Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 78

Chapter 78

Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

fito ya nufi main house jiri na dibansa, yana shiga falo na fadi a bakin kofa yana tari a wahalce gubar da ya taba ci ta taso masa ta hadu da dattin cocaine dake cikin huhunsa (lung) sai aman jini, har idanuwansa suka canja kala kamar ba zai rayu ba, gashi falon babu kowa sai shi kadai. Tun yana iya gani har ya koma yana gani dishi-dishi sai kuma numfashinsa ya soma nisa hankalinsa ya ba ce 6at. Ko da ya farka an dora masa kyalle mai sanyi saman kai, yana kwance saman doguwar kujera, Siraj na zaune kusa da shi Zinatu kuma na fuskantarsa fuskarta dauke da tausayinsa. Unkurawa ya yi ya tashi zaune sai ta yi hanzarin miko masa ruwan gora mai sanyi ya karba ya sha. “Yaushe kuka shigo?” “Tun dazu, gashi har an yi magariba kana sume, Zinatu ce ta gyara gurin kuma da taimakonta muka doraka saman kujerar nan” Cewar Siraj, sai Jibril ya tada kai ya kalleta ya ce “Thank you” “Never Mention Allah ya sauwake ni zanje gida” “Ba zaki bari na sauke ki ba?” Ta kalli Siraj da ya yi maganar ta ce “No zan je da kaina ya kamata ace ina gida by this time, ka kula da abokinka please” Daga haka ta dauki jakarta ta rayata ta fice, sai Jibril ya unkura zai tashi kirjinsa ya yi masa wani mugun tsuka hakan yasa shi saurin komawa ya zauna yana yar kara. Siraj ya dafa shi. “Ka bari ka kara hutawa mana, Jibril kana matsawa kanka da yawa akan yarinyar nan, direban ka ya fada min ka bi bayanta sai kuma na zo nan na sameka cikin jini, ka rika sassautawa kanka dan girman Allah ina tausayin halin da kake ciki” Jibril ya kalleshi irin kallon nan da shi kadai ya san fassarasa. “Miyasa ka ce min ba ni da Nawwara? Bayan kuma ina da shi” Siraj ya hade yawu da karfi. “Wane irin kana da shi? Ban fahimce ka ba” “Na ga dana da idanuwa Siraj dan da na haifa da Nawwara dan me zaka boye min?” “Wace riba zan ci idan na boye maka? Mi zaisa na boye maka? Amman ka tabbatar dan ka ne?” “Da na ne, jinina da nasa iri daya ne, kamata da tasa iri daya ce, da ace ba a kade shi ba da ba zan samu ganinsa da wuri ba” “Amman abun nan ya bani mamaki, sai gaskiya akwai wani a abu a kasa, domin wanda nasa na bincika mana ba zai yi karya ba, shi ya fada mana Nawwara bata da da ko daya, sai idan mutumen dan uwanta ita kuma ta nemi ya boye mana din” “Taya xaka yi bincike kuma ka nemi dan uwanta? Dan ina ne mutumen?” “Dan unguwarsu ne, amman abun nan ya bani mamaki amman ka bincike Nawwara ta tabbatar maka da danta ne? Shin yana ma raye?” “Yana raye wani ya kade shi da mota, and nayi duk wanda ya taba min yaro ko da Nawwara ce ba zan kyale ba” Siraj ya karkato ya kalleshi “Amman idan kaddara ce fa?” “Ban san kaddara akan da na ba, da ce ni ta mai motar ya kade zan dauka ko amman da na? No never da yanzu na rasashi fa? Kasan halin da Nawwara zata shiga ko kasan halin da ni zan shiga? Who's ever that person is i will never forgive him” Wani gumi ne ya soma saukowa Siraj, Jibril kuma ya mike tsaye yana jin zafin da kirjinsa ke yi ya nufi bedroom dinsa, saurin mikewa tsaye Siraj ya yi ya rufa masa bayan. “Yanzu ya zaka karbi danka hannun Nawwara?” “Shine abunda na ke tunani, zan yi duk yadda take so wajen ganin ta bani da na” “Ni abunda na ke tunani mai zai hana ka fara fake love da Zinatu, so that ka samu kan Nawwara kuma ka gane idan har yanzu akwai soyayyarta cikin ranka” Jibril ya kalleshi “Wani lokacin kana yin abu kamar baka san waye ni ba Siraj, am straight forward, if yes yes if no that's means no for sure” “Baka fahimta ba ne Jibril ai fake love na ce, kuma da sani Zinatu zaka yi” “Ba zan yi ba, ka tafi kawai zan samawa kaina mafita” Cikin sanyin jiki Siraj ya juya har zai fita sai kuma ya juyo ya kalli Jibril ya ce. “Cocaine...” “No please bar ni na ji da abunda ke damuna” Ya fada yana daga masa hannu, sai Siraj ya juya kunya kunya da shi ya fice. Bathroom Jibril ya shiga ya sakarwa kansa ruwa sosai sannan ya yi wanka gaba daya tare da alwala ya fito, ya saka jallabiya ya rama sallah la'asar ya yi magariba, yana saman carpet din har aka kira isha'i, bayan ya yi ya taso ya dawo parlor ya shiga kitchen ya hadawa kansa ruwan tea. Sai kuma ya dawo falo ya zauna hoton Noor kawai idanuwansa ke nuna masa, sai ga wayarsa na ringing sai a lokacin ya kula da inda wayar take gefen kofa inda ya fadi dazu. Zuwa ya yi ya dauka sai yaga number Abbah. Gaiswa suka fara yi da Abbah kamin ya rufe shi da fada. “An fada min baka da aiki sai shan cocaine, ka maida kanka wani kalar mutun, idan ba zaka iya ba zan karbe ragamar kamfanin nan na mika a hannun Siraj tun da ya fika kula” “Waya fada maka ina shan cocaine Abbah” “Kai ka fada min, kai kullum abun ka gaba yake ba baya ba” “Ka yi hakuri Abbah zan canja” “Da ya fi maka” Daga haka Abbah ya kashe wayar. A ranar Jibril be gi bachi ba sai ya tashi ciki dare yana ta sallah nafila abunda be taba yi ba a tsawon rayuwarsa, kuka ya yi sosai ya kaima Allah bukatarsa, shiriyace a cikin abubuwan da ya fi roko sai kuma Nawwara, da asuba ma bayan ya yi sallah asuba ya dora da istigifari yana kankantar da kansa yana neman Allah ya yafe masa. Washe gari ya kira wani abokinsa ya hada shi da mai tattoo ya zo har gida ya wanke masa tattoos dake wuyansa da kuma na sunan Nawwara da ke hannunsa. Bayan mutanen ya fita ya shiga kitchen ya soma kansa kwai duk da yana da kuku be nemi ya yi masa ba sai ya hada tea da kansa, a dinning room din kitchen ya zauna yana ci sai ga Siraj ya shigo, bayan sun gaisa ya zauna shima ya zuba ma kansa yana ci, bayan sun gama ya budewa Jibril cocaine. Sai da Jibril ya yi kamar ba zai sha ba sai kuma shaeidan ya zugashi ya dauka ya shaka sosai, sannan ya mike tsaye yana fadin. “Ba zanje office ba, ka yi duk abunda ya dace, Nawwara ma ba zata je ba, saboda dan mu ba lafiya” Be jira abunda Siraj zai ce ya fito daga kitchen din na nufi bedroom dinsa. Saman gado ya kwanta ya rika bachi kamar wanda ya mutu, be farka ba sai da aka yi sallah azahar. A daren ranar ma sai da Jibril ya raya shi da nafila yana ta rokon Allah ya karkarto masa da hankalin Nawwara kuma ya shiga tsakaninta da duk wani mai

Table of Contents

Chapters

119 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});