Chapter 80
Chapter 80
na san za a rina saboda ya tsargu da yadda na nunawa Bilal kulawa kuma ina ta masa kalamai masu dadi a gaban idonsa, sai dai mai? Ai be isa ya hana Bilal zuwa ganin Noor ba ko dan na bashi dama ya wuni da shi ya bashi damar samun guri har ya fada min wannan maganar? Bana son na yi wata magana a gaban Noor saboda kar ya fahimci wani abu, wannan yasa na kumde maganar da ke bakina har sai ya fita na bishi na fada masa. Turo kofar da aka yi aka shigo ne yasa dukanmu muka kalli kofar Mustapha ne ya shigo cikin manyan tufafi tare da manyan ledoji Jidda na gafensa. [11/8, 9:37 PM] +234 703 352 5246: *RAI BIYU...♥🖤* Wattpad @KhadeejaCandy 4⃣5⃣ MUSTAPHA POV. Mustapha ya yi farincikin tararda Jibril da ya yi a dakin ko ba komai yasan Jibril ba zai jidadi ba, a farkon shigowarsa ya shigo da fargaba da kuma tunanin irin kallo da wulakancin da Nawwara zata masa, amman ganin Jibril ya sashi sakewa kamar daman can sun saba da Nawwara. Murmushin fuskarsa ya fadada ya kunno kai cikin dakin tare da Jidda yana kallon Nawwara. “Pretty ashe Babynmu babu lafiya, Wallahi ban sani ba sai jiya ya jikinsa” Sai da Nawwara ta hadiye yawu sannan ta amsa masa fuskarta ba yabo ba fallasa. “Da sauki” Kana ta watsa ma Jidda harara. Kamar be san an hallici mutum a gurin ba haka ya bi ta kusa da Jibril ya karasa kusa da Noor ya dire ledodin da ke hannunsa. “Cute Boy waya kade min kai” Noor ya dade yana kallonsa kamin ya amsa masa bakinsa da nauyi. “Nima ban san shi ba” “Am sorry dear” Ya fada yana zama kusa da shi tare da duba hannun sai kuma ya juyo ya kalli Nawwara. “Pretty amman da sauki sosai ko?” Nawwara kamar ba zata amsa shi sai dai ganin Jibril yasa ta karaso gurin tana fadin. “Eh a hannu kawai ya kare” “Wallahi ban sani ba sai dazun nan Jidda ke fada min” Nawwara ta kalli Jidda sai Jidda ta dan zaro idon tana daga kafadarta. “Ya matsa ne sai ya ganki kin san yadda yake damuwa” “Sorry na zo ban fada miki ba” “Ba komai” Cewar Nawwara. Jibril ya rumtse ido ya sauke ajiyar zuciyar da ta mamaye masa kirji, sai ya juyo cikin facin rai ya ce. “Ya kamata ku tafi yanzu, amman kai yaron nan i warning you karka sake shiga sabgar Nawwara ko ban fada maka ba” Daga Nawwara har Mustapha da Jidda kallonsa suke. “Waye wannan daman ka san shi ne?” Jidda ta tambaya tana kallon Mustapha, sai Jibril ya yi cikinta kamar zai dake ta. “Babu ruwanki a ciki” Matsawa baya Jidda ta yi ganin yadda temper dinsa take, sai Mustapha ya taso daga inda yake zaune kusa da Noor yana murmushi ya karaso daf da Jibril ya soma gyara masa kwalar rigarsa. “Ka kwantar da hankalinka Man, macece fa ba namiji ba kasan namijin da ya amsa sunansa namiji baya taba dukan mace, ko da yake kai ragon namiji ne, shiyasa kake duka kuma kake cin zarafin yarinyar nan marainiyar Allah, anya babu kai a cikin kashe mata mahaifi kuwa? Saboda na ga ka tsawwalla rayuwarsu ne da yawa ka siye gidansu... oops sorry na manta she's your ex...- ” Ya karashe maganar yana murmushi. Jibril ya daga hannu cike da hasala zai naushi bakinsa sai Mustapha ya rike hannunsa cikin zafin nama ya kai masa na shi naushin a baki har sai da Jibril ya yi baya baya ya rike bakin. “1-1” Mustapha ya fada yana murmushin keta. Sai Nawwara ta katsa musu tsawa. “Miye haka? Ya zaku rika yin abu kamar kananan yara?” Murmushi Jibril ya yi ya kallon Noor da duk tsoro ya gama mamayeshi ya ce “Wasa ne fa kawai karki daga hankalinki, amman ki fada masa karya sake zuwa kusa da yaro na” “Ba dan ka na zo nan ba dan Nawwara ne, duk kuma abunda ya shafi Nawwara dole ne ya shafe ni” Jibril be kara ce masa komai ba, domin yasan wani furuci na fitowa a bakinsa ba mai dadi ba ne, kuma baya son ya yi abunda be kamata ba a gaban dansa, sai kawai ya karasa kusa da Noor ya zauna yana shafashi tare da fiddo wayarsa ya kunna masa game. “Mu zamu koma, daman na zo ne kawai ganin Noor Allah ya tsare gaba” “Amin” Cewar Nawwara, sai Jidda ta daga mata hannu. “Zamu yi waya” “Ok thanks” Suna fita Mustapha ya fara tambayar Jidda labarin Jibril, sai dai bata fada masa komai ba saboda tana tunanin sirrinsu ne ita da Nawwara, but itama tana mamakin yadda aka yi Nawwara ta hakuru har haka ta bari ya zo ganin Noor. “Amman shi Nawwara take so ko?” Mustapha ya tambaya yana driving, sai Jidda ta kalleshi. “Bata son shi, ni dai iya sanina Nawwara Bilal take so” Kamar zai sake cewa wani abu sai kuma ya yi shiru, sai dai ransa yau yana cike da farinciki saboda abunda ya yi ma Jibril. A bakin kofar gidansu Jidda ya sauketa sannan ya juyo ya dawo gida. Tun a yanayin shigowarsa ya tabbatarwa da Momynsa yana cikin farinciki, Daddy sa ma ya lura da hakan kasancewar dukansu suna zaune falo ne har su Ikram da Zarah suna kallo harin da aka kai Iraq a channel din Al Jazeera. “Dad Mom barka da dare” Sai da suka amsa masa sannan ya zauna saman cushion yana kallon tv kamar yadda suma suke kallo, sai dai ko kadan hakalinsa baya gurin yana can gurin Jibril tunanin halin da Jibril zai kasance kawai yake yana murmushin da be san ya fito masa ba. “Son lafiya kake wannan far'ar?” Ya kalleta kamar be san ya yi ba. “Ba komai, but Mom Dad ya kamata ce kunje ganin yaron Nawwara ya samu accident” “What...?” Dadynsa ya fada. “Mu zaka fadawa muje mu duba yaron Nawwara? Hajiya baki fada masa ya fita harkar yarinyar nan ba? Daman yana nan akan bakansa?” Momy ta yi saurin dagawa Dadyn hannu. “Komai da sannu ake binsa kasan halin Mustapha” “Babu ruwana da wani halinsa, ka var ganin kai kadai na haifa zan iya shafe labarinka a doron kasa matukar ka ce zaka auri yarinyar, ka dauki kanka a matsayin matacce matukar ka tsaya kai da fata akan yarinyar nan” Mustapha da zuciyarsa ke boiling gumi ya zubo masa ya bude bakinsa da ke rawa ya ce “Daddy ina son yarinyar nan...” “Baka san so ba Mustapha, taya zaka so mace da ta auri namiji biyu kuma ta haihu? Kuma in banda haukarka macen da kayi ma kanwarta fyade zaka ce kana sonta kuma da aure? Kana tunanin zata aureka ne? Kana batawa kanka lokacin ne kawai, kuma na fada maka karna sake jin maganar yarinyar nan a cikin gidan nan, ka nemo yar kowa zan aura maka amman ban da ita” Yana gama fadar hakan ya mike tsaye ya kabe babbar rigarsa cikin bachin rai ya fice, sai Momy ta matso kusa da Mustapha tana kokarin yi masa bayani “Look son.. ” “No Mom ke kika ce min Dady ya yarda da maganar yarinyar nan, ashe ba
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119