Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 64

Chapter 64

Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

har Sakina ta dama kamu, Inna kuma ta aiki Jamila da Noor su siyo ƙosai da suga, bayan sun dawo muka sha kunun har Inna sannan na kama kan Noor na yi mas addu'a irin wacce Annabi yake yi ma jikokinsa Hasan da Husaini U'eethukumaa bikalimaatil-laahit-taammati min kulli shaytaanin wa haammatin, wa min kulli 'aynin laammatin. Bayan na gama da Noor na karantawa Jamila sannan na suka kama hanyar makaranta tare da Sakina. Ni kuma na tashi na shirya cikin wata atamfar roba na saka Hijab ɗina mai kama da atamfata, sannan na zo yi ma Inna sallama da karɓar kuɗin Napep. “Inna zan tafi aikin” “Allah ya tsare Nawwara Allah ya miki albarka, ban miki faɗa jiya dan wani abun ba sai dan ki gyara” Ta faɗa tana miƙo min ɗari biyu. “Ko babu komai kika min faɗa ba zanga laifinki ke uwace kina da damar ki yi duk yadda kike so da ni, kuma abunda kika min faɗa akai kina da gaskiya, ni kaina na san ina da buƙatar ganin na canja ta yadda zan cigaba da rayuwa na manta komai, ni dai fatana ki kasance mai min addua da kuma haƙuri da hali na miki alƙwarin zan canja” “Addu'a ai wajibi ce ga dukan uwa ta yi ma ƴaƴanta, Allah ya miki albarka ya baki miji na gari wanda zaki ji daɗin zama mai son ki tsakani da Allah” “Amin Inna” Na faɗa ƙasan zuciyata na ta kira min Bilal, tun jiya be kirani ba kuma be dawo ba ni kuma ban kira ba. Sai da na fito daga gidan sannan na soma kiran Bilal amman wayarsa a kashe, hakan yasa ni jin babu daɗi zuciyata na raya min kamar fushi yake da ni, daman na san dole sai ya zargi wani abu ganina tare da Mustapha. Na yi sa'ar samun napep da wuri amman sai da ya sauke mutun biyu sannan ya ƙarasa da ni inda zai kai ni, koda na isa tara saura kwata tunda na doshi kamfanin zuciyata ta soma rayamin wasu abubuwan sai sai tunawa da maganganun Inna yasa na kawar da komai na nutsa kai cikin kamfanin, na yi mamakin yadda kowa yake kallona kamar wace suka ga baƙuwar fuska, wataƙila an faɗa musu wani abun ne akai na ko kuma dan na yi latti suke kallona oho, ban damu da cire Hijabina ba a ganina yanzu ai an canja min aiki dan haka bana buƙatar cire Hijabi duk kuwa da kasancewar ban taɓa ganin kowa da Hijabi ba a kamfanin. Har na doshi lifter tunani na ke irin kallon da Jibril zai min da kuma irin wanda zan yi masa idan har na yi aiki a gurin. Ina dosar office ɗinsa gabana ya shiga faɗuwa, ba faɗuwar tsoro ba ko fargaba ba faɗuwa irin ta maƙiyi zai yi arba da maƙiyinsa. Kamar wacan zuwan nawa na farko haka na yi saka buɗe min, yau ma sai da aka tantance ni a cikin ɗan ƙaramin gilashin nan mai bayyana komai na jikin mutun sannan aka bani damar shiga Office ɗin, ban ji ya ce na aje wayata da ƴar ƙaramar jikar da ke hannuna ba, ni kuma ban aje ba na shiga da abu ta, shi ɗin ne dai mutumen da na taɓa tararwa wacan karon. Tun kamin na yi magana ya rigani. “Please go in” Ya doshi ƙofar da ya nuna min gabana na ƙara faɗuwa, ajiyar zuciya na sauke sannan na kai hannu ya tura ƙofar, ba tare da na waigo ba na maida ƙofar na rufe ina kallon bayansa, kasancewar ya bani bayana ne domin shi yana tsaye ne jikin window ya maido hannayensa baya yana kallon waje. Har yanzu akwai tattoo ɗin taurari a bayansa, mamaki ya kamani sosai ganin sunana rubuce cikin style ɗin wasu harufa tattoo a hannunsa, nasan be san da shigowata ba ko da yake yaji an buɗe ƙofa, ni kuma na gagara kiran sunansa sai kawai na ce “Excuse me” Da sauri ya juyo ya kalleni, irin kallon nan na mamaki sannan ya yi hanzarin warware hannun rigarsa ya nufi ƙasaitacciyar kujerarsa ya zauna. “Kin zo latti, ba a faɗa miki 8am zaki riƙa zuwa ba?” Na yi shiru ban amsa masa ba. Sai ya soma kallona daga sama zuwa ƙasa. “Ba a saka mana Hijabi a nan next time ki san irin tufafin da zaki saka” “Ba za'a saka muku Hijab ba saboda ku ba musulmai ba ne?” Ya yi murmushin gefen fuska sai ya taso daga inda yake ya doso ni yana faɗin. “Aiki muke a nan ba addini ba” “Da wannan aƙidar ka cuci kanka, kai kana ganin kamar babu ruwan addini ko Allah a cikin abunda ya shafi aikinka ko rayuwarka ko? Kana da mummunar aƙida Jibril” “Ko?” Ya tambaya yana ta matsowa kusa da ni ni kuma ina matsawa baya, har sai da na kai jikin ginin ɗaki, sosai ya matse ni yana kallon fuskata idanuwa cikin nasa idon, har na buɗe baki na yi magana sai ya duƙa ya kama zanen atamfata ya murja. “Me kake ƙoƙarin yi ne?” Ya miƙe tsaye bakinsa kusa da nawa kamar zai haɗe bakinmu. “Dirty mind, ni ba ɗan iska ba ne” Ya faɗa kaɗan kaɗan kamar mai raɗa, sannan juya ya doshi kujerarsa. Hakan ya bani damar lumshe ido na sauke ajiyar zuciya, jin abunda yake faɗa yasa ni buɗe idon ina kallon yadda ya haƙimce saman kujerarsa mai juyawa yana min magana cikin isa. “Dan me za ki saka min tamfar roba?” “Ba kai na sakawa ba, kaina na sakawa” “Miyasa kika yi rejecting kuɗin da aka baki ki siye wasu tufafi?” “Bana da buƙata, tufafin jikina sun isheni” “Saka ƙananan tufafi marar daraja na zubarwa kamfanin da ƙima, ya kamata ki san wannan” Ya faɗa fuskarsa babu alamun dariya, sannan ya danna telephone ɗin da ke kusa da shi ya yi magana da halshen nasara. “You can go now” Sannan ya kalleni. “Tea please” Tsaye na yi a gurin kamar an dasani, shi kuma ya bawa banza ajiyata yana ta aiki da system ɗin da ke gabansa. Waige-waige ɓa farayi har na hango teburin dake ɗauke da kayan tea na doshi gurin zuciyata na ta raya min maganar ɗazu, wai shi ba ɗan iska ba ne, wato ni ce ƴar iskar ko? Har na haɗa tea ya kawo masa maganar bata daina min yawo a kunne ba. “Ƙarfe uku zaki tashi aiki, idan kuma har muna da meeting ko aiki da yawa zaki iya kaiwa har dare, kuma a shigo min office haka nan kawai, saboda karki tararda ni cikin wani yanayi, har sai idan ni na kiraki, idan wata magana ce akwai telephone a gurin dannawa kawai zaki yi ki kirani” Ban ce masa komai ba na juya na fita, zuciyata na mugun ƙuna, anya zan iya jurewa na yi aiki a ƙarƙashin Jibril? Sai da na ƙarewa office ɗin kallon sannan na zauna a saman kujerar mai juyawa, komai daki daki na bishi ina kallon da dubawa sannan na kula da ƴar danjar da ke ƙara a gefen teburina, sai kuma computer ta soma nuna min mutumen da ke waje, wato Bilal yana riƙe da wasu takardu. Gabana ya faɗi sosai sai na soma tunani da

Table of Contents

Chapters

119 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});