Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 97

Chapter 97

Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel 1,197 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

yi masa na yi ne saboda Noor idan ya gyaru Noor zai amfana idan kuma ya lalace Noor ne zai tagaiyara miyasa ka kasa fahimtata ne?” “Saboda Noor ko? Komai ma ai saboda Noor ne Nawwara i understand” Yana fadar hakan ya saka hannayensa aljihu ya wucewarsa ya barni nan tsaye ina faman hawaye. JIBRIL POV. Daker yake numfashi saboda nauyin da zuciyarsa ta yi masa, daman yanzu abun ya zame masa kamar jiki idan yau be yi ba gobe sai ya yi, sai dai duk wannan abun be taba yarda ya yi gaban Nawwara ba, idan har suna tare abun ya taso masa sai ya kulle office dinsa ko kuma ya bar kamfanin ya dawo gida. Daker ya unkura ya tashi ya nufi bathroom yana shiga sai aman jini yau kan be yi shi da yawa ba kamar yadda ya saba, sai da ya wanke bakinsa sannan ya bude cabinet ya dauko wasu kwayoyi ya hade tare da ruwa sai ya juyo ya fito daga bathroom ya zauna saman kujera ya lumshe ido yana sauke numfashi a hankali. Nawwara ce kadai macen da yake gani idan ya rumtse idonsa, duk da a yanzu ya sadakar ba zata taba zama tashi ba, yana ji a jikinsa kamar ba zata sake rabarsa, but he's happy da ta yi aiki da shi ta maida da shi cikakken namiji, dukan wani canji daya samu a rayuwarsa yasan ta dalilin Nawwara ne, domin be yi zaton zai iya daina shan cocaine ba amman gashi yanzu komai ya zama tarihi, and now he can read Quran duj da be yi nisa sosai a ciki ba amman ya san bakin domin kullum Malaminsa yana zuwa yana koya masa har ma da wasu littafan na daban da kuma bayani akan sallah da wasu abubuwan na addini, shi kansa a yanzu yana jin dadin rayuwarsa Saboda yana jin ya kara kusanci da Ubangijinsa hakan yasa ba janye dokan hana saka hijabi a kamfaninsa domin a yanzu ya fahimce babu komai a cikin addininsa sai rahama da jinka ga gata da addinin musuluncin yake ma ko wane musulmi, bashi da wata matsala ta rayuwa a yanzu sai tunanin Nawwara da ya zame masa kamar abinci, idan suna office har baya son su rabu saboda kewarta da yake komai ya zo masa kamar a mafarki ace Nawwara ce ta sake jiki da shi suna aiki haka, but a duk lokacin da ya tuna zancen aurenta da Bilal sai yaji kamar ya hade zuciya ya mutu, wannan tunanin ya yi tasiri a zuciyarsa da har ya zurfafa masa ciwon dake damunsa, a iya yanzu ya sadakar kuma ya yarda rayuwarsa ba mai tsawo ba ce a duniya, saboda matsala da cocaine ya haifar masa da kuma yawan tunanin da yake a baya ga kuma wanda yake a yanzu, wannan yasa shi yin saku saku da rayuwa. Wani lokacin yana kan kamar ya samu Nawwara ya fada mata hakan sai dai yasan ba zata fahimta ba kuma zata zargeshi da cewar saboda yana son bata alakarsu da Bilal ne, wannan yasa ya danne komai ya barwa zuciyarsa sai kuma mahaifinsa da Siraj da suka san da matsalar. Kalaman da ta yi masa yau a office na cewar zata aje aikinta a wannan satin mai zuwa ne suka haddasa masa ciwon kai har ya abun ya sauko a zuciyarsa, kullum sai ya kirga kwanakin da suka rage na aurenta da Bilal kamar da shi za a daura auren. Ji yayi yana da bukatar ganin dansa domin a yanzu shine kawai farincikisa, a duk lokacin da Noor yake kusa da shi yana jin dadi sai ya dinga jin kamar Nawwara ce a kusa da shi. Unkurawa ya yi ya tashi cikin karfin hali ya koma bathroom ya yi wanka ya fito ya shirya cikin kananan kaya ya feshe jikinsa da turare sannan ya dauki wayarsa da car keys ya fice daga dakin. Har ya fito harabar gidan be daina jin zafin da zuciyarsa take masa ba. Haka ya shiga motar ya dauki hanyar da zata kaishi gidansu Nawwara. A kofar gidan ya yi parking sannan ya dauki wayarsa ya kira Nawwara, bata dauka ba har ta katse sai ya sake kira haka ya jera mata kira hudu ba tayi picking sai ya fita daga motar ya je kofar gidan ya buga, sai gata ta fito hawaye shabe shabe a fuskarta. “Dan Allah dan girman Allah karka sake zuwa kofar gidan nan Jibril da sunan ganina, yanzu yanzu Bilal ya bar gurin nan da ya tararda kai ai ba zai ji dadi ba, saboda kai yau na fada min magana marar dadi, kuma na fada maka cewar komai ya kare a yanzu, tun da zaka iya komai da kanka shiyasa nima zan aje aikin saboda na samu damar kula da Bilal da kuma kaina” “Ina son ganin Noor ne shiyasa na zo” “Idan kana son ganinsa ka sanar da ni zan sa a kawo maka shi har gidanka, amman a i zuwa yanzu ka daina zuwa nan sai na yi aure” “Okay Nawwara ba zan sake ba, and ki bawa Bilal hakuri akan abubuwan da suka faru, na san mun shiga hakkinsa but yanzu komai ya wuce” Ba tare da ta sake cewa komai ba ta juya ta koma ciki, shi kuma ya cikama bakinsa iska ya busar sai ga Noor ya zo da gudu, sai Jibril ya risina kasa ya shafa fuskar dansa sai kuma ya rumgume shi ya lumshe ido. ‘Ni na jawa kaina komai saboda haka dole na yarda da rashinki’ Ya fada a ransa, a fili kuma sai ya dago fuskar dansa ya kalleshi ya ce. “Dukan abunda Nawwara ta yi da wanda na yi mun yi ne saboda kai Noor, ina son ko da bana raye ka kasance mai alfahari da ni a matsayin ubanka” “Ni ban gane abunda kake cewa ba” “Zaka gane wata rana, ina son ka zama mai biyayya ga Mahaifiyarka ita ce zata rayu da kai har ka girma, na yi farincikin da na rayu da kai Noor ina son ka sosai” Ya rumgume shi idanuwansa cike da kwalla, sosai da sosai yake shakar kamshin jikin Noor, domin haka na masa dadi yana jin kusan da dansa sosai. “Noor zamu je yau ka yi weekend gidana ko?” “Ee amman Uncle Bilal ya ce zai je da ni yawo gobe Saturday” “Yaushe ya zo?” “Dazu” “Okay, idan kun dawo sai na aiko a dauko min kai ka ji” “Okay Daddy Momy har da cake ta yi ma Uncle Bilal” Wani irin daga kai ya yi ya sauke numfashi saboda yadda maganar ta sokeshi. “Okay je cikin gida ni zanje gida kar dare ya yi” Ya sumbanci goshinsa. “Goodnight” “Goodnight” Noor ya fada yana daga masa hannu sannan ya shige cikin gida, shi kuma ga mike tsaye ya jingina da motarsa ya lumshe ido yana sauke ajiyar zuciya. Ya samu thirty minutes a gurin sannan ya bude motaraa ya shiga cikin rashin dadin rai. *** *** *** NAWWARA POV. Na farka yau cikin rashin dadi rai saboda abunda ya faru jiya, sam ban jidadin yadda Bilal ya kasa fahimta ta ba, duk da nasan kowa waye dole ya zargi wani abu a tsakaninmu, amman komai ya kare a

Table of Contents

Chapters

119 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});