Chapter 55
Chapter 55
Taya zan zuba har milion ɗaya na siye gidan dubu ɗari biyar sannan ka zo ka ce na fansar maka ni ba a min wasa da kuɗi sai dai ni na yi ma wasu wasa! Mu kamfaninmu baya siye da siyar da gidaje ni ma kuma ba sana'a ta ba ce, so wannan gidan akwai dalilin da yasa na siye shi, so walk out of my office ba zan siyar ba” Mustapha ya tashi tsaye yana murmushi. “Zuciya na raya min ka siye gidan nan ne saboda wata manufa is that the reason yasa ka basu lokacin tashi? Kuɗin ka be amfane ka ba Mr Billionaire, tun da har zuciyarka zata raya maka siye gidan talakawa kuma ka takura musu bayan kasan babu su da inda zasu koma me suka maka ne?” Jibril ya ƙyalƙyale da dariya daga inda yake tsaye ba tare da ya juyo ba ya ce. “Na siye gidan ne saboda na isa na siya, ni mijin Nawwara ne idan ma akan ta kake wahalar da kanka so ka daina yaudarar kanka” Mustapha ya yi murmushi tare da zuba hannayensa aljihu. “Her ex-husband dai Nawwara bata da wani miji a yanzu” Jibril ya juyo yana kallon Mustapha murmushin da ke fuskarsa yana dusashewa, can kuma sai ya fara dariya. “Yeah yeah it Funny am laughing, amman bari na faɗa maka wani abu ka bar irin wannan wasan i don't play when it comes to Nawwara” Mustapha ya nufo kamar yadda Jibril yake doso inda yake. “Kana son zaka saketa? Ƙarya so kake mata tun da har ka iya siye gidan da suke ciki dan kawai ka takura mata, a haka ake so? Ko dai jikinta kake so ne huh? Da nine na samu damar auren Nawwara ko ƙuda ba zan bari ya taɓa ba balle har ya kai ga na saketa ko da kuwa kullum ruwan zafi take zuba min a jiki, but look at yourself ka yi arzikin aureta amman ka saketa ooph so sad maybe rabona ce shiyasa ka saketa” Cewar Mustapha yana wani abu da fuska kamar mai magana da ƙaramin yaro yana murmushi, cikin zafin rai Jibril ya kai masa bugu a fuska ya sake kai masa wani a gefen baki, cikin zafin nama Mustapha ya ɗago zai rama sai Siraj ya yi saurin riƙeshi ya jashi baya, hakan ya bawa Jibril ƙara kai amsa wani dukan a baki sai jini ya fara zuba. “Abraham” Siraj ya ƙwalawa PA ɗin Jibril kira sai gashi cikin ɗakin da sauri. “Riƙe min wannan” Da sauri ya Siraj ya saku Mustapha ya nufi Jibril ya riƙe shi yana faɗin. “Take him out” Ganin Abraham ɗin ba zai iya fitar da shi shi kaɗai ba, yasa Siraj ya saki Jibril ya nufi Mustapha suka fitar da shi tare. Juyowa Jibril ya yi ya nufi teburinsa ya buge System ɗin da ke saman ta faɗi ƙasa. “I need to see her, we need to talk zan bata haƙuri zan yi komai akan ta, ba zan bari wani ya ɗauki muhallin na a zuciyarta ba” Komawa ya yi gaban teburin ya ɗauki wayarsa ya danna number Abbah, yawo ya riƙa yi cikin office ɗin zuciyarsa na mugun bugawa, a ƙarshe ya samu tsayawa jikin window saboda Abbah ya yi picking. “Afternoon Abbah” “Afternoon Jibril ya aiki?” “Alhamdulillah, Abbah we need talk” “About?” “Nawwara Abbah na gano inda take” “Ai nasan zaka gano inda take, shiyasa na ce ban yafe maka kaje ƙofar gidansu da sunan neman gafararta ba, kai yanzu dan baka da kunya sai kaje ƙofar gidansu har ka iya haɗa ido da ita? Mu muka zaɓa maka ita lokacin da zaka aureta ka butulce ma umarninmu ka ce kai ba haka ba yanzu kun rabu miye na bibiyar yarinyar mutane?” “Na tuba Abbah Wallahi na tuba” Ya duƙa har ƙasa kamar yana gaban Abbah. “No ban yarda ba” “Abbah ko dan na nemi gafararta ba, ina da buƙatar na tambayi abunda yake cikin maybe ta haihu, you know how i love to see my carbon copy Abbah kasan yadda na ke son haihuwa” “Sai ka ƙara aure ka yi haƙuri har Allah ya baka” “Abbah kasan na yi aure ba ɗaya ba amman Allah be bani haihuwa ba, taya Allah zai bani haihuwa bayan na yi masa butulci” “Sai ka yi haƙuri" Abbah na faɗar haka ya aje wayar. Sai Jibril ya miƙe tsaye yana cizon lips ya wulgarda wayar ƙasa iya kar ƙarfinsa, kamar mahaukaci ya fara bugun ginar gurin da duka hannayensa har sai da jini ya fitowa ko wannensu sannan yaja baya yana haƙi. Zinatu ce ta shigo office ɗin da sauri hankalinta tashe ta doso inda Jibril ya ke. “Miya same ka haka?” Zata taɓashi sai ya yi baya yana ɗaga mata ɗayan hannunsa. “Don't touch me, na yi ma kaina alƙawarin ba zan sake taɓa wata mace ba sai Nawwara, wata mace kuma ba zata sake taɓa ni sai ita” Mutuwar tsaye ta yi a gurin ta, kamin ta juyo ta kalli Siraj da ya shigo yanzu. “Miya faru kuma? Zinatu go and call doctor please” Kainta kaɗa sannan ta juya ta fice jikinta a sanyaye. Siraj ya nufo Jibril yana faɗin “Be kamata ka tada hankalinka akan wannan gayen ba” “You don't know what Love is you have no idea how i feel so karka faɗa min wannan maganar” “Ina ƙoƙarin faɗa maka wannan gayen be isa ya ƙwace Nawwara daga hannunka ba har sai idan kai ka so” “Kasheshi zan yi Siraj babu wanda ya isa ya so Nawwara sai ni kaɗai ne wanda Nawwara zata so sai ni” Siraj ya kai hannu ya dafa ƙirjinsa. “Baka buƙatar kashe shi, sai idan kasheshi zaka yi da ranshi babu wanda ya isa ya yi gasa da kai Jibril sai idan ka so” Wata kujerar da ke gefe Jirbil ya nufa ya zauna yana ta sauke ajiyar zuciya, wani haushi yake ji da baƙincikin da be shaƙe Mustapha ba. *** *** *** Misalin huɗu da rabi ina zaune tsakar gida ni da Inna muna tattauna abunda ya faru a ɗazu. Kamar daga sama sai muka ji sallamar Zinatu daman na ji tsayar mota a waje sai dai ban ɗauka mai motar nan zata shigo ba. Na yi mamakin yadda na ganta fuska a sake kamar ba ita, cike da walwala ta gai da Inna sannan ta kai min duka irin na wasa. “Ke ƴar gari gurinki na zo” Cike da mamaki na tashi ina dariya na nufi ɗakinmu sai ta biyoni, bayan ta zauna saman katifar mu sai na fita na ɗebo mata ruwa na dire mata gabanta. Sai ta ɗauke ruwan ta maiyar gefe ta fuskance ni ta ce. “Nawwara ranar da kika mari Ogan mu, abun ya ban mamaki, abu na biyu kuma ya matsa akan yana son ki dawo aiki wai sai ya mugun wulaƙantaki, shine na ke son na san wace irin gaba ce a tsakaninku har haka duk da yake na ji ya kiraki da matarsa amman abun ya ɗaure min kai” Murmushi na yi a zuciyata ina cewa ki ce gulma ce ta kawo ki kenan. A fili kuma sai na ce “Babu wata alaƙa fa, kawai ya taɓa hannuna ne ni kuma bana son yadda
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119