Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 66

Chapter 66

Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

yake na shigo mayun idanuwansa suka dawo kaina har na ƙaraso kusa da teburinsa. “Lokacin Sallah ya yi” Iskarka bakinsa ya busar sannan ya kalli tsadadden agogon hannunsa. “Idan na gama aikin nan zan yi” “Har sai ka gama aikin? Jibril mi ka ɗauki sallah ne? Sallah ita ce rukuni na biyu daga cikin rukunan addinin musulunci, kuma ita ce gimshiken addinin musulunci. Barinta kafirci ne da yake fitar da mutun daga cikin addini, babu addini babu musulunci ga wanda ya bar sallah namiji ko mace!” “Ba fa kafiri ba ne ni, ina sallah” “Na san ai kana sallah, amman ba akan lokacinta ba, ina mamakin avunda zai ɗaukewa mutun hankali har ya watsar da bautar Ubangijinsa, kasan irin azabar da Allah ya tanadarwa masu wulaƙanta sallah kuwa? Jinkira sallah lokacin ya fita ba tare da wani uzuri na shari'a ba, wannan tozarta sallah ne kamar yadda Allah ya faɗa a suratul Maryam aya ta hansi da tara zuwa sitti : Sai mutanen banza suka maye bayansu, suka tozarta sallah, suka bi sha'awace-sha'awace na saɓo; to ba da daɗewa ba zasu haɗu da gayyu wato wani gwalolon azaba a cikin wutar jahannama, sai fa wanda ya tuba. Farkon abunda za a maka hisabi da shi a cikin ƙabarinka sallah ce, kuma ita ce zata tayaka zaman ƙabari (Allah ka bamu ikon tsaida Allah akan lokaci 🙏😭)” Tun da na soma maganar yake kallona fuska a sake, da alama na burgeshi ne ko kuma mamakina yake oho, but to my surprise sai na ji ya ce “Thank you, da kika tunatar da ni, babu wanda ya taɓa faɗa min wannan, inshallah zan gyara ko dan na samu damar rayuwa da ke a aljanna” “Aljanna kowa gidansa daban, na Jibril daban haka ma na Nawwara daban” Dariya ya yi kamar ba shiba ya miƙe tsaye ya nufi wata ƙofar da nake zaton banɗakine a ciki. Ni kuma na juyo na fito, sai na samu computer tana nuna min Rabi da ke waje, sai da na zauna sannan na buɗe mata sai ta shigo fuskarta a sake kamar ko yaushe. “Ga sim ɗinki anyi miki dukan abunda ya dace” “Thank you, amman yanzu idan ina son na kira general meeting a madadin Jibril ya zanyi?” “Sir Jibril zaki ce ko kuma mai gida” Ta faɗa sannan ya buɗe wani ɗan ƙaramin littafi dake gefen teburin ta soma nuna min “Wannan number zaki kira, idan an ɗaga ba sai kin tsaya gaisuwa ba, kawai ki ce Sir Jibril ya ce haɗa masa general meeting, idan emergency ne sai ki faɗa, idan kuma meeting ɗin yana da date da time sai ki faɗa, zasu haɗu a hawa na biyu room 24 domin shi ne kawai ɗakin da yake iya ɗaukar yawan ma'aikatan da ke kamfanin nan, idan har ya yarda ki yi magana a madadinsa zaki iya zuwa kiyi idan kuma shi zaiyi da kansa sai ki raka shi” “Thank you so much” “Your welcome” Sannan ta juya ta fita, ni kuma na saka number da ta nuna min a telephone zuciyata na ta raya min kar na yi, idan har na yi haka na yi karanbani, wata zuciyar kuma na nuna min idan har na yi haka na taimaiki Jibril da rayuwarsa har da da sauran ma'aikatan. Sai kawai na dannan kiran na ce ina buƙatar a haɗa min meeting ɗin gagawa, ni kuma na tashi na fita riƙe da wayata na nufi lifter, ina sauka hawa na biyu na soma ƙirga ɗaki, har na hango ɗakin da mutane suke shiga. Tsayawa na yi sai na kasa ƙarasawa ina ta tunanin ma yadda zan ce musu abunka da wanda be saba ba, sai kawai na juya na koma lifter, na yi mamakin yadda ina isowa bakin ƙofar office ɗin sai kawai ta buɗe min. Ina shigowa na samu Jibril tsaye yana jiran shigowata. “Akan mi kika kira general meeting kuma emergency?” “Am sorry” “Ba hakuri na ce ki ba ni ba, dalili zaki faɗa min” “Da na yi ƙoƙarin na faɗa musu idan lokacin sallah ya yi kowa yaje ya yi sallah, sai kuma na ga kamar na maka karanbani” “Karabanni ne mana, ba yau yau kika kama aikin ba?” “Am sorry” Na faɗa cike da nadama sai ya matso kusa da ni. “Is okay, zan faɗa musu da kaina indai har haka kike so, follow me” Yana faɗar hakan ya nufi ƙofar fita na bishi, tare muka isa da kansa ya faɗa musu cewar a yanzu da lokacin sallah ya yi kowa ya aje aikin da yake yaje ya yi sallah, daman akwai masallaci a cikin kamfanin. A yanayin yadda fuskokin musulmin ma'aikatan suka nuna sun yi farinciki sosai kuma sun nuna jindaɗinsu har ma da yin godiya. Ina tsaye gefen Jibril Bilal na kallona kamar zai cinye ni, irin kallon nan da mutum zai kasa gane manufarsa sai hakan yasa duk na bi na tsargu, mu muka fara fita sannan sauran suka fito. A bayan na tsaya ina amsa waya shi kan gogan na ku tuni ya yi nisa tare da Siraj. Dpo ne ya kirani wai an bashi number ta daga gida, saboda ya zo be sameni ba kuma yana son magana da ni, a ina nake ya zo ya tafi da ni. “Na kusa dawowa aiki, idan na dawo zan kira ka” “Okay” Daga haka na kashe wayar, na cigaba da tafiyata. Ko da na shiga office ɗin ƙpfar Office ɗin Jibril tana buɗe ina hango abokinsa sai dai ban san mi suke tattaunawa a akai ba har sai da na zauna sannan na soma jiyo muryar abokin nasa. “Be kamata ka sake mata har haka ba, so ai ba hauka ba ne....” Sai kawai na ji an ba ƙofar gam an rufe, bayan wani ɗan lokaci sai abokin nasa wato Siraj ya fito kamar cikin ɓacin rai ya fice ba tare da ya kalli inda na ke ba. Takardar da ke gabana na ɗauka na duba sai na ga lokacin meeting ɗinsa da wani Hon Usman Dahiru ya yi, a maimakon na kira sai kawai na tura ƙofar na shiga. Saurin saka bayan hannunsa ya yi ya kare hancinsa, sai dai abunda be sani ba abunda ke gabansa a farar takarda mai kamar hoda ya taɓa masa hannu, juyawa na yi zan fita sai ya kira ni. “Naj” Ina juyowa ya ce “Madarace na ke sha ina fama da ulcer” Ni dai ban ce masa komai ba na juya na fita, ina shirin zama sai gashi na fito daga office ɗinsa ya biyoni. “Madara ce Naj” Nan ma kallonsa kawai na tsaya yi, sai ya ɗaga hannayenasa sama domin shi ma yasan ban yarda da shi ba. “Fine cocaine ce shikenan?” “Allah ya wadaranka Jibril, kullum abunka gaba yake ba baya ba, har yanzu akwai tattoo a jikinka, yanzu kuma cocaine kake sha bayan neman matan da kake? A haka iyeyenka za su nuna ka a matsayin ɗansu ɗan ka kuma ya nuna ka a matsayin uba? Iya yau kawai na zauna da kai, amman na ga halaye masu marar kyau a tare da kai, wasu baka canja ba wasu kuma sabbi ne, na yi nadamar da na taɓa saninka a rayuwata Jibril...” Na faɗa cikin hawaye da kuka

Table of Contents

Chapters

119 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});