zo neman aurena da gaske kuma sai a bi a zuge, a haka zama garin Abuja ya gagareni na koma gurin Yayata Kaduna, na natsu sosai a lokacin na zama ta kwarai fiye da yadda kike tsammani, amman mutuncin da na gagara tsarewa tun a wacan lokacin sai ya kasa bani damar na yi rayuwa yadda na ke so, a haka na fara shafa man nan na mai saka haske wai ko farina zai karu na kara burge maza amman a banza sai ma lalata fatata da na yi, ke ce kadai kika tsaya min a rai ina gani kamar hakkin ki ne yake bibiyata dan Allah dan girman Allah dan darajar Annabinsa ki dubi girman Allah ki yafe min Nawwara” Kuka take sosai tana kokarin kama kafafuna, wanda hakan ke tabbatar min da cewar lallai Aysha ta yi nadama, sai dai me abunda bata sani ba, ba hakkina ne kawai yake binta ba, tabbas hakkin aure ba zai barta ba saboda ta tozarta da aure a lokacin da ta samu dama, amman an baro kyau tun ranar haihuwa, domin kuwa ta yi abun da yan mata yanzu suka dauka wayewa wato bayarda kai ga Namiji tun kamin ka aureshi da kuma shigar banza wacce Annabi Allah da kansa yake cewa masu wannan shigar tufafin ba zasu shiga aljannaba kuma ba za su ji kamshinta ba, taya namijin da ya sakin tun a gidanku zai yarda ya aureki? Ko da kuwa ya aureki ba zai taba ganin darajar ki ba kuma babu aminci na zaman aure a tsakaninku har a bada ga kuma azabar Allah tana jiranki matukar baki tuba ba, daman shi namiji duk abunda ya aikata ado ne, ko ina a qur'ane idan Allah zai ambata da da namiji yake farawa sannan mace amman da aka kai babin Zina sai Allah ya fara da macen kamin namiji saboda mace tafi shiga tarko kuma idan bata bada dama ba babu yadda za ayi ta namiji ya aikata. Ajiyar zuciya na sauke zan yi magana sai ga text ya shigo a wayata na Jibril, wai an sallami Noor kuma ya tafi gida da shi sai gobe za su zo nan. Aje wayar na yi na kalleta zan yi magana sai ga Inna ta shigo cikin dakin tana tambayar lafiya jin shisshikar kukan Aysha. ____________________________________ Al-hamdulillah godiya ta tabbata ga Ubangijin da ke ba mu lafiya da rashinta, na samu sauki sosai na gode sosai da kukawarku da addu'o'inku Jazakallahu Khairan 😘 Let my advice be here, For those ladies da suke daukar mallaka kai ga saurayi ko da an muku engaged a matsayin wayewa ko soyayya Wallahi babu soyayya babu wayewa a cikin zina, kuma ko da mutun ya aureki baki da wata kima da mutunci a idanuwanshi, wani ma ba zai aureki ba kin ga kin ga kin zubar da mutunci a banza, kar kalaman banxa su yaudari zuciyarki kar karatun wasu littafan yasa ki rika daukar saka suturar banza a matsayin wayewa Wallahi ba duka writers ba ne include me suke rubuta dai dai ko rashinsa ba me some of our readers suna daukar dukan abunda aka rubuta ko abunda duniya take yayi a matsayin wayewa wanda sam ba haka ne kama mutunci da kimarki shi zai nunawa duniya ko wacece ke kuma mijinki da yayanki zasu yi alfahari da wannan, kar ki ga wata ta yi haka at the end ta auri a mijin kwarai a novels ne ko movies irin wannan abun yake faruwa, in reality 75% basa auren mutanen kirki matukar kika maida kanki karuwa babu namijin kwarai da zai so ki a matsayin matarsa, su ma mazajen na banza ai matan kwarai suke nema su aura, be wise, women with attitude na kwarai a lady with class class din kuma na kare mutunci ba na zubarwa, ko da ke ta kwarai a irin shigar da kike wani zai dauka ke yar iskace ko kuma marar tarbiya. Some will say ya zata kawo mana wannan dogon sharhin nan ko? 😂 Wallahi abun yana ci damuna ne sosai kuma wannan ce kadai damar da na ke da ita wanjen yin wannan bayanin. Wanda na batawa rai ya yafe min Allah ya shirya mu gaba daya. See you next page i can't wait na ji labarin da Rabi zata bawa Nawwara 💃idan Nawwata ta ji za tayi wani abu kuwan? Anya Iayayen Bilal zasu bari ya auri Nawwara kuwa? Duka zai zo a next page Inshallah. 😘 [11/8, 9:37 PM] +234 703 352 5246: *RAI BIYU...♥🖤* Wattpad @KhadeejaCandy _This Chapter is yours Auntie Sis♥_ 5⃣0⃣ “Lafiya?” Inna ta tambaya. “Lafiya kalau magana ce kawai muke” “Kin tabbata?” “Ba komai Inna” Ba dan ta yarda ta juya ta koma waje, ni kuma na gyara zamana na kalli Aysha na ce “Ba ni kika cuta ba Aysha kan ki kika yi ma, daman duk mai cutar wani yana jin dadi kansa yake cuta domin alhaki zai dawo akansa wata rana, idan ma hakkina ne yake bibiyarki Wallahi na yafe miki daga yau ba zai sake binki ba” Dagowa ta tu ta kalleni da idanuwanta da take faman kuka da su bakinta na rawa ta ce “Wallahi Nawwara ke ta daban ce ban tsammaci zaki yafe min da wuri haka ba, na gode sosai Allah ya saka miki da Alheri” “Amin, amman dan Allah ina son ki fada min taya aka yi kika gane gidanmu?” Sai da ta share hawayenta ta koma saman kujerar ta zauna daidai sannan ta kalleni “Siraj ne ya kwatanta min” “Siraj kuma? Waye haka” Na mata kamar ban san waye shi ba. “Wani abokin Jibril ne, shi kadai ne wanda Jibril ya aminta da shi a yanzu, shine kadai mutumen da yake karfafa min guiwar cewar zai yi duk yadda zai yi wajen ganin Jibril ya aure ni” “Yanzu kina nan akan bakarki cewar Jibril rai aureki duk bayan yaudarar da ya yi miki?” “Bana jiransa shi kadai, idan wanda zai aureni da gaske ya zo zan aureshi, na dade da yafe masa abunda ya yi min saboda na san tun farko laifina ne ba nasa ba, kuma har gobe ina son Jibril” Na sauke numfashi a hankali ina mamakin karfin hali irin nata son wanda baya son ka, ko da yake ya so ta da farko,amman ai ya cuce dan me zata wahalar da kanta gurin son sa. Kamar ta san abunda ke raina sai kawai ta ce “Na san za ki yi mamakin jin har yanzu ina son Jibril, ke ma da ace kina son shi tun farko ko kuma
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119