Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 23

Chapter 23

Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ke har abada!” “Ba zan gudu ba, ba zan je ko'ina ba na miki alƙawari, ko da kuwa Inna zata yanka ni ne” Ya faɗa cikin kuka. Sai na zaunar da ita ina share mata hawayenta, tare da yi mata wasu kalaman da zasu ƙarfafa mata guiwa. Ban bar ɗakinba sai da na tabbatar kuka da take ya tsagaita, sannan na fito na shiga ɗakin Inna. Gurin da barta a nan na sameta sai wannan karon tana daga kwance ne, gurin da fuskarta take ya jiƙe da ruwan hawaye kamar an zuba ruwa a gurin. Daga inda na ke tsaye na soma mata magana ciki da ƙarfin hali. “Habiba ta aikata abunda ta aikata ne saboda tana tunanin kamar hakan shine mafita, ta aikata abunda ta aikata saboda Baba da ke da kuma mu duka, kin yarda da ƙaddarar da ta samu Baba har kika riƙa bani haƙuri, shin miyasa ba zaki yarda da wannan ƙaddararba...?” Tashi tayi zaune ta kalleni a tsawace ta amsa min “Saboda ita ta kai kanta” Na matsa kusa da ita “Akwai ƙurciya da tare da ni balle kuma Habiba, hankalinta da tunaninta be kai inda kike tunaniba, babu banbanci tsakanin wannan ƙaddarar da kuma wacan dukansu ƙadarori ne, babu wanda ya dace ya nunawa Habiba soyayya a yanzu fiye ke, babu wanda zai mata magana hankalinta ya kwanta fiye da ke” “Habiba ta ɗauko wata rayuwa wacce bata gidan nan ba, sam wannan ba tarbiyarmu ba ce” “Wannan kaɗai ya isa ya tabbatar miki da cewar ƙaddarace, ashe ko haka ya isa yasa ki rumgumeta ki nuna mata kina tare da ita” Ajiyar zuciya ta sauke kana ta kalleni “Kina da ƙarfin zuciya Nawwara, haƙiƙa Muhammad Noor ya yi sa'ar uwa” “Ƙarfi guiwata taki ce Inna, kin rigani zama uwa kin fini sanin komai a rayuwa” Wani dogon numfashi taja ta sauke tana cige baki ta ce. “Wani lokacin kaina ya kan kulle har na yi tunani ba dai-dai, Allah ya kan jarrabi bawa da abubuwa da dama har bawa ya ga kamar Allah baya sonshi” “Zamu jarrabeku da yunwa da tauyewar ƴaƴan ittatuwa da rayukan da dokiyoyi, ka yi bushara ga masu haƙuri (Masu jure waɗannan jarabce-jarabce) Waɗanda idan masifa ta samesu sai su ce (Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un) Mu ɗaga gurin Allah muka fito kuma a gare za a maida mu, kyakkawar yabo ya tabbata agaresu daga Ubangijinsu, haka Allah ya faɗa a ciki alƙur'ane mai girma, akwai kuma inda Allah yake cewa ‘Ko wane tsanani yana tare da sauƙi har ya sake maimaitawa Haƙika ko wane tsanani yana tare da sauƙi, sai kuma ya ce Fasbir sabaran jaamila wato ya kai Annabi ka yi haƙuri haƙuri mai kyau, Allah yana tare da masu a haƙuri. Inna duka waɗannan Allah ne ya faɗa. Kin tuna lokacin da na yi aure? Na fuskanci wulaƙanci da ƙalubale kala-kala a gidan aurena, har na fito na haifi Noor cikin baƙinciki da damuwa, na sake wani auren har na fara jindaɗi sai Allah ya karɓe abunsa, na sake dawowa cikin wannan wahalar, sa'anina da wanɗanda muka yi makaranta tare da su, duk sun zama manyan mutane har basa son abota da ni, ni kuma ina nan, amman hakan be taɓa saka ni na yi tunanin ko Allah baya so na ne ba ko da sau ɗaya, da ace Allah ya yi ni kafira da zan yarda Allah baya so na saboda komai na tara a duniyarnan zan mutu na bar shi naje ƙiyama na shiga wuta, amman kin ga yanzu zan iya sha wahala a nan idan har na aikata aiki na ƙwarai ina zuwa ƙiyama kai tsaye aljannah zan wuce, kuma kin ga can ba a mutuwa ba a baƙinciki balle tsufa. Ki rumgume ƙaddarar nan Inna, karki yi Habiba abunda zai ƙara mata baƙinciki, ta ce min zata gudu ta bar gidan nan saboda kar ta zama silar ajalinki” Da sauri Inna ta miƙe tsaye da sauri hankalinta a tashe. “Ina take?” “Tana ɗakinmu” Da gudu ta nufi ɗakin, ni kuma na rufa mata baya. Ko da muka shiga ɗakin sai muka samu babu kowa a cikinsa, daga ni har Inna sai da gabanmu ya faɗi, Inna ta juyo ta kalleni nima na kalleta. “Habiba” Na kira sunanta da ƙarfi, sai ta amsa min daga bayan gambu da take ɓoye, a zatonta Inna zata faɗa mata wata maganar marar daɗi ne ko kuma ta daketa hakan yasa ta ɓuya a nan. Da sauri Inna ta duba gurin domin ta fini kusa da shi sai ga Habiba a tsaye tana hawaye jikinta na rawa tana jiran sakamakon Inna. “Zo nan ƴata na yafe miki duniya da lahira, Allah ya yi miki albarka, ya isar miki” Inna ta faɗa tana miƙa hannu taja Habiba jikinta ta rumgume, sai suka fashe da kuka, sai nima na fara nawa kukan da daga inda na ke tsaye, a raina kuma ina ta godiyar Allah. *** *** *** Haka muka wuni a cikin gidan kamar waɗanda akayi wa mutuwa, Sakina da Jamila ma sun lura da haka su kansu basa wani sakewa saboda ganin kamar muna cikin damuwa, Noor ne kawai yake ta sha'aninsa shi kan be ma damuba. Washe gari kasa zuwa aiki na yi saboda na tashi jikina da kuma zuciyata babu daɗi, duk yadda Inna ta so naje sai na ƙi, su Sakina kawai suka je makaranta, mu kuma muna gida shiru-shiru babu wani motsin kirki da ɗayanmu ke yi, misalin ƙarfe ɗaya da rabi Bilal ya kirani ina ɗauka sai ya fara tambaya miyasa ban je aiki ba, ni kuma na amsa masa da cewar babu komai, sai dai ban yarda ba yana ganin kamar ɗan ya ganni babu hijabi jiya ne yasa na yi fushi. Jikin Habiba ya ƙara tsanani da yamma, har na ke bada shawarar mu kaita asibiti sai Inna ta ƙi saboda aganin asiri mu zai tonu. “Idan mukaje asibiti zasu faɗa mana ciki ne, wanda nasan nan da nan za a ji a unguwar nan, ya kike so acewa Yakumbo da kuma mutane babban gida? Da wane ido zamu kallesu, yanzu zasu ce dan margayi ba shi da rai ne na ƙyale Habiba ta aikata wannan abun ni zasu ɗorawa laifi” “Da ido da muke kallonsu Inna, tun bayan da aka gama amsar gaisuwa kin saki ganin ƙafar wani a gidan nan? Ba mu da nisa da su amman basu taɓa ɗauko ƙafa suce bari su leƙo mu suga ya muke ba, kowa harkar gabansa yake” Ta yi shiru kamar ba komai kamar mai tunani can kuma ta kalleni “Ni da wai na ce ko zubar da cikin zamu yi?” Gabana ya faɗi, naji maganar kamar saukar aradu. “A'a Inna idan muka je zubar da cikin ai dole za'aji” “Ba asibiti ba wai gida” “Taya zamu zubar da ciki gida?” “Ƴan kayan ɗacin nan da ake badawa mana, tun da kin ga yanzu be yi ƙwari ba kuma a iya busa masa rai ba, idan har be zube ba sai mu ƙyaleta” Na kasa cewa komai saboda na lura ranta ya kwaɗaitu da a zubar da cikin, duk da ina ganin zubar da cikin yana daga cikin alamomin rashin yarda da ƙaddara. Tausayin Habiba ne ya kamani sai na ji ina

Table of Contents

Chapters

119 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});