Chapter 76
Chapter 76
ya rayuwarsa ta ke ciki ba? Dan da ka kasa yankawa ragon suna kasa a ka kirashi da shege? Mahaifina shi ya yanka masa rago ya saka masa suna, yanzu har kana da bakin da zaka kira shi da danka? Kana da idon da zaka zo rana tsaka ka kalleshi kuma ka fada masa kai ne mahaifinsa? Ta wace fuskar zai kalleka? Taya zai kiraka Uba?” Tun da na soma magana ya rumtse ido ya matse hannayensa da ke hade guri daya yana cizo baki, da alama maganar tawa bata masa dadi, sai kuma ya dago fuskarsa da ta yi ja ya kalleni. “Fada min abunda zan yi wanda zai sa ki yafe min, fada min tafarkin da zan bi Noor ya karbe ni a matsayin ubansa? Taimakeni Nawwara, ki tausayawa rayuwata zan yi komai kike so am ready to die for you” “Ka wuce sanina Jibril, kaje ka nemi matar da zata so ka ta aureka ta haifa maka yaya, shawara daya zan baka kaje ka yi abunda zai taimaki rayuwarka ina maka fatar samun irin matar da kake so Allah baka sa'a” Mikewa ya yi tsaye ya fice cike da nauyin kafafu, ba tare da ya share hawayen da ke fuskarsa ba. Ni kuma na zauna kusa da dana ina kukan da ban san na minene ba, tausayin da na ko kuma rayuwar da na cinci kaina a ciki.? Bayan sallah isha'i Jidda da mahaifiyarta suka zo duba Noor, daman tun da magariba wasu daga cikin mutanen babban gida suka zo duba shi. Bayan fitarsu sai ga Bilal ya shigo hannayensa da ledoji har gudu hudu har kuma lokacin Noor be farka ba gaba daya hankakina ya tashi duk da likitan ya fada min zai dauki tsawon lokaci yana bachin. Kallo daya na yi ma Bilal na kawar da fuskata, bana ganin komai sai wacan abun da ya faru shekaranjiya wani irin kishi da bakinciki sai suka taro min har na ji kamar na dauki wukar da aka aje ta yanka lemu na daba masa a kirji. Da Inna ya fara gaisawa sannan ya gaishe da wata abokiyar Inna suka gaisa da Sakina, sai duk suka tashi suka ba mu guri, daya ya zama daga ni sai shi sai kuma Noor da baya cikin hayyacinsa. “Nawancy... Wallahi ba abunda kike tunani ba... ” Hannu na daga masa “Kai ko Zinatu ko wani abu da ya shafi rayuwarku a yanzu be dame ni ba” “I know i shouldn't, ya jikin Noor?” “Da sauki” “Allah ya kara sauki” “Amin” Bayan wannan bata maganar bata sake shiga tsakanin mu, da ya gaji da zama ne ya mike tsaye ya karasa kusa a Noor cike da nuna kulawa ya duba shi sannan ya kalleni ya ce “An kama wadanda ya kade sa?” “Ya gudu, amman mutane sun ce da gangan mutumen ya yi cikinsa da mota ya kadesa, kuma likitan ya ce min Noor ya karye a hannu” Na fada ina fashewa da kuka. “Sorry a wani waje ne?” “Sun taso makaranta ne, mutunen ya gudu” “Amman Mahaifinaa ya sani?” Wani kallo na watsa masa na sakar masa idanuwana ina ta kallon fuskarsa cike da tsanar furucinsa. “I mean Jibril” “Kaima kana cikin mutanen da je ganin laifina akan Jibril ko?” Yayi saurin komawa ya zauna. “No ba hakan na ke nufi ba, Jibril ya wulakanta ki Nawancy kuma ya cancanci ko wane irin sakamako daga gareki, Wallahi ko ke ce baki da gaskiya i will support you ballantama kina da gaskiya, kawai bana son abubuwa su miki yawa ne, tunani a yanzu ba na ki ba ne, ki sassautawa zuciyarki, kuma ki rika neman shawara akan abunda ya shige miki duhu” Na share hawayena na maida idanuwana gurin da na, sai na cinkayo muryarsa yana fadin. “Ni kaina ban san ranar birthday dina yayi ba, sai a Facebook, su suka turo Zinatu kuma friend dita ce a fb few weeks ago ta turo min friend request na yi accepting ba tare da tunanin komai ba, ta yi min happy birthday tun ana saura kwana daya na yi birthday na, ina tunanin ta nan ta gane xan yi birthday a ranar har ta siyo wannan cake din, ina zaune ta shigo da shi ta kira abokan aikina ban ma san ta kira ki ba sai da na ganki office din” “Mi zai sa ta yi haka? Daman can tana son ka?” “Gaisuwa bata taba shiga tsakanin da Zinatu ba, idan har kiga na mun hadu sai idan aiki zamu yi, ina tunanin ta yi hakan ne saboda ta shiga tsakaninmu ko kuma...” Sai ya yi shiru be karasa ba. “Ko kuma me? Jibril ne ya sata ko? Zai iya saboda mugu ne” “Ni dai iya abunda na ke son ki sani, ba zan taba cin amanarki ba” “Amman miyasa ka yi blocking din number ta? Kuma ina ta tura maka sako baka min reply” “Saboda na baki damar yin tunani da zuciyarki, ina ganin kamar ina kan hanyar da ba zata bulle ba ne, zuwan Jibril a karo na biyu cikin rayuwarki ya karyamin kuzari, bana son na shiga tsakanin farincikinki da kuma tunaninki, bana son na yi abunda zai raba hankalinki gida biyu, na yi hakan ne saboda na daga miki kafa kuma na samawa rayuwata mafita saboda bana so na rasa a take, zuciyata na raya min kamar ba zan aureki ba Nawancy, kin ki bani damar da zan ga magabatanki kuma gashi Jibril zai yi duk abunda zai yi wajen ganin ya mallakeki” Tausayinsa ya kamani, duk da kasancewar ni ma ina tausayin kaina. “Kokarin mallakata yake Bilal kai kuma tuni ka malleke zuciyata, idan har Nawwara bata auri Bilal ba to ban cancanci auren ko wane irin namiji ba a duniyar nan, na fara rayuwa sau daya sai kuma na mutu, kai ne ka dawo da ni duniyar da mutane suke rayuwa, ka yi nasarar canjani daga mutum mutume zuwa mutum wacce ta san mi ake nufi da rayuwa, na rayu a lokacin da rayuwa take da muhimmanci a gareni, sai Jibril ya kashe min ruhi kuma ya kona shi ya maidashi toka ya shekarda da shi ya bi iska, kai ne mutumen da ka hada tokar ruhina ka tattarata ta sake zama cikakken ruhi na maida shi a cikina, har zuciya ta bude ta kamu da son ka. Kai ne kadai mutumen da nake so Bilal kai ne mafarkina, burina idan har ka ga ban aureka ba ka tabbatar gawata ce ta ke magana ba ni ba” Lumshe ido ya yi ya hade yawu sannan ya bude kamar dai be yarda da ni ba, sai ya mike tsaye yana fadin. “Idan kina bukatar wani abun ki fada min, ko ki kirani, ina son ki san da wannan Nawancy ina sonki sosai ina kaunarki kauna ta hakika” Da kallo na bishi har ya fice, sannan na juyo ina share hawayena na kalli Noor da ke motsi. _______________________________ I dedicate this chapter to my wattpad people 😘😘😘 *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @KhadeejaCandy 4⃣4⃣ Bayan fitar Bilal su Inna suka shigo tare da Mama Turai wato Yayar Inna wacce suke uwa daya uba daya. Inna ta zauna saman tabarma ita kuma ta zauna saman kujerar da ke gefen gadon ta Kalli
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119