Chapter 91
Chapter 91
rabo ya shiga tsakaninku da za ki kula shi, ko da yake Siraj ya fada min yanzu matsalar rashin haihuwa take damunsa shiyasa babu ruwansa da ko wace mace” “Haka ya ce miki? Yaushe rabon da ki yi magana da shi?” “Ko jiya mun yi waya da shi” “Amman har yanzu be fada miki Jibril na da da ba?” “Haka ya ce min Jibril ba shi da da kuma ya lalata rayuwarsa da shayeshaye hakan yasa mahaifinsa ya koreshi daga kamfanin da yake ya dora Siraj” “Amman gaskiya Jibril be kyautawa rayuwarsa” “Ni ma da na ji ban jidadi ba, amman Siraj ya ce zai yi iya kokarinsa wajen ganin ya dawo da shi hanya” “Allah ya bashi iko” “Amin” Sai da ta shafe fuskarta ta gyara Hijabinta sannan ta dauki jakarta ta rayata ta mike tsaye. “Na gode sosai Nawwara zan wuce” Har bakin kofa na rakata sai zuciyata na ta tunani akan abokinsa Siraj, miyasa be fada mata cewar yana da da ba? Haka ma yasan lokacin da na fara aiki a kamfanin amman be sanar da Jibril bayan yasan Jibril yana neman ganina, amman kuma miye damuwata da shi ai abokinsa ne babu ruwana a ciki, maganganun Rabi ne suka fado min a rai kan na ankaro Inna ta jefo min wata tambayar. “Wacece wannan yarinyar? Kamin nan miye shigo da ke kina kuka?” Sai a lokacin na tuna da cewar na shigo ina kuka, sai wacan bacin rai ya dawo min na soma jin tsanar Jibril sosai a raina. Kusa da ita na zauna. “Inna wannan Aysha wacce ta yi soyayya da Jibril ce lokacin da ya aureni, ita ce wacce ya ce yana so, shine yanzu take neman gafarata” Haka na kwashe firarmu gaba daya na fada mata irin halin rayuwar da ta ce ta shiga bayan rabuwarsu da Jibril, sai kuma na dora mata da bayanin abunda Jibril ya yi min kamin ya fada mata cewar ya ansallami Noor daga asibiti. “Jibril be kyauta ba, be da ce ya yi miki haka ba, ina tunanin ya yi haka ne saboda ya bata ki a gurin iyayen Bilal kuma suma ya saka musu fargabar wani abu zai iya faruwa da dansu matukar ya aureki” “Ni Inna na tsane Jibril bakin mugu ne Wallahi ni ya dawo min da yarona ba zan barshi ya kwana a can ba” Na fada ina shirin fashewa da kuka. “Ai kara ki kyale Noor ya shaku da Ubansa tun wuri domin kin san dai Jibril ba zai ta ba bari ki je masa agolanci da dansa ba, ke ma kuma ba za ki ji dadin zaman auren ba matukar kika je da Noor domin Mahaifinsa zai rika amfani da wannan damar yana cin zarafinki da mijin da zaki aura, idan kuma mijin da kika aura ya nuna baya son zaman Noor ki ce baya son ki” “Allah ka min mafita” Na fada a fili a zuci kuma na ce Jibril din nan yabi ya tare min ko ina bana da wani sakewa. Muna nan zaune su Sakina suka dawo daga islamiya sai muka dauko wata firar har take fada mana wai malaminsu ya ce satin saman za a kawo kudin da zasu ba iyayensu domin su cigaba da daukar nauyin karatunsu. “Wai Inna ba zamu koma sabon gidan nan ba?” Ta tambaya, ni har na manta da maganar gida domin ban taba zuwa ma ganinsa ba. “Ba zamu koma ba, ko kudin nan ba zamu karba ba duk Jibril ne yake shirya wannan abun, saboda ya siye mu da dukiyarsa” “Ya fada miki shine?” Inna ta tambaya. “A a amman na san shi kadai zai iya wannan abun, idan ba shi ba ne waye ne” “Nima na yi wannan tunani” “Dan Allah Inna karku sake karba komai na sa idan ya baku, Wallahi mutumen ya raina mana hankali sosai ma saboda ya maida mu talakawa, ai da masu kudi ne mu be isa ya taka mu ba” “Kin dai ce kin yafe masa, bana son wata rigima kuma bamu je muka rokeshi ya bamu ba bana son wata fitanar kuma” “Ba zan yi komai ba ai, amman kawai abun yana ci na sosai Wallahi ya ci amanata sosai, kuma ya raina min da wayo da har zai ce ya wai yana neman ya sake aureni, Wallahi aurena da be so da Bilal sai an yi sai dai ya mutu azzalumi kawai” Na fada cikin daga murya hawaye na zuba a ido, ji nake kamar ace Jibril yana kusa da ni yanzu na shakeshi ya mutu. Bayan mun yi sallah magariba na kira Bilal a waya sai ya dauka, na yi tsammanin zan ji shi a cikin wani yanayi marar dadi ko makamancin haka amman sai ya zo a kasin tunanina na jishi cikin farinciki da walwala “Yar halak kin kirani daidai lokacin da zan kiraki na ce ki fito waje gani nan” “Bilal kai ne” “Ni ne mana, wani kika je kira ne kika kirani?” “Aa kawai na ji na cikin farinciki” Ya yi dariya “Cikin bakinciki kike son jina” “Aa kawai na dauka zaka ji haushi na ne kai da Abbah” “Akan me zan ji haushinki Nawwara, abunda kika aikata be kara min komai ba sai kaunarki, yanzu dai fito gani nan kofar gida” Daga haka ya kashe wayar ni kuma na lumshe ido cike da jindadi na sauke ajiyar zuciya, sannan na fadawa Inna na dauki Hijabi na saka na fito kofar gida, jingine da ginin gidan na sameshi kamar kullum yana jiran fitowa. “Pearl” Na kalleshi fuskarta da murmushi. “Wallahi ban tsamaci haka ba ko kadan, na yi tsamanin Abbah zai maka fada ne” “Nawancy kenan, ya yi min fada sosai amman akan rashin kunyar da na yi ma Hajiyar Mustapha ba wai akan abunda ya faru ba, kuma ko da yayi min fada akan ai ba zan dora laifin akanki ba, shine ma ya bani shawarar karna fadawa Mama cewar kin je station domin ya fahimci muna son junan kuma idan Mama ta ji zata yi fada” “Na gode Allah da Abbah ya fahimta” “Kuma ya ce na fada miki cewar Assabar din nan mai zuwa zai zo ya ga su Baba Sulaiman” Na rufe idona da sauri saboda dadi da kunya da suka rufe ni lokaci daya. “Da gaske?” “Aa da karya” Ya fada da fuskar zolaya, sai na sa dariya. “Mama fa mi ta ce?” “Me kike tsammanin zata ce?Addu'a kawai ta yi mana da fatar Allah ya sa alheri a ciki” Na san yace haka ne kawai dan ya kareta amman ba zata so aurena da danta saboda tana ganin kamar kwaruwace xan yi ma danta bayan na yi aure biyu har da kuma yanzu na ce zan auri danta. Mun sha fira sosai a wannan daren sai da aka fara kiran sallah isha'i sannan muka yi sallama ba dan ran mu ya so ba ya tafi ni kuma na dawo cikin gida. Inna ta yi murna sosai kuma ta nuna jindadinta akan maganar har ma ta yi mana addu'a, daga baya kuma ta tambaya abunda iyayensa suka ce kan abunda ya faru yau, ni kuma na labarta mata kamar yadda ya labarta min. Bayan mun gama sallah isha'i wayata ta yi ringing
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119