Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 12

Chapter 12

Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel 1,207 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Kai kawai na kaɗa, na bi bayansa yana gaba. Faɗuwar gabana ne ya ƙaru yayinda da muka doshi ƙaton gate ɗin nan, yana isa suka buɗe masa ƙofar da biyo ɗazu ya wuce suna zolayarsa ni kuma ina bayansa. Tafiya mika mai nisa sosai sannan muka isa katafaren kamfanin, hakan ya bani damar kallon gurare da dama a harabar gurin, daga dama wani ɗan madaidaicin guri ne mai kamar ma'aikata an rubuta masa RESTAURANT, sai kuma wani ƙaranin gate dake can hagu an rubuta masa PARKING SPACE, a can gefen gurin kuma an wani gate ne mai zagaye da falawoyi an rubuta masa GARDEN GROVE. Duka cikin manyan harufa masu ƙyali da burgewa. “Gurin nan na da girma sosai Bilal” Na faɗa ina kallon gaban kamfanin da duk madubi har takalminka kana gani a ciki da duk wanda zai zo bayanka, gida sama ne mai hawa biyar, na gane haka ne ta windows ɗin dana ƙira, hawa-hawa har biyar. “Yeah kin ga can gurin cin abinci ne, can kuma duk wani mai abun hawa can zai aje shi, garden kuma gurin hutawa ne ko kuma fira ko meeting haka, kamar idan wanda ba ɗan kamfaninba ya zo ganinka zaku iya tsayawa a can ku yi firarku” Ya ƙarasa yana nunnuna min guraren, ni kan sai bawa idona abincin na ke, gaba ɗaya na zama baƙauya sam ba zaka taɓa cewa Nawwara ce wacce ta taɓa zama a London ba, ko da yake shekaru da yawa yanzu na zama baƙauya. Ƙofa biyu ce a gurin ko wacce ƙatowa, ɗaya a dama ɗaya a hagu mutane na ga suna ta shiga da damar masu fitowa kuma na fita ta hagun, muna ƙarasawa sai ƙofar ta buɗe mana da kanta a ƙasan gurin inda mutun zai ɗora ƙafarsa an rubuta WELCOME ɗa manyan haruffa masu ƙyali. Tsaye na yi ina kallon yadda mutane ke zirga-zirga ba dan ina tare da Bilal ba dan zan iya rantsewa wata ƙaramar duniya ce na shigo, kamin ka shigo fuskar kamfanin duk madubi ce cikinsa kuma komai kamar zinari yake, ga wasu manya-manyan plasma da ke tallata abubuwan da kamfanin ke yi. Reception ne ke facing ɗin duk wanda ya shigo, ma'aikatan gurin na sanye da suit maza da mata. a dama da Reception ɗin manya lifted ne guda huɗu, a hagu kuma Excavator ne babban guda biyu na hawa da kuma na sauka, a can gefe kuma wani ƙaton guri ne mai kamar falo an jera ƙasaitatun kujeru ga plasma a gurin, ko ina security camera ne a gurin, ac ta ko'ina ratsa jikin mutum ya ke. “Nawancy...” Kiran da Bilal ya yi min ne ya dawo da ni hankalina, har na kalli inda ya dosa, na rufa masa baya da sauri. lifted da ke farko ya danna, sai da muka yi tsayin minti biyu zuwa uku sannan ta buɗe mutun uku daga cikin lifted suka fito sannan muka shiga, bayan mun shiga muka juyo muna fuskantar ƙofar sai ya kai hannunsa a maɓallan da ke gurin ya danna number four, sai lifted ta rufe. “Wow...” Na furta ina lumshe ido. Sai kawai Bilal yasa min dariya, har da ciro wayarsa yana ƙoƙarin min video. Lokacin da lifted ta buɗe mun tarar wasu na jiran mu fito ta su shiga. A nan na ma ashe wata duniyar ce, da komai na ta na glass ne, mutane sun kasu kashi-kashi, wasu na ta aikin akan documents wasu na gaban computer. “Haka aikin na ku ya ke?” “Yeah nan na masu diploma ne, kin san mu NCE ne da mu muna hawa na biyu” Yana min maganar muna cigaba da tafiya har muka isa wani ƙofar wacce kana tsinkayar wanda ke ciki shi ma kuma yana tsinkayarka. Buɗe min yayi na shiga sannan shi ma ya shiga ya nuna min gurin zama, yana mikawa wanda ke gaban conputer hannu su gaisa. “Manir” “Ya Bil ya aikin?” “Ba daɗi, ga baƙuwar da na ce maka zata kawo takardunta” Wanda aka kira da Manir ɗin ya juyo yana min wani kallo baki a sake. “Wow Welcome Ma'am, gaskiya tana da kyau sosai gata fara mashallah” Bilal ya shafa yancinsa yana satar kallona fuskarsa ɗauke da murmushi, yanayin yadda Manir ɗin ya yi min ya karantar da ni kamar akwai abunda Bilal ɗin ya ce masa a kaina. “Sannu ya aiki?” “Hooooo i beg see golden eyes” Ya furta yana ba Bilal hannu su taɓe. Na yi ma Bilal wani kallo da shi kansa ya san ba na lafiya ba ne, sai kawai ya miƙa hannu ya karɓi takardun hannuna ya miƙa masa. “Gashi ka shigar da bayanan mu zamu wuce” Ya miƙa hannu ya karɓa yana dariya. “Okay ba matsala, Allah ya sanya alheri ya tsare, perfect match” Har na buɗe baki na ce wani abu sai Bilal ya yi saurin buɗe ƙofar. “Muje Nawancy” A dole tasa na miƙe tsaye na nufi ƙofa, ƙamin na ƙarasa sai yayi saurin tare ni. “Sorry Nawancy bari Oga ya wuce” “Wane Oga?” “Mai kamfanin” Jin hakan yasa ni miƙa wuya dan na hango mai tarin wannan dukiyar, sai dai ban yi sa'ar ba dan har ya shige Lifted. A nan Bilal ya ba ni hanya na fito muka jera muka nufi lifted da muka shigo ɗazu, ƙashim turaren da na ji ya sani faɗuwar gaban da har ya haddasa min ciwon kai a take, saboda na tsani wannan ƙamshin kamar yadda na tsani mutuwa, jin sunan turaren kaɗai zai iya haddasa min hawan jini saboda tunawa da mai shi. “Wannan da ya wuce ogan mu ne, mahaifinsa ne ke da wannan kamfanin, shi baya son idan na zo a lifted kai ma ka zo, sai dai kowa ya ja baya har sai ya zaɓi wacce zai shiga idan ya shiga sannan kowa ya shiga, kuma baya son yaga mutun ba a gurin aikinsa ba, abu kaɗan kan iya sakawa ya ƙoreka aiki, ba shi baya ɗaukar ƙaddara idan kika fasa masa kofi sai an cire cikin albashinki, ba a latti zuwa gurin aiki, minti ɗaya kika ƙara daga lokacin da kike zuwa aiki sai an rubuta, da kin yi haka sau goma sha biyu zai koreki, idan wata matsalar ta same ki sai kin faɗi dan wuri ki rubuta takardarki ki aika idan ba haka ba zai koreki” “Kai amman ya cika tsauri, sai kace turai” “Gashi ba shi da dariya, kuma baya son kallo” Na haɗe yawu ina jijina lamarinsa, domin nima kaina bana son kallo. Ya cigaba da ba ni labarin kamfanin da kuma yadda suke abubuwansu har muka iso bakin ti-ti. “Kamfani da ke saffara duk wani abu da shafi ƙarfe, kuma kamfani da ke siye da sai da hannu jari, ga kwangiloli kala-kala kamfanin yana yi, kuma akwai wasu ƙananan kamfaninni da suke ƙarƙashin kulawarsa” “Ayyah za su ɗauke ni aiki kuwa?” “Za su ɗauke ki kan, amman sai kin yi haƙuri da kuma kin jure ba a makara ba a ɗauke ƙafa, kuma ba a kuskure” “I will try” Sama-sama yake ta labarta min abubuwan akan kamfanin, kamin ya tarar min Napep, ya faɗa masa inda zai kai ni, ya miƙa masa dari biyar ya ce ya bani ragowar canji. Ni kan jikina har rawa yake na

Table of Contents

Chapters

119 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});