Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 100

Chapter 100

Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Inna ta kasa ce masa komai, ni da nake zaune nesa da ita na kalleshi cikin hawaye na ce “Ban san komai a akan batan Noor ba, idan kuma baka yarda da ni ba, zaka iya sakawa a kulleni kamar yadda ka yi ma Bilal” “Na rasa mahaifiyata Nawwara a lokacin da ban san miye duniya ba, ban sani ba ko zan iya jure rashin Noor” Haka kawai ya fada ya mike tsaye ya shafa kansa ya fice. Sai da ya fice sannan Inna ta ce “Miyasa baki fada masa gaskiya akan abokinsa ba? Mai yiyuwa shi ya sace Noor” “Idan kuma ba shi bane fa Inna? Sai mu dauki laifin mu dora masa? Mai yuyuwa yan satar mutane ne suka sace shi ko kuma yan garkuwa da mutane sai mu dauki laifin mu dora masa?” “Amman idan ba a bullowa wannan matsalar da wuri ba zata iya zama babba, kina da dalili da hujja mai karfi ta zargin wannan mutumen kuma shi kadai ya rage a yanzu wanda zamu iya zargi” Tabbas ni kaina zuciyata a yanzu Siraj take zargi, amman ina cikin kwankwanto saboda kar na yi zargi na jefa rayuwarsa cikin matsala daga karshe kuma ya zama ba shi din ne ba. Ina jin kewar da na sosai kullum mafarkinsa na ke yadda muke rayuwa da shi a cikin gidan yana ta min gizo a ido wani lokacin har ji na ke kamar yana kirana. JIBRIL POV. Daga gidansu Nawwara kai tsaye ya nufo gida har ya iso be daina hawaye ba, zuciyarsa kuna bata daina kuna ba, nan da nan ya fara tarin jini sai da ya saka tissue ya goge, babu wanda idanuwansa suke son gani kunnuwansa suke son jin muryarsa a yanzu irin Noor, daman tun kamin faruwar hakan jikinsa yake masa ba dadi ashe na rabuwa da dansa ba, rabuwansu na karshe ya tuno lokacin da yaje daukarsa yace Bilal zai fita da shi, rumgumar da ya yi masa ya dingajin kamar yanzu yake masa ita. “Ina kake Noor ina kake?” Ya tambaya yana buga sitarin motarsa yana kuka sosai kamar makaramin yaro. “Miyasa nake ta rasa abubuwan da suke da muhimmanci a rayuwata ne? Miyasa ne? Allah karka karbi rayuwar da na a yanzu da na fi bukatarsa Allah kada ba basu damar cutar da shi Allah ka kubutar min da dana” Kamar zai fadi haka ya fito daga motar yana kuka be damu da ma'aikatan gidan su ga kukansa ba shi dai matsalarsa da isheshi. A falo ya zauna yana ta misalta irin yadda Noor yake idan ya zo gidan, sai kuma ya dauko wayarsa ya bude gallery yana kallon hotunan Noor da kuma wanda suka yi tare. “Wa zai min haka a duniyar nan? Mina tarewa wani? Bilal mi na maka? Oh Allah” Ya mike tsaye yana share hawayensa, a dare kasa bachi yayi kamar dai ko wane dare yana ta aikin sallah da rokon Allah ya fito masa da dansa, kudi mai yawa ya diba ya bawa Malamin nan mai koya masa karatu akan yasa a yi masa addu'a Allah ya bayyana masa dansa. Yana zaune yana shan ruwan tea kamar kullum domin tun da abun ya faru baya cin komai sai ruwan tea maganinsa ma ya daina sha. Sai ga Kiran Abbah ya shigo wayarsa cikin yanayin damuwa ya daga. “Assalamu Alaikum” “Wa'alaikassalam Jibril ka zo gida yanzu nan ina jiranka” “Okay” Yana kashe wayar ya mike tsaye ya shiga bedroom ya canja kayan jikinsa daga jallabiya zuwa kananan kaya, a gaggauce ya fito saboda yasan yau Abbah zai bar sokoto yasan dalilin kiransa ba zai wuce ya fada masa Maganganun hakuri ba. Ko da ya isa Abdullah fodio road ya tararda Abbah tare da wani bako, bayan sun gaisa sai Abbah ya gabatar masa da shi. “Ga Dsp Sani Muazu nan na fada masa komai akan case din Noor, abunda yasa na ce kasa a saki Bilal saboda a bullo masa ta wata hanyar, tun da har ya kwashe kwana uku a station da duk irin wahalar da ake bashi be fadi gaskiya ba zai taba fada ta hanyar tsiya ba, so wannan dsp ya san yadda xai bibiyi Bilal har a gano gaskiyar lamarin” “Thank you Abbah” Abbah ya dafashi. “Ka kwantar da hankalinka Jibril Noor dinka yana nan lafiya kalau, kuma za a gano shi da yarda Allah duk wani bayani sai kanyi masa ni yanzu zan wuce” Sai da Abbah ya koma ciki yayi yan mintuna sannan ya fito Jibril ya raka shi har gurin mota suka yi sallama dan baya jin xai iya binsa har airport, bayan Abbah ya wuce ne Jibril ya dawo ya cigaba da yi ma Dsp bayani akan abunda ya sani a game da Bilal sai Dsp ya nemi hoton Bilal da addirensa da komai nasa. Suna haka wayar Jibril ta yi ringing yana dubawa ya ga Number Siraj cikin sauri ya dauko a tunaninsa ko zai sanar da shi wani abun ne, domin shi ma ya damu sosai akan batan Noor duk wani shiga da fita da ake tare da shi ake yinsa. “Hello Siraj” “Jibril kana ina ne?” “Ina nan Abdullah Fodio Road lafiya?” “Nawwara ce ta kirani a waya tana kuka tana min magiya wai na fada mata inda danta yake” “What? Ita da kanta?” “Yes ita ce ni abun ya bani mamaki ne” “Kana ina ne? ” “Ina gida” “Bari naje na sameta” Yana kashe wayar ya mike tsaye yana kallon Dsp “Taso muje can inda zamu samu hotonshi” Tare suka fito sai Dsp ya shiga motar Jibril suka nufo gidansu Nawwara. Sai da ya tsaya nesa da gidansu Bilal ya nunawa dsp gidan sannan ya karaso kofar gidansu Nawwara, kiranta ya yi ya sanar mata yana kofar gida yana son magana da ita sai ta ce ya shigo ciki. Ko da ya shigo ya sameta tsakar gida tana aikin kuka duk ta rame ta yi baki sosai kamar ba ita ba, sai da ya gaisa da Inna sannan ya zauna saman tabarmar da Inna ta shinfida masa yana kallon Nawwara har cikin ransa yake jin kukanta. “Ki yi hakuri Nawwara dan Allah ki daina kukan nan kina tada min da hankali” “Jibril Siraj ne ya sace Noor” Ta fada cikin kuka. “What?” Ya kalli Inna sai kuma ya maida dubansa gurin Nawwara a tunaninsa bakinciki ne yake son taba ta. “Listen Nawwara...” “Wallahi ba karya na ke ba, shi ya kade Noor kuma yana cikin plan dinsa kashe Noor da ni da kuma kai” “Okay na ji shikenan zan masa magana” “Ba hauka na ke ba Jibril ka tambayi Rabi ka ji ita ta fada min komai, shiyasa na koma aiki tare da kai nasa ka karbe kamfanin daga hannunsa ya dawo hannunsa shine yake kiran Abbah ya fada masa komai saboda ya lalata maka rayuwa yasa ka fara shan cocaine, kuma shi ya kade Noor da mota lokacin da suka taso makaranta, Noor ya ganshi shiyasa ya ki yarda su yi ido hudu da Noor saboda karya nuna shi” “No Nawwara Bilal ne ya kade Noor” “Ba shi ya kade ba, lokacin da Noor ya yi hadari Bilal yana kamfaninka yana aiki, shine duk ya tsara wannan Jibril ka karda da ni, Rabi

Table of Contents

Chapters

119 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});