Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 117

Chapter 117

Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel 1,198 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

fadin. “Rufe idonki” “Mi zaka bani?” “Just close your eyes please” Mikewa tayi tsaye ta soma zagayensa ita ala dole sai ta ga abunda ya shigo da shi shi kuma ya rika juya hannayesa ta kasa ganin a dole ta hakura ta rufe idanuwanta. “To na rufe” “Ban yarda da wannan rufewan ba, juya bayanki” Ba musu ta juya baya, zuciyarta cike da zumudin son ganin abunda yake boye mata. Da sauri ya juya ya koma gurin kofar ya bude musu suka shigo da kayan da suke dauke da su suka dora saman center table sannan suka fice da sauri, har lokacin Nawwara bata juyo ba duk ta tana jin kamar motin abu a bayanta. “Juyo ki bude idonki” Juyowa tayi sai dai bata bude idon ba, har sai da ya sake fadin ta bude idonta. A hankali ta soma bude idon sai idanuwanta suka sauka kansa. Still har yanzu hannayensa suna bayansa da alama akwai abunda yake cigaba da boyewa. “Minene tau?” Ya nuna mata tsakiyar falon inda center table yake, what a surprise katon cake ne a saman teburi an rubuta masa HAPPY BIRTHDAY MY PRINCESS, da mayan haruffa da sauri ta doshi gurin tana kallon cake din cike da excitement. Katuwar farar paper da ke gefen cake din da aka kawata da flowers da masu harufa an rubuta FOR MY LOVELY WIFE, ta kai hannu ta dauka ta bude jikinta ya rawa ta soma karantawa. _Happy birthday to someone close to me, today my queen was born, the queen of queens, how can I forget your birthday Queen? The woman whos make feel better person, she's stay by my side i learned many things about life and love, she's the only woman i love and i know lucky is the man who is the first love of a woman, but luckier is the woman who is the last love of a man, you got it all Baby, I loves you yesterday. I love you still. I always have .. I always will. Happy birthday to you my heart_ Dagowa ta yi ta kalleshi idanuwanta cike da kwalla. “My soul i love you so much” Hannunta ya kama ya saka mata zoben da ke hannunsa mai alphabet din NJ. “Happy birthday Princess” “Thank you, ni na manta da yau ne birthday na ma” Ta kwantar da kanta jikinsa tana hawaye. “Ni kan ba zan manta ba, taya zan manta birthday din babbar mace kamar wannan? Matar da ita farincikina mace da ta zame min RAI BIYU, kuma muka zama RAI BIYU ni da ita” Ta yi farincikin da abunda ya yi mata har bata iya misalta jindadinta, haka yake mata a ko da yaushe yana surprising dinta da abunda zai sata farincikin ko ya kara mata son sa a zuciyarta. A ranar farinciki ya hana Nawwara bachi kamar yadda yake hanata a duk lokaci da wani abun farinciki ya same ta, baya da bukatar godiyarta domin yana tunanin duk wata hanya da zata gode masa ta yi masa yawa, shine ya kamata ace yana gode mata ko dan canjin rayuwar da ya samu. *** *** *** BAYAN WASU SHEKARU..... Rayuwa ta canja mana, lallai dukan abunda Allah ya rubuta zai samu bawa babu makawa sai ya sameshi, lokuta da dama muna son abu sai ya zamo ba alheri ba ne a garemu wani lokacin kuma mukan ki abu kuma ya zama shine alheri a garemu, shiyasa ka bawa Allah zabi shine abunda ya fi domin shi zai zaba maka dukan abunda zai zama alheri a gareka ko kuwa kai kana ganin kamar ba alherin ba ne. Kaddara data rubuta cewar ni matar Jibril ce a karo na biyu ita ce ta sake rubuta min farincikina da jindadi a gidansa, abunda ko da a mafarki aka cemin zan yi rayuwar jindadi da farinciki a gidan Jibril ba zan yarda ba amman yau gashi ina ganin kamar ma nafi kowa ce mace dace da mijin aure, you deserved happiness shine a abunda yake yawan fada min kuma yake ta kokari wajen ganin ya faranta min a rayuwata. Lallai Jibril bango ne shafi kuma jigo a rayuwata majinginata mai share hawayena a duk lokacin da kuka ya tunkaroni. Bayan yankewa Siraj da abokan ta-addacinsa hukuncin daurin rai da rai a gidan kaso bamu da sauran fargaba ni da Jibril, ba ma kamar yanzu da hankalina ya kwanta sosai ganin cewar Zinatu ta yi aure, macen da take barazana ga rayuwata da kuma ta miji, irin rayuwar da nake a gidan mijina rayuwace da ko wace mace mai aure zata so kasancewa a cikinta, domin kuwa Jibril yana sani na manta da damuwata a duk wani fargaba da yake tare da ni, a da na yi tunanin rasa Yar'uwata Habiba da na yi da kuma Mahaifina farinciki ba zai sake ziyarta ta, ashe shirme na ke ta yi Allah ya tsara min wani jindadi da farinciki a gidan Jibril. Wani lokacin na yi dariya idan na tuna irin kiyayyar da na nuna masa ko kuma na ce irin soyayyar da na yi da Bilal wacce na ke ganin kamar idan babu shi babu farinciki a rayuwata, lallai yan karon magana sun yi gaskiya da suka ce karshen kiyayya soyayya domin kuwa ni da Jibril a yanzu kamar mu hade junanmu muke wa ma zai ganmu a yanzu ya zaci mun taba wata rayuwar ta bakinciki da kiyayyar juna. Lokuta da dama na kanyi ma Allah godiya akan zabin da yayi min na auren Jibril sama da Bilal domin kuwa a yanzu na gane irin tazarar dake tsakaminsu da kuma irin rayuwar farinciki da jindadi da Bilal yake ciki, domin shi ma na samu labarin irin rayuwar jindadin da yake da matarsa tun bayan da kama aiki a kamfanin hakar man fetur na dangote dake Lagos, wata kila da ni ya aura da mahaifiyarsa ba ta barmu munyi zaman aure kamar yadda ta barshi yana zaune da matarsa a yanxu ba. Na kanyi kokarin taimakawa a duk gurin da na ana bukatar taimako domin kuwa a yanxu na fahinci yadda rashi yake da kuma shiga halin rayuwa, duk a yanxu muna cikin ni'imar Allah Al-hamdulillah. Inna ma a yanxu ba zaka ganta ka ce ita ba ce, domin sun tare da sabon gidan da Jibril ya siya musu, duk wani wulakanci da halin ko inkula da familyn suke nuna mana a yanzu ya wuce mu ne kan gaba a komai, ashe daman rashin yake sa ake wulakanta mu kamar marar galihu. Bayan Haihuwar Nana Asma'u wato yata ta biyu da take bin Noor na sake haibuwar Bashir wanda na kira da Babana, sai kuma na sake haihuwar Fatima da Aisha, a duk lokacin da muka samu hutu mu kan kwashesu muje hutu Abuja. Idan kuma muna sokoto ranakun Assabar da Lahadi sai na sa direba ya kaisu gurin Inna a can suke hutun sati, har bana son su dawo saboda hayaniyarsu. A ranar da muka samu hutun karshen shekara nasa ya kaimu Katsina gurin Hajiya Aisha wato matar margayi Alhaji Dahiru, ta yi mamakin ganinmu kamar yadda na yi mamakin halin da na sameta a cikin, da bakinta take fada min, zaman abuja ya gagareta saboda gadon da Alhaji ya bar masu ta

Table of Contents

Chapters

119 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});