Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 44

Chapter 44

Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

taru a gidan kowa ya keɓe wani ɓangare nasa ya kafa nasa iyalin. Lokatuta da dama takan keɓe ita kaɗai ko kuma da mu tayi ta kuka tana roƙon Allah ya bawa mahaifina wani aikin duk da bashi da wani karantun zamani a wacan lokacin, muna haka wani maƙocinmu Malam Buba kuma abokin Baba da yake yawan zuwa Abuja ya faɗa ma Mahaifimu cewar wani attajirin mai kuɗi a garin Abuja yana neman mai masa gadi kuma ya ce baya buƙatar kowa sai bahaushe ɗan'uwansa, Malam Buba ya kasance yana masa gadin wani babban kamfanin siyer da kayan alatu ne dake can garin Abuja. Muna zaune gida ranar wata talata, bayan mun gama cin kwaɗon ƙanzo, sai Baba ya shigo da far'arsa yana labarta mana abunda Malam Buba ya faɗa masa, Inna ta yi murna sosai kuma ta nuna jindaɗinta, a nan suka yanke shawarar ba zasu sanar da Yakumbo da Hajiya ba saboda sunsan ba zasu bari yaje ba, sai suka haɗa kai da Malam Buba ya faɗa musu Babanmu zaije Abuja ya kai fatune saboda ana bukatarsu a can, sun yi na'am suka masa addu'ah da fatan nasara, sai Baba ya karɓi fatun bashi da sunan idan yaje can zai aiko da kuɗin. Ranar da zai tafi munyi kuka sosai ni da Inna har ma da wasu mutanen gidan saboda muna ganin kamar ba zai dawo ba, tafiya nisa kuma har garin Abuja garin da a wacan lokacin muke ɗaukarsa kamar wata ƙasar dabam. Bayan wata ɗaya da tafiyar mahaifinmu sai gashi ya dawo cikin shigar mutunci da kamala, sai dai ya ɗanyi rama kaɗan ya kuma yi haske, ya labarta mana komai yake muna nan cikin ranshi wannan tunanin ne ya hanashi ƙiba, har ma yake faɗa mana cewar mai gidansa ya ware masa wani ɓangare na gidansa ya bashi ya ce ya ɗauko iyalansa su dawo nan kuma ya zo mana da kuɗi mai yawa. Ba ƙaramin yaƙi akayi ba kamin Hajiya ta yarda ta barmu aka tafi da mu, a nan ma sai da ya yi mata wata ƙaryar cewa ya canja sana'a yanzu yana siye da saida takalma ne na fatu har ma ya ce mata hayan gida ya kama a ƙauyen Abuja acan zai zauna da mu ya cigaba da sana'arsa. Amaina huɗu a mota kamin mu sauka zaria, aka siya min abinci da ruwa na cika cikina ni da Habiba sannan muka cigaba da tafiyar, ko da muka shiga garin Abuja ina bachi, sai da motar ta tsaya sannan Inna ta tasheni muka koma can wani ɓangare na tashar, Baban mu ya ari wayar wani ya kira Alhaji ya sanar masa mun iso domin ba a shiga da wani abun haya a unguwar. Dare ya yi sosai har Baba ya yanke shawarar zuwa gurin abokinsa Malam Buba mu kwana a can sai ga ƴan komisho sun zo suna neman Malam Musa Kafinta, a nan suka haɗa mu da mutumen yanayin yadda Baba ya gaisa da shi sai ya tabbatar da cewar ya sanshi, ashe direban Alhajin ne. Ni da Inna duk da tsoro muka shiga motar saboda ganin Babbar motar kamar wannan wacce ni dai zan iya rantsuwa hannuna ma be taɓa kaiwa akanta, amman yau zan shigeta. Ina ta rabon ido har muka iso wata kyakkyawar unguwa. Idona be ƙara buɗewa har sai da muka iso cikin ƙaton gidan dake cike da ababen more rayuwa. Iyalan mutumen ne da Alhajin shi kansa suka fito suna tarbonmu, har yake bawa Baba haƙuri akan rashin ɗaukoshi da wuri wai yaje meeting ne kuma sai ya manta sai da ya dawo gida sannan ya tuna. Cikin Falonsu muka shigo sai suka saka mai aikinsu ta kwashi kayanmu ta kai BQ, mu kuma suka kawo mana abinci da abin sha. Cikin sati ɗaya muka sake da ƴan gidan kasancewarsu mutane da suka san darajar ɗan'adam tun daga Hajiyar gidan har yaranta, Ƴaƴanta maza biyu manya sannan mata uku ɗayar tana aure sauran biyu kuma a lokacin suna karatune, sai ƴar ƙaramar ƴarta Salima, wacce ta kasance ta shida a cikin yaranta takwas. Shaƙuwa sosai da sosai ta shiga tsakanina da Salima, har ta kai zuwa makaranta ne boko ne kawai yake rabamu, kasancewar ni bana zuwa bokon sai dai islamiya Alhaji Dahiru wato mahaifinta ya sakani Islamiyarsu. Duk ƙarshen wata Baba yake zuwa gida duba Hajiya, wani lokacin kuma sai dai ya yi mata aike a haka muka kwashe shakara ɗaya a gidan Tsohon ambasadan nigeria a ƙasar London, muka zama kamar ƴan gida, shaƙuwa sosai ke ƙara shiga tsakanina da Salima, da kuma Babban yayanta Jamal, shi yake koya min karatu duk da ba a sani makaranta ba a lokacin, Jamal mutum ne mai son jama'a da far'a, har ta kai idan be ganni ba sai ya aika an kirani, bayan ya gama koya min karatu sai ya ce na yi masa gatana, ba laifi a lokacin na iya zuba gatana har da wacce ba'a taɓa yi ba, haka zai zauna ya yi ta saureren shirme na wani lokacin har da Hajiyarsu. Shi ya fara yaba ƙwazo na sai ya yi ma mahaifinsu magana aka sakani a makarantarsu Salima, na kashe kuɗi sosai gurin samo transfer dake nuna daga wata makarantar na ke, sannan aka samu sa'a aka sakani aji ɗaya da Salima, Habiba kuma aka sakata wata maƙarantar wacce ƙannen Salima suke yi. Tare muke zuwa mu dawo, mu tafi islamiya tare, wasa-wasa sai na tattara kayana suka na koma ɗakinta da zama, a lokacin Inna na da cikin Sakina, komai a iri ɗaya muke da Salima bana da ƙawa sai ita itama bata da ƙawa sai ni, idan ba a ganta ba sai an tambayeni haka itama. Ta ɓangaren Jamal kuma soyayyace mai ƙarfi ta shiga tsakaninsu duk a lokacin ban san miye so ba, na kan samu kaina da tunaninsa da kuma rashin jindaɗi a duk lokacin da baya gida. Muna daf da ƙare makarantar secondary school ni da Salima Hajiya ta samu labarin cewa Baba gadi yake a wani gida, babu irin bala'in da bata mushi ba cikin har da zance zata tsine masa gidan be dawo ba, wai Inna zata kaishi ta baro yana biye zancen mace. A dole tasa Baba ya tattara ya koma gida sai dai be zauna gidan ba sai ya kama haya kusa da su inda muke zaune har yanzu. Ni kuma a aka barni nan da sunan idan na gama zana jarabarwar za a maidani gida, bayan mun gama jarabarwa ta fito ta yi kyau, a lokacin ne ɗan wani mai kuɗi ya fito neman auren Salima, Alhaji Dahiru ya yi na'am ya sallama masa bisa sharaɗin zai jirata ta yi karatu na gaba, a lokacin shi kansa yaron be kammala karatunsa da yake ba. Bayan sati ɗaya da faruwar haka sai Ya Jamal ya fara min zancen aure, ni kuma ina ta tsoro saboda ina ganin kamar iyayensa ba zasu yarda ba, sai na nuna masa bana son shi, duk abunda muke a tsakaninmu ne iyayensa basu sani ba, har Salima ma tada zame min jinin jiki ban taɓa labarta mata ba, shi ma kuma be taɓa nunawa kowa ba. Bayan takadun mu sun fito sai Alhaji Dahiru wanda muke kira da Daddy

Table of Contents

Chapters

119 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});