Chapter 77
Chapter 77
Noor sannan ta kalleni ta ce. “Innarki ta labarta min komai, kuma abunda kike ba ki kyautawa, tun da har ya tuba ya dawo ya nemi ganin dansa ai sai ki bashi dama, ke yanzu in ban da Allah ya nufa ko hanya kin isa ki hada da babban mutun kamar wannan balle har ya zo yana rokonki? In wani ne karbe dansa zai yi da karfi ya barki nan, kin samu ya dawo yana neman yafiyarki kina ta masa wasa da kwakwalwa kamar karamin yaro” Na tada kai na kalleta. “Ke ma laifina kike gani ko Mama Turai?” “Ai dole na ga laifinki, mutumen arziki irin wannan mai kudi haka, ai sai ki bashi dama ko arzikin nasa ku tatsa ni Wallahi da yana son yata da na aura masa mu ga karshen iskanci” “Amman yanzu har kun manta irin cin mutuncin da cin zarafi da ya yi min?” “Yanzu ba ya dawo ya tuba ba? Ai Allah ma mukan masa laifi ya yafe mana balle ke da wani be san da zamanki a duniya ba, ke kikan irin laifin da kike yi ma Allah ne?” Idanuwa sun cika da kwalla saboda na san babu wanda zai fahimce balle ya goya min baya, ni kadai na ke jin abunda na ke ji wata kila saboda ni Jibril ya yi ma abun ba kowa ba. Wannan karon Inna ce ta dora da “Idan har sakamakon Ubangiji kike so tau ko ya kamata ki mika lamurranki gurinsa, ba yin kanki ba ne Allah ne ya jarrabeshi da sonki kuma ya saka masa nadamar abunda ya yi saboda ya jarrabeshi, ki yanzu ba jindadinki ba ne mutumen da ya ce Noor ba dan sa ba ne yanzu har yake risina miki kasa yana neman ki hada shi da dansa? Allah yana son masu yafiya, kuma ba a rama cuta da cuta sai dai a maye cuta da alheri, ina ji miki tsoron kar wannan abun ya dawo kanki, kuma da Noor ya girma ya nemi ubansa ai kara ya girma da Ubansa” Ganin yadda na ke sharar kwalla yasa Inna ta taso ta dafa. “Na san ya cutar da ke yata amman karki mata shi ma Allah ba zai barshi ba, kuma ba kisan halin da ya shiga ba kamin ya gane cewar ke alheri ce a gareshi, ba dan Jibril yana da arkizi na ke son ki yafe masa ba, sai dan hakan zai wanke ki daga zargin da duniya take miki, kuma Noor zai samu rayuwa mai kyau, ke kuma zaki samu damar gina taki rayuwar a gidan aurenki idan kika auri wanda kike so” Bani da wani zabin na yafiya ga Jibril saboda yadda Inna take son na yafe masa din, na kan yi kokarin yin abunda duk mahaifiyata take so ko kuwa abun nan baya min dadi, ba dan komai ba sai dan na san ba zata cutar da ni ba, kuma yarda Allah tana tare da yarda iyaye, na yi ma uwar wasu biyayya ma balle tawa uwar wacce ta dauki ciki ta yi nakuda ta haifeni ta raineni na girma, hakika bana da wani farinciki sai na mahaifiyata. “Zan yafe masa Inna matukar yafe masa din zai faranta ranki, zan yafe masa” “Na jidadi Allah ya miki albarka kema ya baki yayan da zasu yi miki biyayya” Ajiyar zuciya na sauke na share hawayen da ke min zuba ina kallon Mama Turai da ke wasar baki. “Haba ko ke fa, amman ace zuciya kamar ta kafiran farko, Allah ya shiga ya tsakaninku ai mun fi son a shirya” “Dan na yafe masa ba yana nufin zan aureshi ba ne, dan Allah karku tirsasamin yin wani abun daban kuma” “Babu wanda zai tirsasa miki, wata rana ke da kanki zaki karanta mana sirrin zuciyarki” Cewar Inna, ni kuma na kalleta na ce “Zuciyata bata da wani sirrin bayan wanda ke zahiri ke kanki kin san babu wanda na ke so bayan Bilal, be kamata ki zargeni da son wani bayan shi ba” Sai Mama Turai ta taso ta karaso kusa da ni tasa hannunta ta tallafo fuskata yadda zan fuskanceta. “Tausayin Bilal kike Nawwara amman asalin son yana gurin Baban Noor, ke kanki ba ki san abunda ke damunki ba a yanzu, kina tausayin Bilal amman ba za ki iya aurensa ba, kaddarar da ta hada ku ba zata iya bari ku yi aure ba, saboda ke makwafin RAI BIYU ce a gurin Baban Noor idan babu ke koda ya samu Noor rayuwarsa bata kammaluba, haka ma Noor kina matsayin RAI BIYU a gunsa matsayin uwa kuma uba, babu rabon Bilal a jikinki shiyasa kika kasa bashi dama, Baban Noor kuma be da rabo a jikin kowa ce mace sai ke shiyasa kaddara ta sake hada ku kuma zuciyarsa ta kasa barinsa zama lafiya har sai ya nemo mata yar'uwata, ke ma kuma baren zuciyarki yana gurin Noor da Babansa wannan yasa har gobe ba zaki iya amsa kanki a matsayin cikakiyar mace mai jin kanta a mace ba, kika kasa bawa kowa damar sake aurenki gashi Baban Noor ya dawo. Wani baya auren matar wani Nawwara, da kika auri Faruk baki haihu da shi ba ya mutu ya barki saboda Baban Noor ya samu damar sake aurenki, ko da kin haihu da Faruk sai kin fito saboda kaddara ta yi niyar hadaki da tsohon mijinki Nawwara, kurciya ce take cin ki ke kanki yanzu baki san abunda kike so ba, da yanzu za a daura miki aure da Bilal da ba zaki iya zaman aure da shi ba saboda ba shi zuciyarki ke so ba, kuma kaddara ba zata barku ku yi zaman aure ba, ya kamata ki yi tunani karki aikata abunda zai cutar da ke” Tana gama fada min haka ta kalli Inna ta ce. “Ni na tafi Allah ya ba Noor lafiya” Binta Inna ta yi suka fita tare suka barni a dakin ina faman hawaye, ba zan iya bari kalaman Mama Turai su yaudari zuciyata ba, tabbas ni dai na san Bilal na ke so kuma shi zan aura, ba zan zargi Inna ma domin nasan bata cikin irin mutanen nan da ke son yayanta su auri mai kudi, amman wani lokacin ina ganin kamar saboda Jibril yana da kudi ne yasa take son shi, duk da kasancewar Bilal ba talaka ne talak ba, yana da aikinsa kuma ya yi karatu familynsa ma suna da rufin asiri, amman zuciyar Inna ta fi karkarta gurin Jibril. Motsi Noor ya sake yi a karo na biyu har yana kokarin bude idonsa yana motsi da hannu. “Momy... ” Na yi saurin share hawayena na kama hannunsa. “Na'am Noor sannu ka ji” “Momy da zafi sun jimun ciwo sosai” “Kyalesu Allah ya isar maka ya baka lafiya” Ya kalleni da idanuwansa da suka yi fari sosai, sai kuma ya kalli gefena. “Momy na yi mafarkin Babana ya zo nan” Gabana ya fadi. “Wane Baba kuma?” “Wanda ya rasu” Ajiyar zuciya na sauke. “Wanda ya rasu ai baya dawowa Noor, mafarki kawai ka yi” Na shafa kansa sannan na mike na fita dan kiran likita. JIBRIL POV. Da taimakon Allah ya isa gida, zuciyarsa ta yi masa mugun nauyi, ko parking din kirki be yi ba ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119