Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 42

Chapter 42

Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

what he did to her’ Shine abunda ke ta masa yawo a cikin kai, zuciyarsa na wani irin zafin, sai goma har da kwata sannan na bar bathroom ɗin cikin yanayi marar daɗi. Vest ya saka da ɗan guntun wando, be shafa mai ba amman ya shafa turare, sannan ya fito parlour ya haɗa ma kansa tea ya zauna saman cushion yana kallon hoton nawwara Tea ma sai ya gagara sha. Yana zaune gurin har shaɗayan dare ta buga be ko motsa daga inda yake ba. Siraj ne ya turo ƙofar falon ya shigo hannunsa riƙe da takardu masu yawa, ɗakin karatun Jibril ya nufa ya aje takardun sannan ya dawo ya zauna kusa da shi yana faɗin. “Gaskiya yau Jibril ka bani mamaki, wai su waye iyayen yarinyar nan ne da har zata wulaƙanta a gaban jama'a ka ƙyaleta?” Sai a yanxu ya gincira saman kujerar yana cigaba da kallon hoton Nawwara. “Maruƙar haka zai sa ta yafe min, zan jure har sai ta yarda da na yi nadama kuma na tuba” “Wannan ba revenge ba ne, it's an embarrassment, ko ma mi kayi mata baka cancanci ta yi maka wannan tuzarcin ba, su fa mata ba a ƙyalesu hakan ya bata damar cigaba ne, gaba ɗaya yau ak kamfanin nan kai aka wuni ana magana wannan ai tozarci ne” Murmushi Jibril ya yi ya kalli Siraj ya ce. “Data mareni a gaban mutane na ji yadda ta ji a lokacin da na mareta airport, na ji yadda ta ji a lokacin da na mareta a gaban iyayena, na ji yadda ta ji a lokacin da na mareta a bakin titi na jefar da ita na yi tafiyata, at least now na san yadda mutun yake ji idan aka disgashi gaban jama'a” Siraj ya juyo yana fuskarta shi da kyau ya ce. “Kana da banbanci da kowa Jibril be kamata ka auna kanka da sauran jama'a ba, weather you like or not abunda yarinyar nan ta yi maka bata kyauta ba” Miƙewa Jibril ya yi tsaye ya nufi window falon yana faɗin. “You're my new tight friend Siraj, bana son kana faɗar wata kalma marar daɗi a kan nawwara, saboda hakan zai sa na tsane ka ita kuma na ƙara ƙaunarta, zan iya jure ko wani kalar wulaƙanci daga Nawwara matuƙar hakan zai sa ta yafe min, soyayyata da ta rasa a can baya ita nake son nuna mata a yanzu, kulawar da na gagara bata a da, ita na ke son bata a yanzu. Na wulaƙanta yarinyar sosai Siraj irin wulaƙanci da ban taɓa tsamanin Allah zai jarrabeni da son kamar haka ba, a gaban idonta na ke shigowa da budurwa a gidanta kuma ta dafa mana abinci ta haɗa mana ruwan wanka, ta san fasadi muke aikatawa amman haka be taɓa damunta ba, ko da yana damunta bata taɓa nuna min ba. Idan ta dafa abinci sai ta kawo min tana jiran na yaba mata amman sai na kushe wani ko ci ba zan ba, idan ta yi kwalliya tana jiran na yaba mata ba zan kalleta ba, ban taɓa riƙa hannunta da nunan sha'awaba sai idan zan hukunta ko kuma na doketa, idan mahaifina ya tambayeta ko akwai wata matsalar sai ta ce masa babu komai muna zaune lafiya...” Hawaye ya zubo masa sai yasa gefen hannunsa ya shafe yana cigaba da kallon titi kasancewar window yana fuskantar titi ne. “Lokacin da na gano tana da ciki, sai na saka mata maganin bachi a lemu ta sha, da tayi bachi sai na cire mata tufafi na ɗauki hotonta na kai ayi editing aka haɗa da na wani, da gangan na sa aka ɗauko min mahaifinta aka zo da shi garin abuja na tarasu da mahaifina na ce cikin da ke jikinta ba nawa ba ne ga wanda ya yi mata shi nan, i'm very fool Siraj can you imagine na ɗauki hoton mamata na haɗa da hoton wani saboda kawai bana son ta kuma ban shirya haihu da ita ba a wannan lokacin...” Ya zuba hannayensa aljihu hawaye na ta masa zuba, sannan ya sauke ajiyar zuciya. “A gaban mahaifinta da mahaifina na nuna waɗancan hotunan kuma na ce na saketa saki uku, sai mahaifina ya ce min saki uku idan aka yi su a take a matsayin saki ɗaya suke dan haka na yi haƙuri na maida matana, jin wannan yasa nace na sake tsaki ɗaya tsaki biyu tsaki uku, a ranar Nawwara ta riƙe min hannaye tana roƙon na rufa nata asiri na karɓi cikin nan, wannan roƙon da ta yi min sai yasa mahaifina ya yarda cewar ba cikina ba ne. A ranar mahaifina ya tabbatar min da sai na yi nadamar abunda na yi mata, saboda yana ganin ta bi maza ne domin kawai na kasa bata kulawa, ashe da gaske zan yi nadama. Bayan na rabu da ita mace huɗu na aura suka kasa zama aure da ni, wasu basa mutunta ni kamar yadda take, wasu kuma su nuna min suma ƴaƴan manya ne ba zasu iya abu kaza da kaza ba, daga lokacin na fara kewar Nawwara, kuma duk wannan auren da nayi babu wacce ta taɓa samun ciki da ni, kuma ba dan bana haihuwaba ba dan ina da wata matsala ba sai dai isgilancin da na yi Allah ya jarrabe ni, sai bayan na yi aure na biyar ashe ita ba ɗana ba ne ban ganr haka ba sai da na auna jininsa, gudun afkawa cikin wata matsalar sai step mom ɗita ta aura min ƙanwarta, sai da tafiya ta tafi sai na gano kasheni take son yi ta ci gado tun da bana haihu ita kuma tana son haihu amman bata son fita ta bar ɗaular gidana, sai ta saka min guba a abinci shine ciwon da har yanzu yaƙi warkewa a jikina, bayan na rabu da ita na dawo na cewa mahaifina ina son naje gidansu Nawwara, sai ya ce min shi ba babu ruwansa kuma ba da yawun bakinsa ba, saboda na kunyatashi na tozarta shi kuma na ci amanarta bayan shi ne silar aurena da ita, daga ƙarshe ya ce be yafe min na taka ƙafata ƙofar gidansu Nawwara ba, tun daga lokacin sai tunaninta da halin damuwar da na saka ta ya riƙa damuna, wani lokacin na kan rufe kaina ni kaɗai a ɗaki ina kukana amman babu mai bani haƙuri saboda mahaifita bata raye. Komai nawa sai ya tsaya cak, idan naje asibiti bana iya komai sai tunani da damuwa, wannan ne ƴasa Abbah ya dawo da ni kamfaninsa na nan sokoto saboda na rage damuwa, na jidaɗi da Abbah ya yi min haka ko ba komai ni ma zan yi rayuwa garin da Nawwara ta taɓa rayuwa, lokacin da na zo na haɗu da kai, na saka nemanta sai ka ce min ta mutu kuma iyayenta ma sun mutu, daga lokacin na yafe farinciki da walwala a tare da ni.” Ya juyo ya kalli Siraj sannan ya ce “Nawwara ce kawai macce da ta samu ciki da ni ta hanyar halak, Nawwara ce kawai take kula da ni kamar mahaifiyar da ta haifeni, Nawwara ce kawai zuciyata ke ƙauna, ko a can baya ba ƙaunarta ne bana yi ba kawai dai

Table of Contents

Chapters

119 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});