Chapter 101
Chapter 101
ce ta fada min komai idan bata fada min ba babu yadda za ayi na sani” Wayarsa ya dauko ya kira Rabi tana dauka ya ce. “Duk inda kike ki zo ki same ni yanzu nan gidansu Nawwara” Be tsaya jiran abunda zata ce ba ya kashe wayar ya kira Siraj. “Siraj ka zo nan gidansu Nawwara gani nan na iso” Nan ma kashe wayar yayi sannan ya kalli Nawwara. “Siraj ba zai min haka ba, babu dalilin da zai sa Siraj ya sace Noor” “Wallahi da gaske nake Siraj ne ya sace shi” Siraj ya riga Rabi isowa duk da kasancewar ta fishi kusa da unguwarsu Nawwara, bayan ya shigo cikin gidan ne sannan Rabi ta iso, Nawwara na ganinsu ta mike tsaye tana hawaye “Rabi fada masa gaskiya fada masa abunda kika fada min akan Siraj” Rabi ta nuna kanta. “Ni Kuma? Mina fada miki ne?” Nawwara ta girgiza kai. “Karki min haka dan Allah ki fadi gaskiya” “Gaskiyar me zan fada? Ni ban san komai akai ba” Inna ta matso kusa tana kallon Rabi da mamaki ta ce “Yar nan ki ji tsoron Allah ki fada gaskiya, ke fa kika sami Nawwara a cikin gidan a nan kika fada mata cewar Siraj so yake ya kashe Jibril da ita kuma shi ya kade Noor” “Haba Inna da girmanki be kamata ki yi wannan maganar ba, bata dace da ke ba, ni gaskiya ban san komai a kai ba” Jibril ya kalleta “Look Rabi ki fada mana gaskiya” “Sir Jibril ban san komai a kai ba, idan ma wani abun ne ai kai zan sama na fadawa gaskiya ba Nawwara ba” Faduwa Nawwara ta yi kasa tana kuka da tureturen kasa kamar mai aljanu, hakan yasa Jibril zargin tana kokarin fita hayyacinta ne. Sai ya kalli Siraj “Siraj yi hakuri dan Allah ka je gida yanzu zamu kaita asibiti Rabi ku wuce kawai” Siraj da tuni gumi ya gama keto masa ya juyo a firgice ya fice, sannan Rabi ita ta fice hankalinta sam baya jikinta. Sai Dsp nan ya kira Jibril gefe yana tambayarshi alakar da shi tsakaninsa da Siraj, Jibril be boye masa komai ba ya fada nasa sannan Dsp ya bi bayan Rabi. NAWWARA POV. Ba zan iya cewa ga halin da na ke ciki ba, ni dai nasan bayan abunda ya faru a gidanmu Inna da Jibril sun kawo ni asibiti shi ma sama sama nake gani kamin Jibril din ya shigo ya yi min allura, sai yanzu da na farko sai na ke ganin komai kamar a mafarki hudun da na hango a window ne ya tabbatar min da cewar dare ya yi domin ko da abun ya faru da safe ne misalin tara zuwa goma. Tashi na yi zaune sai naga drip a hannuna, tunawa da Noor yasa idanuwa cika da kwalla, dakin babu kowa sai kayan tea da dan karamin freezer, ina haka Jibril ya turo kofar dakin ya shigo. “Sannu” Ya fada yana cire min drip din a hannu. “Ka yarda da ni Jibril Wallahi Siraj ne” “Na yarda Nawwara” Ya fada sannan ya cire safar hannunsa ya shi ya shiga hada min tea. Wayarsa ce ta yi ringing sai ya aje hada tea da yake ya yi picking. “Eh miya faru? Da gaske? Okay gani nan zuwa” Haka kawai na ji ya fada sai ya juyo ya kalleni. “Anga Noor police sun tafi da shi asibitin Uduth za a duba shi” Da sauri na sauka saman hospital bed din hankalina a tashe. “Jibril zan je” Tare muka fita, a waje muka hadu da Inna sai duk muka dugunduma gaba daya muka nufi Uduth din dake gawon nama. Kamin a isa har jin na yi kamar na runtse idona na ganni gaban asibitin. Muna isa parking space din na asibitin na bude na fito da sauri ni da Inna sai dai duk da haka jibril ya rigamu isa Emergency din kasancewarsa Namiji kuma ya hada da gudu, muna isa muka tararda Dsp din nan na dazu tare da wasu yan sanda sanye da uniform. Muna isa sai ya tare mu wai Jibril kawai zai shiga ya ga Noor ba tare da ni ba. “Kamar ya ni ce mahaifiyarsa fa” “Na sani amman shi zai shiga” Zan kara magana Inna ta rike ni ta ce ta Jibril din ya shiga, sannan ta shiga kiran yan'uwa tana sanar musu a waya. Jibril ne ya fara shiga ni da Inna muka tsaya ina ta jin kamar na yi tsalle na shiga na gani. Muna haka Jibril ya fito a daya daga dakunan dake Emergency din fuskarsa da hawaye, kamin ya karaso kusa da mu ya zame kasa ya fadi yana kokarin rike wata kofa dayan hannunsa na danne da zuciyarsa. [11/11, 10:56 PM] Farar Mace...: *RAI BIYU...♥🖤* Wattpad @KhadeejaCandy 5⃣4⃣ JIBRIL POV. Wani irin nauyi zuciyarsa ta yi masa har ta kai kafafunsa ba sa iya daukarshi, yadda ya ga Noor yana ta masa yawo a idanuwa, but Nawwara da ya hango ta fadi zaune tana hawaye, sai tausayinta ya lullube masa zuciya, a kokorin mikewa ya yi tsaye ya tunkareta yana kokarin buye damuwarsa. “Ya mutu ko?” Ta tambaya cikin rawar muryar da kuka ya dakishe mata ita. “No lafiyarsa kalau” Ya fada yana kokarin tare hawayen da suke son zubo masa. Daukar Numfashi Nawwara ta fara yi idanuwansa na kokarin rufewa kamar wacce za a cirewa zuciya. Inna kuma ta dora hannu saman kai ta fashe da kuka tana rika Nawwara. “Help us please” Jibril ya fada yana karasawa kusa da ita, hankalinsa a tashe dan shi a yanzu ba nata yake ji ba na Nawwara yake ji, sai wasu Nurses suka zo da gudu suka rikata suka dauketa suka dorata saman gado suka nufi wani bangare da ita, shi kuma ya juyo ya dawo dakin da Noor yake kwance kamar gawa likita biyu ya tarar a gurin sai Nurse daya da ta mika masa wasu takardu Jibril ya saka hannu sannan suka dauki Noor din suka fita da shi zuwa dakin tiyata. Jinginawa Jibril ya yi da kofar gurin ya lumshe ido hawaye suka zubo masa, zuciyarsa na ta raya masa kamar Noor ba zai rayu ba, an yanka masa ciki da wuka har hanjinsa sun bayyana ga gefen fuskarsa ma ya kumbura. Sai da ya share hawayensa sannan fito daga dakin ya nufo gurin da Dsp din yake wani irin bakinciki da bacin rai na fisgarsa. “Dsp taya haka ya faru? Na fada maka idan har kun gano inda yaron nan yake ku fada kamin ku yi komai” Dsp be ce masa komai ba sai da suka fito daga Emergency din sannan ya kalleshi ya ce “Aikinmu muke yi Jibril da ace na tsaya kiranka da wata kila yaron nan be rayu ba, domin a can cikin daji muka dauko shi, can cikin arkilla tanki can cikin dajin nan dake saman dutse” “Ina Siraj din yake?” Ya tambaya yana sauke ajiyar zuciya. “Yana can station nasa a tsare shi, karka damu da wannan” “Rabi fa?” “Am sorry jami'an mu gawarta kawai suka samu” “How” Ya tambaya a rude. “We don't know yet but idan komai ya laba zamu bincika” Kansa ya daga sama ya kalli taurari zuciyarsa na mugun
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119