Chapter 98
Chapter 98
yanzu ba zan sake bari wata alaka ta shiga tsakanina da Jibril ba da har zata sa Bilal ya zargeni. Na dade a kwance kasancewar yau weekend har su Noor da Jamila suka dawo daga islamiyar safe ban tashi ba ba dan kuma ina bachi ba sai dan ina jin jikina da rayuwata babu dadi, ina son na labartawa Inna sai wata zuciyar ta hanani saboda na san ba komai ya kamata ace iyaye sun sani ba musamman a abunda ya shafi fada a tsakanin ma'aurata ko kuma masoya, har sai idan ya kai ya akwo mun kasa shawo kan abun. Wayata na dauka na aika masa da sakon barka da safiya amman be maido min da amsa ba, hakan yasa na kirashi sai be yi picking ba. Tashi na yi na fita tsakar gida na gyara ko ina sannan na shiga na yi wanka na shirya cikin bakar abaya, Inna ma ta kula da yanayin da na ke cikin na rashin dadin rai, sai dai bata min magana ba, wata kila ta fahimci akwai abunda ya shiga tsakaninmu da Bilal jiya da dare saboda na dawo ina kuka duk da kasancewar ta tambaye dalilin kuka na ki fada mata. Misalin sha daya da rabi Bilal ya kira ni ina picking ya ce “Ki shirya ma Noor gani nan zuwa” “Tau, har yanzu fushi kake da ni ko?” Sai kawai ya kashe wayar, ni kuma na ja dogon numfashi na sauke na tashi na fita. Ko da sha biyu ta yi da kwata Bilal na kofar gidanmu yana jiran Noor, ban san miyasa ba na samu kaina da rashin jindadin fitar shi tare da Noor duk da sun saba fita amman yau ina jin daban gashi gabana sai faduwa yake, wata kila saboda bana cikin dadin rai ne ko kuma wani abun ne daban oho. Da kaina na riko hannunsa na kaiwo shi kofar gida, saiga wayar da ke hannuna ta yi ringing Jibril ya kira, daman yakan kira da safe ya yi waya da dansa haka ma da dare idan zai kwanta sai dai yau yayi ranar kira domin har sha biyu ta gota ko da yake yasan yau weekend ne Noor baya suwa school. A nan na mika masa wayar ya gaisa da Jibril sannan Bilal ya rika hannunsa ba tare da yace da ni komai ba suka tafi Noor nata dariya yana dago min hannu. Cikin gida na dawo na dora girkin rana, sannan na dauko tufafin Inna da suka yi datti muka soma wankewa ni da Sakina muna fira sama sama, sai dai faduwar gabana na ta karuwa, ina jin kamar na yi kuka kuma ba dan a min wani abun ba. Da la'asar Jibril ya aiko da dare bansa a daukar masa Noor sai na fadawa direban cewar basu dawo ba, daman idan suka fita wani lokacin har isha'i suna kai wa basu dawo ba, direban na wuce da kamar minti biyar sai ga Bilal ya kirani a waya hankalinsa a tashe. “Nawwara Noor ya dawo?” “Aa kun dawo ne?” “Bayan fitar mu be dawo ba?” “Aa be dawo ba, lafi... ” Kamin na tambaya ya kashe wayar, ni kuma jikina ya yi sanyi na soma ambaton Allah a hankali “Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un” [11/10, 6:59 PM] Farar Mace...: *RAI BIYU...♥🖤* Wattpad @KhadeejaCandy 5⃣3⃣ Jina yi kamar bana da karfi a jikina na kasa shanyar da na ke, sai na zauna a gurin gabana nata faduwa. “Nawwara” Inna ta kirani saboda ta lura da yanayina, sai na kasa amsa mata saboda kukan da ya cika min zuciya nasan ina bude bakina zai fito. “Lafiya miya faru? Dawa kike waya?” “Bilal ne, tambayata yake wai Noor ya dawo” Na fada ina ta kokarin danne kukana. “Kamar ya? Ba tare suka fita ba” “Tare suka fita” “Amman shine zai kira ya tambaya ya dawo bayan kuma ya san tare suka je? Wane irin rainin wayo ne wannan?” Cewar Sakina tana matse zanen Inna. “Wata kila wani abun ne ya faru, ina ji jikina ba dadi” “Tun jiya na lura da ke sai dai nasan matsalar bata wuce tsakaninki da Bilal ba shiyasa ban yi magana ba, sabodana bana son ina yawan shiga fadanku, amman babu abunda zai faru da Noor Inshallah” Ajiyar zuciya na sauke ya share guntun hawayen da ya zubo min na tashi na koma bakin kofar dakinmu na zauna, Sakina ta cigaba da wanke kayan. Haka muka zauna shiru har aka kira magariba Bilal be sake kirana ba gabana kuma be daina faduwa ba. Bayan na sallah isha'i na dauki waya na zimmar na kira Bilal sai kuma nake ganin rashin dacewar hakan, saboda ya saba fita da Noor su kai har dare basu dawo ba, dan me yanzu zan soma kiransa ai sai ya zargeni yace ko dan munyi fada ne, haka na maida wayar muhallinta na aje, kamar Inna ta san abunda ke raina sai kawai na ji ta ce “Karki ji kunyar kiranshi Nawwara, ki kirashi mana ko muma hankalinmu zai kwanta” Ba musu na daga wayar na kira number Bilal amman har ta gama ringing be dauka ba, haka na jera masa kira hudu be daga ba, daga baya kuma sai naji wayar a kashe, hakan ya kara fadar min da gaba, ina kokarin fadawa Inna cewar wayarsa a kashe take sai ga sakon Jibril ya shigo. _Nawwara Noor ya dawo? Ina son gani dana zan aiko da mota yanzu_ Ni kuma na yi saurin mayar masa da sakon cewa basu dawo ba, sai ya sake aiko min da wani _Dan Allah karki shiga tsakanina da dana Nawwara na roke ki, kiyi min duk abunda zaki min amman karki hana min Noor_ _Idan sun dawo zan fada maka_ _Gani nan zuwa na dauki dana_ _Aa karka zo_ Bw sake cemin komai ba, nasan be yarda da ni bane yana ganin kamar ina kokarin hana masa Noor ne. “Inna na ta kira na kira be daga ba daga baya kuma sai aka kashe wayar” “Allah dai yasa lafiya” Cewar Inna ni kuma na amsa da Amin, kamin mu hada baki gurin amsawa Jidda da ta shigo a yanzu kamar marar lafiya, ina kallonta na san ba lafiya ba, sai dai ban kawo cewar maganar Noor bane saboda a tunani bata san sun fita ba. Kasa gaisawa ta yi da Inna sai kawai ta sakar min ido hawaye ya soma mata zuba “Ke lafiyar ki?” Na tambaya ina dafata. “Nawwara” Sai kuma ta yi shiru kamin ta cigaba. “Dazu da Bilal ya fita da Noor wai ya tsaya da shi a AGG MALL ya siya masa chocolate shine sai yaga wani abokinsa suka tsaya gaisawa, wai Noor ya fito daga ciki ko da suka gama gaisawan ya nemeshi ya rasa” Nina mike tsaye da sauri Inna kuma ta dinga furta “Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un” Sakina kuma ta dora hannu saman kai tana kiran “Mun shiga uku” “Yanzu ina shi Bilal din yake?” Inna ta tambaya hankalinta a tashe. “Yana can gidansu, wai besan yadda zai fada muku ba shiyasa be zo ba tun dazu, nima yanzu yake fada min kuma ya ce ya bada report gurin yan sanda da gidan radio” Ni dai ban iya cewa komai ba ban da hawayen da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119