Chapter 15
Chapter 15
na tabbatar min da cewar ƴan sanda suka duki margayin har ya mutu” Na nuna mata ƙofar fita raina a ɓace. “Fita ki bar mana gida, mutanen da suka labarta miki abunda ya faru ki je can su ƙarasa miki, mu bamu san komai ba” “Haba Baiwar Allah...” “Ki fita Wallahi ko na sa taɓarya na fasa miki kai yanzu” Da gudu ta juya ta fice daga gidan. Ni kuma na cigaba da aikina zuciya na zafi har na gama gyara komai, ciki na shiga na samu Inna har lokacin tana bachi Hijabina na saka na ɗauki kuɗin da suke ƙarƙashin filo na fita neman mai ruwa. Karo na ci da Dpo dake tsaye jikin motarsa yana kallon ƙofar gidanmu, ban gama tabbatar da shi ɗin ne ko a'a ba saboda yau a cikin kayan gida yake. “Assalamu Alaikum Malama” A maimakon na amsa masa sai kawai na watsa masa wata muguwar harara. “Ni ba gurinki na zo ba, matar gidan na ke son magana da ita” “Bachi ta ke” “Ki taimaka ki tashe ta kuma ki nema minlH izinin shiga cikin gidan” “Saboda?” Ya gyara tsayuwarsa yana kallona fuskarsa ba yabo ba fallasa. “Na ga dai ke ba ƴar jarida ba ce, be kamata ki tsare ni kina min irin waɗannan tambayoyin ba, beside ni ba gurinki na zo ba gurin Inna na zo” “Gida mallakinmu, mahaifiya bachi take baƙincikin kashe mahaifinmu da ka yi take ragewa saboda hawan jini” Ban tsaya jiran abunda zai ce ba, na cigaba ta tafiyata. Sai ya zagayo ta gaban motarsa ya sha gabana, cikin ɗaga murya ya fara magana. “Miyasa kuke rayawa zuciyarku cewa ni na kashe mahaifinki? Mi mahaifinki ya yi min da zan kasheshi? Idan na kashe shi wace riba zan ci?” Nima cikin zafin rai na zaburo masa. “Saboda zalincin ƴan sanda, yayarka ta laƙaba masa sata bayan kuma be sata ba, kuka yi ta dukansa har sai da kuka kasheshi akan kawai sai ya amsa laifinsa, wannan ba halinku ba ne? Saboda yayarka tana taƙamar kai dpo ne yasa kuka wulaƙanta mana mahaifi cika tozarta shi sannan kuka ɗauki gawa kuka kawo mana, yanzu kuma kana raina mana hankali har kana wasa da hankalinmu” Ya matso kusa da ni ya nuna ni da yatsa yana magana cikin jin zafin kalaman da na yi masa, har haƙoransa na ƙasa na haɗuwa da na sama yana cizonsu tare da zaro min ido. “Karki sake saka bakinki a akan aikina, karki sake yin furucin akan abunda kika jahilta, i hate nonsense, na zo nan ne dan na faɗa muku karku kuskura bada bayanin mutuwar mahaifinku ga ƴan jarida” Na yi baya-baya ina hawaye, tare da murmushin da ya fi kuka ciwo. “Kamin ta zo nan ashe sai da ta bi ta gurinka, ka yi nasara ban faɗa mata komai ba, amman yanzu kan ni zan tara ƴan jarida da kaina na labarta musu irin zaluncin da kuka mana, wato so kuka a rufa muku asiri kar kowa ya ji ko? Ta yadda muma zaku samu damar ɓatar da mu, Wallahi Allah ba zai barku ba azzalumai macuta-” Ya ƙara matsowa kusa da ni har sai da na matsa baya. “Ki tara ƴan jarida, ki faɗa muku ƴan sanda sun kama mahaifinki sun masa duka har ya mutu, za su tambaye ki dalilin hakan, kuma ki faɗa muku komai karki ɓoye, ni da ke za a ga waye zai ji kunya, idan ba ki yi haka ba to baki haifu ba!” Yana kaiwa nan ya haɗa hannunsa na dama da na hagu ta taɓa saitin fuskata, har sai da na rufe ido. Sannan ya buɗe motarsa ƙirar 406 ya shiga ya fisgeta kamar zai tashi sama, ko da na ɓuɗe idona ƙurar motar kawai na gani hawaye ya sauko daga idona, lallai wannan shi ne a dakika a hana kuka, kuma a mareka a ƙwace maka jaka! Kasa zuwa kiran mai ruwan na yi saboda kuka da ya ci ƙarfina, na koma cikin gida da sauri. Bana son na tashi Inna balle har ta ga hawayena hakan yasa na shige ɗakinmu na kwanta saman tabarma, na ci kuka na sai da na ƙoshi sannan bachi ya yi gaba da ni. Motsin shigowar su Habiba ne ya tasheni daga dogon banchin da ya ɗaukeni, babu komai a mafarkina sai wacan tashin hankalin da ya faru, Baba ne kawai na ke ta gani sai kuma irin zamantewar da muka yi a gidan kamin rasuwarsa. Ko da na fito na samu Inna ta farka har suna fira da Habiba ma da ke cire safa. “Nawwara kin tashi?” Inna ta tambaya tana kallona, sai na zauna bakin ƙofar ina amsa mata. “Eh ashe rana ta yi” “Tun ɗazu su Noor suka dawo na ce kar ya tasheki kin gaji da yawa, ƙara ki samu bachi ki ɗan huta” Kallo ɗaya Habiba ta yi min ta ɗauke kai, kamar ba ta ganni ba, hakan ya karatar da ni da akwai wani abu a ƙasa, sai dai ban ce da ita komai ba na tashi na ɗauki bula na shiga banɗaki, bayan na fito na yi alwala na shiga ɗakinmu dan Sallah. A ciki na sameta tana ɗaura zane, naje kusa da ita na tsaya. “Habiba kamar akwai abunda ya ke damunki?” Ta ɗaga kai ta kalleni a maimakon ta yi magana sai ta kawar da kai ta soma magana. “Nawwara ɗazu da zanje makaranta na haɗu da Mustapha, na tsayarda shi na bashi haƙuri akan abunda kika masa, sai yake tambayata ke yayata na ce eh, shine ya ce wai tun da yake a rayuwarshi wata mace bata taɓa ɗaga hannu taareshi ba ko da uwarsa ce sai ke, akan me zaki mareshi, bayan da ke yake magana ba, kawai ya buga motarsa ya yi tafiyarsa. Nawwara miyasa kika mareshi? Zaki ƙara ja mana matsala” “Shiyasa kike jin haushi na? Babu abunda zai faru Habiba, kuma bari kiji na faɗa miki ko da Mustapha zai yanka ni ya dafa namana ya soma ya ci, ba zan bashi haƙuri ba, ke ma kuma kinyi kuskure da kika tunkare shi kika ba shi haƙuri wannan ba halinki ba ne Habiba” “To ya kike son na yi? Bamu da wani gata sai na Allah mutane kamar jiranmu suke su yi mana abu, yanzu idan wani abu ya sake samun family mu ban san ya zan yi ba, Allah kasa ni ce zan fara bin Baba na gaji da wannan rayuwar” Ta fashe da kuka. Ni kuma na riƙeta muka zauna tare ina rarrashinta. “Babu abunda zai sake faruwa inshallahu, na miki alƙawari, share hawayenki kar Inna ta ji” Ta ɗaga min kai tana share hawayen. Haka muka zauna cikin jiran tsamanin abunda zai same ni daga Mustapha domin na san ba zai bar ni ba, Habiba ma kullum cikin tunanin wannan abun take, bata ƙaunar ko waje na leƙa saboda gani take kamar zan iya haɗuwa da shi ya yi min wani abu. Wasa-wasa muka kwashe sati uku babu abunda ya faru sai dai tunanin abun zai faru ya hanani sukuni ni da Habiba, a cikin satin ne su Murja da Hajiya Umaima da Hasana suka zo min gaisuwa tun ɗaga Kebbi. Wato Yayar tsohon mijina da kuma ƙannensa, mahaifiyarsa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119