Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 53

Chapter 53

Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ɗaya ba shi da kyau Ya Mustapha domin idan mace da Namiji suka kasance su kaɗai suka kaɗaice to sheɗan ne na ukunsu, amman wannan be taɓa zuwa a ran Momy ba balle kuma kai da ace hankali ko kuma sha'awarka ta kwaɗaita maka ni da yanzu ka gama da ni kuma ba za ayi komai ba saboda kai ɗan gata ne. Ka misalta kanka Ya Mustapha da ace kana aikata zina da wannan yarinyar ne Allah ya karɓi ranka mai zaka faɗawa Ubangijinka? Kamar kaina da bawa ka ce karya aikata abu kaza wata rana sai ka sameshi da tsabama Umarninka har ma ya yi maka sata kuma ka kamashi dumu-dumi wane irin hukunci zaka yanke masa?” Tun da ta fara maganar jikinsa ya yi sanyi hankalinsa ya tashi tun da yake a rayuwarsa babu wanda ya taɓa tsayawa ya faɗa masa gaskiya kamar Ikram, yana sauraren wa'azi amman be taɓa natsuwa ya yi aiki da shi ba. Hawaye yake hawayen da ke nuna nadama da tashin hankalin da ke fuskarsa. “Miyasa baki faɗa min wannan ba tuntuni? Da kin tunatar da ni da yanzu ban faɗa wannan halin ba” “Ko da na faɗa maka zaka faɗa saboda ƙaddaraka ce a haka, kuma a lokacin na san ba zaka saurareni ba saboda ba zaka taɓa ganin munin abunda kake aikatawa ba, ban ga sha'awa ga abincin da zan wanke hannu na ci ba wani yazo hannunsa da datti ya ci wani ma yazo hannunsa da datti yasa ya ci ni kuma na zo na sake saka hannu na ci, sam babu kishi kuma babu imani ga duk mutumen da yake aikata Zina, ban san miye daɗinta ba balle kuma ribarta, saboda yawan mata da kuma yawan wasu ɗabi'u na ɗan adam Allah ya halattawa maza auri mace sama da ɗaya amman kai kaba ma yi auren ba ka faɗa a zina kana neman hallaka kanka, a wannan halin da ka shiga a yanzu ina tunanin shiriyarka ne yazo, dan haka ka yi ta istigifari kana neman Allah ya yafe maka abunda ka aikaka kuma ka yi ma Allah alƙwarin ba zaka taɓa komawa a cikin wacan ƙazamin halin ba, ka yi ta aikata dik wani abin da ka san zai kusantar da kai ga Ubangijinka” Ya gyaɗa mata kai alamar gamsuwa. “Amman Nawwara ba zata yafe min ba ko?” “Zata yafe maka matuƙar kana kyautata mata, kuma kan tuba tuban gaske sai Allah ya dafa maka ta yafe maka har ma ta so ka idan ƙaddarar sonka yana cikin ƙaddararta” “Idan kuma so na baya cikin ƙaddararta fa?” A hankali ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce. “Zai iya zama son ka yana cikin tawa ƙaddarar...!” Da sauri ya miƙe tsaye ya share hawayensa daman tun ba yau ya lura da take-taken Ikram da ke nuna alamar tana son shi. “Ki ɗauki abincin idan na fita waje zan ci, na gode sosai Sis” Yana faɗar hakan ya nufi banɗakinsa dake cikin ɗakin, murmushi ta yi murmushin da ke nuna rashin jindaɗinta sannan ta kwashe kayan ta fice. bayan ya fito wankan ya ɗauki wayarsa ya nemo number Jidda bugu uku ta ɗaga muryar a sake har wani zaƙi take ƙara mata. “Hello Mustapha” “Ya kike?” “Lafiya ƙalau” “Kina gida?” “Ee ina gida lafiya?” “Lafiya ƙalau, kawai ina son ganinki ne akwai wata magana mai muhimmanci da na ke son mu yi da ke idan babu takurawa kuma idan kina free” “Aiko bana free dole zan samu time dominka, faɗa min yaushe zaka zo i mean time?” “Yanzu nan gani nan har na yi wanka” “Okay sai ka shigo” Yana aje wayar ya nufi gurin da tufafinsa suke ya buɗe, cikin ƙanƙanen lokaci ya shirya cikin manyan tufafi riga da wando na shadda, sannan ya fito ya nufi gurin motarsa ya shiga sai ƙofar gidansu Jidda. Waya ya buga mata sai gata ta fito ba ɓata lokaci fuskarta ɗauke da kwalliya sai ƙamshin turare take kamar sabuwar amarya, motar ta buɗe ta shiga kasancewar be fito ba ne yana daga ciki zaune. Front seat ta zauna tana ƙara miƙa masa gaisuwa ciki kashe murya fuskarta ɗauke da murmushi, bayan sun gaisa ya koro mata da bayanin da ke tafe da shi. “Jidda ko kin san wanda yake da gidansu Nawwara da suke haya?” “Ee Malam Haruna ne yana nan gaba da su kaɗan, ya aka yi?” “Na je gurinta ne sai take zargin ko nine na siye gida na saboda ance an siye gidan” “Haka nima na ji amman ban san waya siye ba” “Ai nasan Malam Haruna zan masa magana na ji wanda ya siya sai ya fansar min. Am Jidda ina son ki faɗa min duk wani abu da Nawwara take so da wanda bata so da kuma taimaka min akan duk wani abu da zai ƙara kusancina da ita na san ke zaki iya daboda kinfi kowa saninta” Ta kalleshi Jiki a sanyaye. “Saboda me?” “Saboda ina ƙaunarta son ta na ke Jidda wannan dalilin yasa na ƙulla abota da ke” Tafiyar daƙiƙu biyar zuwa shida numfashinta ya yi sannan ya dawo jikinta har ta iya jiyo bayanin da Mustapha yake koro mata. Be ɓoye mata komai ba daga irin son da yake yi ma Nawwara da kuma abunda ya aikatawa Habiba, ko da ya ƙarasa bata labarin kuka yake sosai kamar ƙaramin yaro. Lumshe ido ta yi ta haɗeye yawu sai hawaye suka sauko mata, hawayen da ita kanta ba san na minene ba na tausayin Habiba ko Nawwara ko kuma kanta ko Mustapha, wani baƙon al'amari ya ziyarceta labarin ya zo mata banbaragwai domin Nawwara bata taɓa labarta mata wannan ba, sai dai yanzu ne ta gano dalilin tsanar da Nawwara take yi ma Mustapha. “Please help me...” Ya faɗa cikin muryar kuka. Sai ta kalleshi tana kukan kamar yadda shi ma yake yi. “Zan yi tunani akwai, ina da buƙatar natsuwa bana iya banbance komai a yanzu” Tana faɗar hakan ta buɗe motar ta fita ta shiga gida da sauri tana kuka. Ya kusan minti talatin sannan ya bar ƙofar gidan zuciyarsa na mugun ƙona ya nufi gidan Malam Haruna. *** *** *** Anya zan iya aiki tare da Jibril kuwa? Mutumen da ya wulaƙanta ni zan iya bashi wannan damar ta kusanci da ni? Yes zaki iya, ga dukan alamu ya gane kuskurensa yanzu kan ya san ƙimarki tun da har zaki maresa a gaban jama'a ya ƙyaleki, yanzu ne ya fi dacewa ki nuna ko wacece ke, yana da kyau yasan ba wacan Nawwarar ba ce this is the time da zaki rana abunda ya yi miki kuma the same time da zaki nunawa Bilal son gaskiya kike masa, kuma idan har ban yi aiki da shi ba na gallaza masa hakan zai bashi damar da zai riƙa bibiya ni da familyna. Da wannan tunanin na tashi yau ina ta son tsayarda matsaya ɗaya akan na yi ko kar na yi. Su Sakina sun kama hanyar makaranta Inna kuma na bachinta kamar yadda ta fara dabuwa kanta a yanzu da bachin rana, ni kuma na fito na gyara tsakar gidan na yi wanka sai na shirya cikin koriyar atamfata ta roba, jin na yi bana ƙaunar zama gidan dan haka na saka

Table of Contents

Chapters

119 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});