Chapter 27
Chapter 27
yi rashin uwa har abada...! Ƙanwar Bilal ta biyu ce Zulaihatu ta shigo tana kuka sai ta kama hannuna. “Taso muje gida Bilal ya ce na zo da ke” Bana iya uh bale uh uh tana jan hannuna na bita kamar babba da yaro ina ƙwalla ita kuma tana kuka, har muka isa gidansu. Gidansu Bilal irin babban gidan nan ne mai yalwa amman ba sosai ba, ba kuma irin na masu kuɗi ba na masu rufi asiri dai-dai gwagwado, gidane da ke cike da ƴan mata daga ƙanensa da kuma cousins ɗinsa da ake riƙo gida wasu saboda suna makaranta a sokoto wasu kuma zaman ne kawai, sai kuma Mahaifiyarsa da kishiyar mahaifiyarsa, da ƙanwar babansu wato Gwaggo Rabi. Sun tausaya min sosai sun nuna kulawarsu a kaina, daga iyayen har ƴan matan da suke gida, a falon kishiyar mamansu aka fara shiga da ni na zauna sai kuma wata cousin ɗinsa ta shigo ta fita da ni zuwa ɗakin Bilal dake can gefen ɗakunan mazan gidan kuma a farkon shigowa gidan. Kamshin turarene ya fara yi mana murhbun sai kuma lallausan carpet, ya gyara ɗakin kamar na mata komai akan tsari kamar na wani babban mai kuɗi. Wutar daƙin da kunna duk da kasancewar ɗaya da rabi na rana ya yi. A saman gadonsa ta zaunar da ni har ta juya sai kuma ta juyo ta dawo ta kwantar da ni saman gadon kaina akan matashin kai, sannan ta ce “Ya Bilal ya ce a kawo ki nan saboda gudun hayaniya” Ta juya ta fice. Ƙaton hoton Bilal da ya yi da Noor nake kallo, a zahiri hoton na ke kallo amman hankalina yana can gurin Habiba da Inna. Zuwa can na lumshe ido bachin wahala ya yi gaba da ni. Ko da na farka dishi-dishi na fara gani kamin na ga dai-dai, Bilal ne zaune gurin kaina idonsa na kaina Noor kuma na bayana yana bachi sai faman sauke ajiyar zuciya yake yana wani ɗaukar numfashi, da alama ya yi kukan ne har ya gaji. Kallo kallo muka riƙa yi ni da Bilal ni na kasa tashi daga kwance da nake, shi kuma ya gagara motsawa har sai da yaga idona ya fara zubar da ƙwalla. Sai ya yi saurin kai hannunsa for the first time ya riƙa ya tayar da ni zaune, babu wani kuzari a jikina ko ƙire ji na ke kamar ba ni ce ba, fashewa na yi da kuka sai ya yi min masauki a ƙirjinsa ya rungume tsantsan. “Shiiiiiiiii” Rarrashina ya ke amman ji nake kamar yana ƙara min ƙarfin kuka, ban lura da shafa baya da yake alamar rarrashi ba sai da kukan ya tsagaita min, sai na yi saurin barin jikinsa na miƙe tsaye, shi ma ya miƙe tsaye yana kallona. “Ina zaki je?” Ban iya amsa masa ba na juya ina kuka, sai ya y hanzarin kai hannu ya juyo da ni ya rumgume a karo na biyu, a nan na rushe da kuka muka durƙushe da a ƙasa tare ni ina kuka shi kuma yana hawaye suna sauka saman kaina. Wata irin natsuwa da kwanciyar hankaline suka ziyarce ni, na ji daɗin rumgumar da ya yi daman i need some shoulder to cry, har ga Allah na san ba dan wani abun Bilal ya rungume ni ba sai dan rarrashi da kuma tausayi, hakan yasa na sake jiki na yi kuka iya yadda zan iya sannan yasa handkerchief ɗinsa ya goge min fuska yana shafa saman kaina kamar wata yarinya. “Shiiiiiii karki tashi Noor, daker na samu ya yi bachi” Gunɗe bakina na yi na lumshe ido ina sauraren bugun zuciyata, yanayin Bilal yana min kamar na tsohon mijina wato Margayi Faruk, yau a bayar tafiyarsa wani namiji mai natsuwa da kamala ya rumgume da har na samu natsuwar da na kasa samu a farkon aurena, sai dai wannan ba da ijiya uku ya rumgume ni ba. Tuna wannan yasa na yi hanzarin barin jikinsa, duk yadda ya so ya tsayar da ni sai na ƙi a dole ya biyo bayana yana min magana amman ban kula shi ba har na bar gidan. JUMMA'AT MUBARAK...😘 *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 2⃣0⃣ I dedicated this chapter to each and every RAI BIYU fan's, especially RAI BIYU CONVERSATION and RAI BIYU FAN'S GROUP together with KHADEEJA CANDY NOVELS. Thank you so much for your lovely and meaningful Comments. Son So Fisabilillah 😘 •••~••• Ko da na isa gida na tarar ƴan'uwa da masu karɓar gaisuwa suna Sallah la'asar, ashe huɗu ta yi ni ban ma sani ba kasancewar na kwanta ne a lokacin da ba a fara zuwa masallaci ba. Ba zan iya kwatantan yawan mutane da na tarar a gidanmu ba, daga ɗakinmu har ɗakin Inna da tsakar gida cike ya ke da ɗan adam, hakan ya tabbatar min da an kaita gidanta na gaskiya kenan. Duk yadda na so na danne kukana sai na kasa saboda raunin zuciyata, kuka na ke haƙuri ake ba ni amman kamar wuta da fetur na zama, haƙuri na ƙara min kuka, daker mutaneɓ suka rarrasheni har wasu suka samu damar yi min gaisuwa, da yawa na ji suna faɗar dole zan yi kuka saboda shaƙuwar da ke tsakaninmu da Habiba. Bana iya kwatanta yawan mutane da ke ta zuwa gaisuwa ba, tsakanin ita da Baba bana iya banbance waya fi yawan jama'a, tun daga maza har mata, ta samu addu'ah da yabo sosai, kowa ya ji mutuwar Habiba har ma da waɗanda basu danta ba gani ko kuna jin ta rasu haka kawai babu wani ciwo. Ban tabbatar da na yi rashin ƴar'uwa ba sai da dare ya yi naga inda take kwantawa babu kowa sai matashin kanta, da kuma komatsan kayanta a gefe, ban san lokacin da na fashe da kuka ba sai kuma dariya ta biyo baya, wata ƙanwar Inna ce ta shigo ɗakin ta fita da ni zuwa ɗakin Inna, amman har lokacin ban bar kuka da dariya ba, ni kaina zan iya cewa na kusa na haukace ne a wannan lokacin. Addu'ah suka riƙa min suna tofa min har sai na dawo ina kukan kawai babu dariya, kuka ne ya saka Inna kuka, ni da ita aka rasa mai rarrashin wani. Ni da Inna ba mu runtsa ba sai dai ƙannenta ne suka samu suka yi bachi, ni kuma na tashi na raya dare ina tayi ma Habiba da Baba addu'ah da kuma Faruk, sai mutuwar ta dawo min ta yi min tsaye, duk mutanen da suka da muhimmanci a rayuwata ina ta rasa su. Ka rasa mahaifina sai kuma na ƴar'uwata, na rasa RAI BIYU masu muhimmanci a rayuwata, kuma duk a cikin shekara ɗaya. Har aka yi kwana ukun Habiba aka gama bana aikin komai sai kuka, bana iya cin komai sai ruwa, a wannan babin kan na yarda Inna ta fini tawwakkali domin da kanta tana kan zauna na bani haƙuri tana min maganganu masu tausasa zuciya, amman na kasa jurewa wannan ƙaddarar kan na saka ɗaukarta, a kowa ne dare gani nake kamar Habiba zata dawo, bana da mafarki sai nata, da naja numfashi na sauke addu'ah nake mata, ƙiriƙiri bachi ya gagareni duk dare bana iya bachi har garin Allah ya waye, wani lokacin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119