Chapter 65
Chapter 65
wace fuskar zan kalli Bilal shi kuma wane irin tunani zai min.? JIBRIL POV. He's just can't believe Nawwara tana ƙarƙashinsa a yanzu, wani irin daɗi yake ji yana ta yi ma Allah hamdalla, cike da so da ƙauna yake kurɓa tea da ta haɗa masa yana wani lumshe ido. Jin ya yi ba zai iya jure jin wannan farincikin shi kaɗai ba, ya ɗauki wayarsa ya danna number Siraj dan labarta masa. *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy *Dedicated to My Asmee* 3⃣9⃣ Ba ni da wani zaɓi face na bashi damar shiga, domin nasan komai dare daɗewa dole zai sani. Kamar yadda Rabi ta nuna a wacan karo haka na danna sai ƙofar ta buɗe masa, a ta biyu mai gilashi muka riƙa kallon kallo ni da shi. Ƴar ƙaramar danjar sai tsuwa take tana nuna min agogon hannunsa da pose ɗin kuɗinsa sai kuma takardun da ke hannunsa. Ban damu da ce masa ya aje ba na sake dannawa ta buɗe ya shigo yana ta kallona kamar wanda be sanni ba. Hanzarin miƙewa na yi tsaye Cikin yanayin damuwa na zan masa magana sai ya rigani “Takardun nan zaki kai wa oga ya saka hannu” “Na yi ta kiran wayarka ban samu ba, miyasa ka kashe wayar” “Zamu yi maganar anjima let's do this now” Yawun bakina na haɗe kana na ɗaga masa kai sannan na karɓi takardun kai tsaye na nufi office ɗin Jibril duk kuwa da kasancewar ya yi min gargaɗi ɗazu akan na daina shigowa ba noticing, waya na tarar yana yi fuskarsa shimfiɗe da farinciki tea da na haɗa masa yana hannunsa sai kurɓa yake, yana ganina sai ya yayi hanzarin yanke wayar ya kalleni, sai dai be ce min komai ba jira yake ni na fara masa magana. “Hannu zaka saka a waɗannan takardun Bilal ne ya kawo” Na faɗa kamar mai shirin yin kuka, domin har ga Allah ban jidaɗin yadda na ga fuskar Bilal kamar baya cikin farinciki. Saman tebur na aje masa takardu sai ya duba ya saka hannu sannan ya miƙa min. Ni kuma na karɓa na juyo jiki ba gwari na miƙawa Bilal takardun sai ya karɓa yana faɗin “Congratulations” Ni dai ban ce masa komai ba har ya juya ya isa gurin ƙofar sai ta buɗe masa da kanta ya fice. Faɗuwa na yi saman kujera da ke kusa da ƙofar ta zaman baƙi ina sauke ajiyar zuciya, har ga Allah na san dole ne sai Bilal ya zargeni amman ta yarda zan fahimtar da shi ne aiki tasowa na yi na dawo saman saman kujera ko kuma na ce kujerar office ɗin na zauna zuciyata a jagule, ina ta tunani mafita sai bachi ɓarawo ya yi gaba da ni. Babu komai a mafarkina sai Jidda da Mustapha, wai ya mata fyaɗe kuma ya kasheta ga ƴan sanda da mutane cike a gidansu, ni kuma sai aikin kuka na ke ina kiran Mustapha, abunda ban sani ba ashe har a fili na ke kiran sunansa. “Mustapha...” Abunda na furta kenan daga farkowatawa, sai na ga Jibril tsaye a kaina yana kallona, hakan yasa ni saurin zabura na tashi. “Me zaka min?” “Me kike tunanin zan miki? Mayaudariya kina spn Mustapha kina yaudarar Bilal ko?” “Ina ruwanka babu ruwanka da rayuwata” Sai ya mire baki tare da ɗaga kafaɗunsa sama alamar abun be dame shi ba. “Tashi muje meeting, baki da aiki sai bachi abunda ya kamata ace ke zaki faɗa min lokacin meeting ɗin ya yi amman wani ne daga can waje yake sanar da ni” Na tashi tsaye idona kan agogon office ɗin da ke nuna ƙarfe goma sha ɗaya na safe, shi ya fara fita ni kuma ina binsa a baya har muka shiga Lifter, a nan ya miƙa min ƙaramar jakar da ke hannunsa. “Kin duba akan me zamu yi meeting ɗin?” Na girgiza kai alamar ban sani ba, sai kawai ta cigaba da kallona ko kunya baya ji, ni kuma na yi kamar ban ganshi ina ta kallon numbobin lifter, sai dai haka be sa ya ɗauke idonsa daga kallon da yake min ba har lifter ta tsaya a hawa na uku ta buɗe da kanta, sai na yi saurin fita duk da ban san inda zamu shiga ba, sannan shi ma ya fito sai ga Rabi ta tare mu ta karɓi layin wayata wai zaa saka min numbobin ƴan ƙamfanin ta yadda zan gane duk wanda ya kirani. Ko da muka shiga ɗakin taron mun tarar da mutum biyar wannna abokin nasa Siraj sai kuma Zinatu da wasu ɓakin fuska uku, yana shigowa duk suka miƙe tsaye ya miƙa ma baƙin fuskar hannunsa suka gaisa sannan ya gabatar musu da ni. Ɗaya daga cikinsu ne wanda na ke zaton ba musulmi ba ne ya miƙo min hannu dan mu gaisa yana faɗin sunansa. “Divid Sam” Sai Jibril ya yi saurin miƙa masa na sa hannun a ƙaro na biyu, ya kuma amsa masa kamar ni ɗin. “Nawwara” Ni kuma na zauna a kujerar da ya nuna min, ban maida hankalina kan abunda suke tattaunawa ba, sai dai hakan be hanani fahimtar cewa wani kamfanine yake son siye, har aka yi meeting ɗin aka gama Siraj da Zinatu idonsu na kaina duk wani motsi da nake suna kallona har na soma jin babu daɗi. Tare muka fito daga ɗakin taron sai ya koma daga bayana yana kallon tafiyata, hakan yasa ni ƙara sauri na shiga tifter, sai da tana daf da rufewa sannan ya ƙaraso ya shigo, still yanzu ma idonsa na kai, da alama dai kallona daɗi yake masa, ko kuma yana min ne dan kawai na tsargu, sau ɗaya na ɗago na kalleshi sai yayi min kwarjini sosai na yi saurin sadda kaina ƙasa ban sake kallonsa ba har Lifter ta sauke mu a hawa na biyar, har na miƙa jiki na fita sai ya riga fita. “Baki iya competition da ni” Ya furta daidai lokacin da zai fice, a nan na kalli bayan kansa sannan na fito muka doshi office ɗin, da fari na tsaya tunanin wa zai buɗe mana tun da ba mu bar kowa a ciki ba, muna isa sai kawai naga wata ƙaramar na'ura tana ɗaukar fuskarsa, sai ƙofar ta buɗe masa ya shiga, ina zuwa na shiga sai wani jan layi ya shata yana ta ƙara. “Ki tsaya a nan karki raunata kanki, ba zaki iya shiga yanzu ba saboda bata tantance fuskarki ba” Bayan ya shiga ciki da kamar minti biyu sai ƙofar ta buɗe min. Ina shiga ya jawo ni gaban computer ta ɗauki hotona ya saka sunana sannan ya juya ya shige Office ɗinsa. Ina zaunawa idanuwa suka kai kan agogon Office ɗin na ga ɗaya da kwata, lokacin Sallah azahar ya yi, wata ƙofar da ke cikin Office ɗin na nufa ina taɓawa sai ta soma ƙara tana nuna min na saka password, ta biyu kuma ina turawa na ga toilet, daman shi na ke nema, alwala na yi na fito na d8ba ko'ina na gurin babu carpet ɗin Sallah sai na shimfiɗa ɗankwalina na yi dashi bayan na gama, na nufi Office ɗinsa dan tunatar da shi lokacin Sallah ya yi. Zaune na sameshi yana ta aiki a system ɗinsa, kamar jira
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119