Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 108

Chapter 108

Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ya yi. “Oucccc am such a fool taya Nawwara zata kirani yanzu ba bayan fushi take da ni” Bude idonsa ya yi ya danna picking ya kara a kunne. “Hello Abbah” “Jibril kana lafiya?” “Lafiya kalau Abbah ya Abuja” “Al-hamdulillah ya Noor yaushe zaka shigo” “Da dai cikin satin nan ne amman yanzu ban sani ba gaskiya” “Ya dai kamata kasa lokaci ka zo” “Wani abun ne?” “Akwai maganar da ya kamata mu yi” “Ba zamu iya yi ta waya ba?” “Magana ce mai muhimmanci zai fi kyau idan kana nan zaka fi fahimtar abun” “Idan magana mai muhimmanci ce ka fada min a waya dan bana tunanin zuwa yanzu” “Magana ce akan aurenka Jibril be kamata kana zaune haka nan ba, yarinyar nan da keke so aure zata yi, zama haka ba ba zai maka ba, na sha baka dama ka fitar da wacce kake so sai ka ce sai Nawwara kuma yanzu gashi yarinyar nan aure zata yi, dole ne idan ta yi aure zaka karbo dan ka dan ba zamu barshi can ba, babu yadda zaka yi ta gujeka kuma ta zauna da danka, na san ka yi kuskure kuma ka zalinceta amman ai an bata hakuri so dole ne ka nemi matar aure wacce zata rike maka yaronka” “Haka ne Abbah amman har yanzu ba a daura mata aure ba ba lallai ne ta auri yaron da yake son ta ba” “Wai kai ba zaka cire ranka a gareta? Yanzu dai mun yi magana da Hajiya (Step Mother din shi) akwai wata yarsa margayi Alhaji Dahiru wato Salima wacce ta fito sai kaje ka gani idan kana sonta ba zamu cilasta maka ba, amman fa bazawara ce yaranta hudu sai dai duka yaran suna hannun Babansu” “No Abbah wanda zai auri Nawwara ya fasa aurenta saboda mahaifiyarsa ta hana just saboda abubuwan da suka faru tsakanin mu, shine sai Nawwara ta bada damar na tura nawa magabatan” Abbah ya dan yi shiru kamin ya ce “Jibril ka tabbata?” “Yes Abba, jiya take fada min haka kuma kasan yadda na ke son ta Abbah, ni yanzu abunda na ke so da kai kasa rana cikin satin nan ka zo ku ga iyayenta” “Jibril ka tabbata” “Yes Abbah” “Shikenan zan samu iyayenka na nan mu yi magana” “Thank You” Daga haka Abbah ya kashe wayar, sai Jibril ya yi murmushi. “Idan ma karya ne Bilal yake ai idan Abbah ya zo dole familynta zasu fada masa gaskiya” Ya fada kana na nufi kitchen dan hada kansa tea. NAWWARA POV. Na ci kuka sosai a daren nan, na kasa yarda da abunda Bilal ya fada min na san yana so na dan me mahaifiyarsa zata shiga tsakaninmu? Miyasa idanuwan wasu suke rufewa su kasa fahimtar komai sai kansu. Washe gari da asuba bayan na gama sallah na dauki qur'ane na karanta Yasin wato zuciyar qur'ane, Suratul Yasin tana da fa'idodi da yawa ga musamman ga mutumen da yake cikin matsala da damuwa ta matsalar mijin matukar ka karanta sau goma sha biyar zama daya idan ya gama ya roke Allah bukatarsa idan da hali sai mutum ya yi sadaka, ba ni da halin karanta Yasin sha biyar hakan yasa na karanta ta sau daya na karanta Ayatul Kursiyo dari domin ita ma tana da nata fa'idan sosai kuma idan Allah ya amsa maka kamar yankan wuka yake, bayan na gama na roki Allah ya zaba min abunda duk yafi zama alheri a rayuwata, sannan na aika Jamila ta siyo min kosai na yi sadaka, a lokacin Sakina har ta shirya mana abun kari sun yi breakfast ni ce kawai ban ci komai ba tun tashina. Dakin Inna na shiga na gaishe ta a lokacin Sakina ta gama shiryawa ita da Jamila suka kama hanyar makaranta, bayan sun fice Inna ta kalleni ta ce. “Nawwara ki yi hakuri da yadda rayuwa ta zo miki, kuma ki yarda duk abunda Allah ya zaba miki shi yafi zama alheri a gareki, ni dai ina nan ina ta yi miki addu'a, dan haka ki daina sa kanki a damuwa, tashi kije ki zuba abinci ki ci” Na tada kai na kalleta idanuwa cike da hawaye. “Amman Inna kina ganin wannan dalilin kawai ya isa yasa Mahaifiyarsa ta hana shi aurena?” “Ya isa mana, idan kika duba daman can ai ba sonki take ba, kuma tana ganin an wulakanta mata da, ni kaina babu irin maganar da bata fada a gabana ba lokacin da na ke zuwa duba shi, amman idan har Allah ya rubuto ke matarsa ce Wallahi bata isa ta hana ba, ki sawa kanki wannan” Na gyada mata kai na share hawayena sannan na mike tsaye ina amsa sallamar da naji wani namiji na yi a waje, bakin kofar na nufa babu mayafi a jikina hakan yasa na leka da kai na yayinda jikina yake cikin gidan, wani saurayi saman babur hannunsa rike da ledoji sai ya miko min. “Ga sako daga Candy Restaurant Jibril ya ce a kawo ma Noor” Kamar ba zan karba ba, sai kuma na mika hannu na karba ba tare da na ce masa komai ba, dakin Inna na dawo na aje ledodin tare da fadin. “Wai Jibril ya aiko a kawo ma Noor, ni ban gane masa ba ya raina abincin gidan nan ko mai?” “Ba raini ba ne, yana ganin dacewar hakan ne kawai” “Ina Noor din?” “Yana bandaki tun dazu ya shiga” Cewar Inna sai gashi ya shigo dakin yana tafiya a hankali. “Momy gurin kaikayi yake min” “Karka sosa dai ciwon zai iya tashi” Na fada masa, sannan na juya na koma dakinmu jin wayata na ringing. Jibril ne yake kirana katse kiran sai ya sake bugowa cikin fushi na dauka “Wai ba zaka daina kirana ba ne?” “Amman kin san ba ke na kira ba Noor na kira dan me zaki dauka? Na ce ina son magana da ke ne? Da na na kira kuma kin sani na ce zan siya masa waya saboda na rika kira ta nan kin hana ya kike so na yi” “Akan me zaka aiko masa da abinci bayan kuma kasan muna da shi” “Ta nan kika bullo kuma? Na aiko masa ne saboda na san ya saba da abincin ba zai iya cin wani abinci bayan wannan ba a yanzu, kuma ina da hakki na ciyar da dana bana son wata dogowar magana da ke dan Allah ki bashi waya na tambayi lafiyarsa ko kuma na zo gida yanzu na duba shi” Kashe wayar na yi na koma dakin Inna sai gashi ya kira na mikawa Noor suka gaisa, sun dade suna waya daga karshe Noor ya fita daga dakin ya koma can gurin bandaki yana magana kadan-kadan da alama wani abun yake fada masa, sannan ya dawo ya kawo min wayar. “Momy wai ya ce yana gaida Inna da kowa da kowa amman ba da ke ba” Ya fada yana dariya, tabe baki na yi na tashi naje ya dauko kofi na zuba koko nasa suga na dawo dakin na zauna ina sha, domin shi kadai na ke jin zan iya sha kasancewar bana cikin dadin rai. Guraren goma da kwata ina yi ma Noor wanka tsakar gida sai ga Baba Sulaiman ya shigo

Table of Contents

Chapters

119 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});