Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 75

Chapter 75

Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel 1,197 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

idanuwansa suka cika da kwalla kamar ba namiji ba, be ankaro da nauyin da kafafunsa suka yi ba har sai da ya daga kafarsa daya ya taka zuwa gurin gadon da Noor yake kwance. Sama yake kasa yake duniya yake lahira yake? Sai ya kasa ganewa iyakar abunda idanuwansa suke kallo kamaninsa dake zuba a fuskar Noor, yasan ba mafarki yake ba kuma idanuwan ba gizo kuke masa ba, abunda yake gani zahiri dake shiga har cikin kwakwalwarsa, faduwa ya yi a gurin yana kuka muryarsa na karkarwa. “This is my Son, ba ko tantama wannan da na ne, he's my Son jinina da na na cikina” Hannu ya kai zai shafa fuskarsa da ke manne da bandeji sai yaji ya rike masa hannun cak.... ____________________________ GOOD NIGHT HABIBATIES 😘😍 Duk Inda Masoyan RAI BIYU Suke Ina Gaishesu Ina Muku SON SO FISABILILLAH ❤ Na yi Wannan guntun Page din ne saboda ku 😍😘 *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @KhadeejaCandy 4⃣3⃣ Dago kai ya yi da sauri domin ganin wanda ya hana hamnunsa zuwa ga gudan jininsa, ganin Nawwara cikin bachin rai da daure fuska yasa shi mikewa tsaye sai ya kama duka hannayensa biyu yana kuka kamar zai narke a gurin. “Naw.....” Fisge hannayenta ta yi ta ture da dukan karfinta. “Karka kuskura ka taba min ɗa, hauka ta daina dibanka kana taba jikina ni ba halalinka ba ce” Ta fada cikin wani irin zafin rai. Doc Ismail ya karasa ya rika Jibril yana kallon Nawwara tare da fadin “Amman ke baki da mutunci ta ya zaki wulakanta babban mutum kamar Jibril a gaban mutane” “Babu ruwanka karka saka min baki a nan” Jibril ya share hawayen da suka ki tsaya masa ya nufi gurin Noor sai ta tsaya masa tsawa hawaye na zuba a idanuwanta. “Karka taba min yaro” Rike shi Doc Ismail ya yi ya ce da Nurses din su wuce da Noor, a gurin Nawwara ta zube kasa saboda jirin da ya dibeta, Doc Ismail ne ya kira wasu Nurse suka kamata suka mayar da kin da ta baro. Hakan ya bawa Jibril damar shiga dakin da aka kai Noor. Ko da ya shiga ya samu Nurses din suna daurashi saman gadon sannan suka saka masa robar jini daya. Fita suka yi daga dakin baya sun gama komai sai Jibril ya karasa inda yake ya durkusa kasan guiwowinsa gurin gadon wasu sabbin hawaye suna zubo masa. Ko da bachi yake ya farka ya kalli Noor yasan dan sa ne, fuskarsa ce shinfide a fuskar Noor babu inda Noor ya rage shi da komai, hannu ya kai ya rika hannun Noor sai yaji wani irinsa ya shiga hannunsa jini ya hadu da jini Noor din ma da be san inda hankalinsa yake ba sai da ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi. Kuka Sosai jibril ke yi irin kukan da aka san mata da yinsa, sai kuma yaja hannun Noor ya kai a fuskarsa ya lumshe ido, yana ta goga hannun a fuskarsa, sannan ya yi masa kiss sai kuma ya soma shinshinar hannun kamar zai cinyeshi. “Am sorry Son, ka yafe min na wulakanta akan haukana, mahaifinka ya tuba ya gane kuskurensa na yi nadama, ban san miya shiga kaina ba ban san miyasa na aikata ba, am really sorry for what i did, please forgive me” Ya kara fashewa da kuka har numfashinsa na son tsayawa, shigowar Doc Ismail ne yasa shi tsagaita kukan ya dago ya kalleshi. “Wai miyake faruwa ne? Miye alakar ka da wacan matar ne? Na san dai wannan ba dan ka ba ne ko?” Tambayar da Doc Ismail ya yi masa kenan. “Dana ne, ita kuma mata ce” Daga haka Doc Ismail be kara cewa komai ba, yasan Jibril baya cikin yanayin da zai iya yi masa bayanin komai a yanzu, after that be kama ya saka kanshi akan matsalar iyali ba. Juyawa ya yi ya fice zuciyarsa cike da mamaki bakinsa kuma gumde da tambayoyi. NAWWARA POV. Ban san iya awanin da na dauka a sume ma ba, ina farkowa na ji goshina ya cika da nauyi har bana iya gani sosai. “Sannu” Muryar Inna ce take gaisheni sai na gyada mata kai dan bana iya magana a wannan lokacin, na dade ina kallon silin sannan idanuwana suka dawo daidai har ya kalleta. “Ina Noor?” “Yana can an kaishi wani dakin” Sai a yanzu na tuno da abunda ya faru, ashe fa wannan suma ta biyu ce na yi. “Inna miyasa kike bari Jibril ya zo har ya ga Noor” “Ba zan iya ce miki ga dalilin zuwansa ba, ban kuma san ta ina ya ji ba, nima na tafi neman jini ko da na dawo na tarar ya bada jininsa kuma ya sa an canja miki daki an dawo da ke a nan, shi kuma yasa aka kai shi dakunen nan masu tsada” Na yi sauri sauka saman gado duk da ina jin jikina kamar babu gwari sosai. na fita daga dakin na mike hanya har na isa manyan dakunan, na bude na farko ba shi bane na biyu ma haka na uku hudu biyar haka na bi dakunan sai da na kai daki na bakwai ina turawa sai na hango Noor kwance Jibril kuma zaune saman kujera ya dora kansa gurin jikin Noor hannun Noor kuma a saman kansa dayan hannunsa kuma na sanye cikin na Jibril. Ban damu da na rufe kofar ba na karasa kusa da gadon cike da tausayin halin da Noor yake ciki, ina tsayawa dai dai kan Jibril sai ya bude idanuwansa da suka kumbura suka ja a hankali ya kalleni, sai kuma ya lumshe. “Jibril tashi ka fita” Na fada a tsawace, sai ya bude ido ya yi ma hannun Noor kiss sai ya sake shi, na yi zaton tsaye zai tashi sai kawai na ga ya zube kasan gwuiwowinsa ya fashe da kuka yana hade hannayensa. “Ki dubi girman Allah Nawwara, ki sassautawa zuciyarki dan Allah ki yafe min, Wallahi na canja dabi'u da halayya duka na canja ki ceci raina kuma ki ceci ran yarona ki taimakeni ki yafe min ba ni da wani buri da ya wuce na ki da na wannan dan nawa, please Nawwara for the sake of our Son ki hakura mu sake sabuwar rayuwa, zuciyata na cike da kuna ina bakincikin abunda na yi muku, kaina a kasa yake ki taimaka min ki bani damar da zan gyara laifina, ba ni buri sai na ki, ki min masauki a gefen zuciyarki dan Allah Nawwara” Hawaye na zuba a idanuwansa yake min wannan rokon da ya soma karyar da zuciyata, nima na fara hawaye. “Bata lokacinka kawai kake Jibril, ka fitar da ni a ranka ka manta da ni a duniyarka, kai ba tsarata ba ne, na rumtse ido daga kallo duk wani abu da ya shafi rayuwata” “Ji ceci rai Nawwara, idan yanzu na fadi na mutu ke ce sila, ki taimaka ko dan dan mu” “Dan mu? Ko da na? Dan da ka ce ba naka ba ne? Ka wulakanta ni saboda cikinsa? Dan da tun da ka turo ni gidanmu ba ka taba saka kafarka ka zo duba shi ba? Dan da baka san cin sa ba baka san shansa ba? Dan da baka san

Table of Contents

Chapters

119 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});