Chapter 112
Chapter 112
Ya fada cikin muryar da ke nuna rashin jindadin da ke cikin ransa. Ban masa musu ba a nan na sauko saman gadon sai ya wuce gaba ya nuna min inda bandaki yake ya bude min, na shiga ciki na yi alwala ko da na fito ya shinfida carpet da alama shi da alwalar ya shigo. Wardrobe ya bude ya dauko Hijabi ya miko min na saka sannan ya yi gaba ni kuma ina baya ya kabbatar sallah nafila. Bayan mun gama ya yi addu'a nima na yi tawa addu'ar sai juyo ya rika goshina ya soma karanta addu'ar da annabi ya koyar da mu wacce miji yake rika goshin matarsa ya karanta saboda niman tsarin da zaman lafiya. اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ خَيْرَهَا وَخَيْرَ مَا جَبَلْتَهَا عَلَيْهِ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّهَا وَشَرِّ مَا جَبَلْتَهَا عَلَيْهِ Allaahumma 'innee 'as'aluka khayrahaa wa khayra majabaltahaa 'alayhi wa 'a'oothu bika min sharrihaa wa sharri maajabaltahaa 'alayhi. Na yi mamakin jin wannan addu'ar daga bakin Jibril lallai ba da wasa ya riki karatun qur'ane ba tun da har ya iya maida hankali ga yin addu'o'i ma. Bayan ya gama ya tashi ya dauko manyan ledoji ya aje a gabana tare da plate da cups. Ni kuma na mike tsaye na nufi hanyar da aka shigo da ni wato falo. “Zo ki ci abinci mana” “Bana jin yunwa” Ita ce kawai amsar da na bashi na nufo falo na zauna, sai kuma na kasa yin kukan da na fito yi, haka na zauna a saman manyan kujerun alfamar ina ta kallon yadda aka tsara falon, ba dan ina ganin sha'awa ba sai dan na rasa abun yi zuciyata cike da tunanin Bilal. Har sha biyu ina zaune falon ni kadai kuma Jibril be fito ba. Jin na yi na tsallawa da kayan dake jikina kasancewar atamfar ta matseni sosai hakan yasa na tashi na koma dakin dan dauka wasu tufafin domin Jidda ta fada min inda ta aje min kayan da zan canja idan zan kwanta. Aabunda na tarar ya tashi hankalina sosai, Jibril ne kwance kamar matacce ga jini nan gefensa da alama amai ya yi. A firgice na kai hannu na taba shi amman be motsa ba. “Na shiga uku Jibril Jibril Jibril” Shiru be amsa ba balle ya motsa, tun ina girgizashi kadan har na fara yi da karfi ina kuka, hannu na kai daidai hancinsa sai na ji baya numfashi hakan yasa ni fasa ihu na fito a firgice falo ban san lokacin da na fito harabar gidan ina ihu ba. Ban san da akwai mai gadi ba har sai da ya taso ya nufoni yana tambayar lafiya. “Jibril ne ya suma ya ya ya mutu” Na fada cikin Matsainancin kuka da tashin hankali. Tare muka dawo dakin da shi babu abunda ke fita bakinsa sai Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, yana girgiza Jibril tare da fadin “Mai gida Mai gida” Amman Jibril be motsa ba. “Mi ya same shi” Ya tambaya yana cigaba da girgiza shi cikin tashin hankali na ce “Wallahi ban sani ba, ni ma ina falo ko da na shigo na ganshi haka” Wayarsa ya ciro ya kira wani wanda ban san ko wanene ba, cikin kankanen lokaci mutumen ya iso a nan na gane direban da Jibril yake aikawa a gidanmu ne. Tare da taimakonsa suka saka Jibril a mota nima na shiga muka dauki hanyar asibitin One On One Special Hospital. Muna isa aka karbeshi aka shiga dashi wani dakin suka shiga bashi taimakon gaggawa, sai direban ya dawo yana cewa na kira iyayensa na fada musu. “Babu waya hannuna tana hannun Mamana” “To ki kira line sai ki sanar musu idan kina da number a kai” Ya fada yana mika min wayarsa. Cikin hanzari na karba na saka numberta na kira, sai da tayi ta ringing har ta katse na sake kira sai a na uku Inna ta dauka cikin muryar bachi. “Assalamu Alaikum” “Inna Nawwara ce ni ce, muna asibiti Jibril ba lafiya ya suma ko ya mutu” “Wani abun kika masa ko?” Na yi shiru na kasa amsawa sai kuka nake. “To kin kyauta, kuma bari kiji na fada miki ko mutuwa ya yi karki kuskura ki dawo inda na ke, ki nemi wata uwar can ba ni ba fitsararriyar yarinya” Tana fadar hakan ta kashe wayar. Sai na mika masa ina kuka kamar zan hadiye zuciya na mutu. “Ki kira mahaifinsa ki fada masa” Kuka da nake ya hanani fadin bani da numbersa numfashina har gargada yake. Shi da kasan ya kira Abbah ya fada masa, kusan a tare suka iso da Inna da wasu yan uwan Inna. “Miya sameshi” Shine abunda mahaifin Nawwara yake ta tambaya, ni kuma na kasa magana saboda kuka, Inna kan ban da hararata babu abunda take. Bayan likitoci sun gama bincikensu daya daga cikinsu ya zo yana ma Abbah bayanin cewar Jibril yana da heart attack kuma da alama an bata masa rai ne shiyasa wannan dogon suma. “Zuciyarsa ta buga a yanzu, kuma an barshi ya dade ba a kawo shi asibiti ba, ban da Allah ya masa tsawon rai da yanzu ya mutu, da alama an bata masa rai ne ko kuma be samu wani abu da yake so ba ko ya rasa wani abu, so shawarar da zan baku ku yi kokarin kawarda duk wani abu da zai bata masa rai saboda in ta sake bugawa gaskiya zaku rasa shi yanzu ma sa'a ce kawai da kuma rabon shan ruwa a gaba” “Mun gode likita zamu kiyaye” Shine abunda Abbah ya fada, kallo daya ya yi min ya dauke kansa, ya nufi dakin da Jibril ya ke ya shiga, har su Inna suka shiga aka barni nan ni kadai tsaye kamar marar gata. Su Inna ne suka fara fitowa ban san ko karfe nawa a wannan lokacin amman tabbas dare ya yi sosai amman hakan be hana Inna da yan'uwanta bin daren au koma gida ba. Bayan Abbah da yayan Jibril sun fito tare da wasu yan uwansa mata na shiga, sai na tararda wasu yan uwansa a cikin dakin, sai dai ina shiga duk suka fita waje aka bar ni ni kadai. Zaunawa na yi saman kujerar dake kusa da gadon ina hawaye, sai na dora kaina saman gadon da yake kwance ina kallon fuskarsa. Oxygen ne a bakinsa sensor na nuna yadda numfashinsa ke tafiya, tausayinsa ne ya fara kamani da kuma tausayin kaina a lokaci daya... [11/19, 1:12 PM] Farar Mace...: *RAI BIYU...♥🖤* Wattpad @KhadeejaCandy 5⃣9⃣ Ina biyu aka yi sallah asuba, sai na shiga bandakin da ke dakin na yi alwala da na fito sai na shimfida dankwalina already ina da Hijabi a jikina wanda na yi sallah da shi a daren jiya, sai kawai na kabbatar sallah. Dukanin addu'a ta ta nemawa Jibril lafiya, na tsorata sosai da yanayinsa ina tsoron na zama ajalinsa gashi mahaifiyata ta soma fushi da ni mahaifinsa kuma ba zai taba yafe min ba, duniyarta zata sake rikice har ma ta fi ta baya. Idan har ban yi hakuri zama da Jibril ba duk abunda ya same shi a yanxu ni za a zarga, kuma nasan Bilal ba zai aureni a yanxu ba, ko da kuwa na kashe auren ne na fito. Saboda bakin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119